Published in HUMANITIES IN THE SUB-SAHARAN WORLD (University of Cairo/ Umaru Musa Yar’adua University, Katsina, Special Research in Humanities) RUWAN BAGAJA IN PERSPECTIƁES: (Eight Decades of a Hausa Masterpiece in Prose 1933-2013), page 393 – 410
Tarbiyyar Bahaushe a Mahangar Ruwan
Bagaja
English Rendition as, “Hausa Moral Behaviour as viewed from the Eyes of Water of Cure”
Dr. Bashir Aliyu Sallau
Department of Nigerian Languages
Umaru Musa Yar’adua University, Katsina – Nigeria
sarkingaska@yahoo. com
Tsakure
Kafin
shigowar Larabawa da Turawa ƙasar Hausa hanyar da
Hausawa suke bi wajen koyar da tarbiyya da adana ta, ita ce ta hanyar adabinsu
na baka. Shigowar Larabawa da kuma karɓar addinin Musulunci da Hausawa suka yi, ya taimaka wajen
samuwar rubutu da karatu. Haka kuma, shigowar Turawa ƙasar Hausa da kafuwar mulkin mallaka a cikin ƙarni na goma sha tara ya taimaka wajen samuwar rubutun boko
wanda ake yi da haruffan Romanci. Domin samar da littattafan da za su taimaka
wa makarantu su sami abin karantawa, a cikin shekara ta 1933, Hukumar Talifi ta
shirya gasar rubuta litattafan karatun zube. A gasar, marubuta sun rubuta
littattafai masu yawa waɗanda daga ƙarshe aka zaɓi littafin ‘Ruwan
Bagaja’ wanda Alhaji Abubakar Imam ya rubuta a matsayin na ɗaya. Sai kuma littafin ‘Shehu
Umar’ wanda Alhaji Abubakar Tafawa Ɓalewa ya rubuta ya zama na
biyu da sauransu. Maƙasudin wannan takarda shi ne, ta yi
nazarin littafin ‘Ruwan Bagaja’ domin duba yadda marubucin ya kalli
tarbiyyar Hausawa a cikinsa. Dalili kuwa shi ne, a wannan littafi an kalli
manyan ginshiƙan tarbiyyar Hausawa waɗanda suka shafi gaskiya da
riƙon amana da yin biyayya ga iyaye da shugabanni da kiyaye
dokokin addini da riƙo da sana’o’i da nuna kara da yin
zumunci da sauransu.
1.0 Gabatarwa
Bisa ga tsarin ilimi na zamani kowace al’umma tana da
ire-iren hanyoyin da take bi domin adana tarihinta da al’adunta da muradunta
yadda za su tafi daidai da zamani. Kafin shigowar Larabawa da Turawan mulkin
mallaka ƙasar Hausa, hanyar da Hausawa suke bi
wajen cim ma wannan buri ita ce, ta hanyar adabin bakan su. Idan muka waiwayi
tarihi, za mu fahimci cewa, al’ummar Hausawa sun sami hanyar rubutu da karatu
ne sakamakon shigowar Larabawa da Turawa ƙasar Hausa. Da farko a iya
cewa, shigowar Larabawa ƙasar Hausa cikin ƙarni na goma sha huɗu, waɗanda daga cikinsu akwai Larabawa ‘yan kasuwa na Masar waɗanda su ne suka fara zuwa,
sai kuma wasu Larabawa Malamai na Morocco da Bagadaza da Masar waɗanda suka kawo addinin
Musulunci, ya taimaka wajen koya wa Hausawa rubutu da karatu cikin haruffan
Larabci. Sannu a hankali wannan ilimi na addinin Musulunci ya ƙara samun bunƙasa da karɓuwa a wurin Hausawa. Ta
dalilin haka ne, wasu daga cikin Hausawa waɗanda suka sami ƙwarewa a fannin suka ƙirƙiro rubutun Ajami. Wannan al’amari ya ƙara taimakawa matuƙa gaya wajen bunƙasar ilimin addinin Musulunci a tsakanin Hausawa. Haka
kuma, ta wannan hanya ce malaman addinin Musulunci Hausawa suka riƙa rubuta waƙoƙin addini, da kuma yi wa sarakunan da manyan ‘yan
kasuwar ƙasar Hausa magatakarda. Ba a nan
al’amari ya tsaya ba, don kuwa waɗannan malamai sun riƙa rubuta wasiƙu tsakaninsu, waɗanda har a wannan zamani akwai ire-iren su da ake samu a
gidajen ajiye kayan tarihi da kuma gidajen ire-iren waɗannan malamai da suka
gabata.
Kashi na
biyu da za a iya cewa, Hausawa sun koyi hanyar rubutu da karatu, a iya danganta
ta shigowar Turawan mulkin mallaka ƙasar Hausa a cikin ƙarni na goma sha tara. Bayan duk wata yarjejeniya da tataɓurza da yaƙe-yaƙe da suka gudana tsananin
sarakunan ƙasar Hausa da Turawan mulkin mallaka
na Ingilishi. Daga ƙarshe, a cikin shekarar
1903 dukkan ƙasar Hausa ta koma ƙarƙashin mulkin Turawan
Ingilishi. Bayan cim ma wannan buri na kafa mulkin mallaka a ƙasar Hausa, babban abin da ke gaban Turawan, shi ne su sami
‘yan ƙasa waɗanda za su riƙa taimaka musu wajen tafiyar da mulki a ofisoshi kamar
yadda ake yi a Ingila. Waɗannan mutane ba za su samu ba, dole sai an kafa makarantun
da za su horar da su. Wannan ne ya sa Gwamna Lugga, wanda shi aka ba ikon
tafiyar da mulkin Arewa wadda ƙasar Hausa take ciki,
ya ɗauki matakin da ya kai ga
kafa makarantar Ɗan Hausa a Nasarawa Kano,
amma ba ita ce makarantar boko ta farko ba a Arewa. An kafa wannan makaranta a
cikin shekarar 1909 aka kuma ba wani Bature mai suna Sir Hans Ɓischer, wanda saboda yadda yake jin Hausa ake yi masa laƙabi da Ɗan Hausa.
2.0 Ƙoƙarin Samar da Littattafan
Karatun Zube na Hausa Daga Shekarar 1929 – 1933
Bayan buɗe makarantar Ɗan Hausa a Kano, har zuwa lokacin da aka ƙara buɗe wasu makarantu a wasu garuruwa na ƙasar Hausa babu wasu tsayayyun littattafan da aka rubuta da
boko don koyarwa. Mafi yawancin rubuce-rubuce da littattafan da Turawa suka
rubuta cikin harshen Hausa, sun tsara su ne don koyar da Hausa ga Turawa a
can ƙasashensu. A nan ƙasar Hausa kuwa, littattafan Larabci da kuma wasu
rubuce-rubucen da aka yi cikin Hausa rubutun Ajami ne waɗanda mafi yawancinsu waƙoƙi ne (Yahaya, 1988:93).
Bisa tsarin koyarwa a waɗannan makarantu, Sir
Hans Ɓischer, watau Ɗan Hausa tare da taimakon wasu malamai da suke koyarwa a waɗannan makarantu suka samar
da littattafan da suka riƙa amfani da su wajen
koyarwa. Daga cikin littattafan akwai Karatu Hausa, da Littafi
Na Koyon Karatu, sai Littafin Koyon Lissafi da
kuma Lararin Ƙasashen Afirka waɗanda dukkansu a Ingila aka
buga su.
2. 1
Kafa Hukuma Fassara
Sakamakon
bunƙasar ilimin zamani da kuma ƙaruwar makarantun boko a ƙasar Hausa, ya sa ma’aikatar ilimi ta fahimci akwai
babban ƙalubale a gabanta na samar da
littattafan Hausa da za a yi amfani da su wajen koyarwa. Wannan dalili ne ya sa
Gwamnati ta kafa Hukumar Fassara (Translation Bureau) a cikin shekarar
1929. Da farko a ƙarƙashin wani Bature mai suna Mr. C. E. J. Whitting, kuma a
gidan Ɗan Hausa da ke Nasarawa a Kano aka
fara buɗe mata ofis. Bayan shekara
biyu da kafa wannan hukuma, watau 1931, sai aka mayar da ita Zariya inda aka buɗe mata ofishinta na
dindindin. Shekara ɗaya bayan dawowar wannan Hukuma Zariya, watau 1932, sai aka
miƙa shugabancinta a hannun wani haziƙi, kuma mashahurin masanin Hausa, mai suna Dr. R. M. East.
Domin
cim ma burin kafa wannan hukuma, an ɗora mata nauyi kamar haka:
i. Fassara littattafai daga
waɗansu harsuna, musamman
Larabci da Turanci zuwa Hausa.
ii. Wallafa littattafai cikin
harshen Hausa.
iii. Shirya littattafai manya
da ƙanana don karantatawa a makarantu.
iv. Taimaka wa ‘yan ƙasa su dinga wallafa littattafai (Yahaya, 1988:93-94).
A karon
farko a iya cewa, kafa wannan Hukuma ya taimaka wajen samar da littattafan da
aka fassara musamman daga Larabaci zuwa Hausa. Haka kuma, da wasu daga Turanci
zuwa Hausa kimamin goma sha huɗu, waɗanda suka haɗa da:
a) Dare Dubu da Ɗaya – Larabci zuwa Hausa
b) Labarun Hausawa da Maƙwabtansu – Larabci zuwa Hausa
c) Labaru na Da Da na Yanzu –
Larabci zuwa Hausa
d) Littafi na Bakwai na Leo
Africanus – Turanci zuwa Hausa
e) Siɗ Hausa Plays –
Turanci zuwa Hausa
2. 2.
Kafa Hukumar Talifi
Hans Ɓischer (Ɗan Hausa), ya gabatar da
wani shiri a cikin shekarar 1933, don gudanar da gasar rubuta ƙagaggun labarai na rubutun zube. Domin cim ma wannan buri,
sai aka sauya sunan Hukumar Fassara zuwa Hukumar Talifi, don ta gudanar da
wannan gagarumin aiki. Dalilin sauya wannan suna shi ne, a ƙara faɗaɗa aikin wannan hukuma daga fassara ayyuka daga wasu harsuna
zuwa harshen Hausa.
Domin
gudanar da wannan aiki. An bai wa Hukumar Talifi ƙarƙashin shugabanci Dr. R. M.
East nauyin gudanar da gasa. Daga nan ne, sai shi Dr. East da kansa ya zagaya
manyan garuruwan ƙasar Hausa don tallata
wannan gasa, inda ya sadu da malamai masu gaurayen ilimin zamani da na Arabiya
ya yi musu bayani kan ire-iren littattafan da ake so su rubuta. Ya kuma ƙara bayyana musu cewa, dukkan wanda ya ƙago wani labari a rubuce, za a karɓa a shirya shi a buga shi,
domin a sami abin karantawa, kuma za a ba shi na goro. Wannan talla ta jawo
hankalin marubuta da yawa. Sakamakon ta aka sami rubuta littattafai masu yawa
da suka shiga cikin gasar. Daga ƙarshe, bayan an tace waɗannan littattafai, an zaɓi biyar da suka yi nasara:
i. Ruwan Bagaja M. Abubakar Imam
ii. Ganɗoki Malam Bello Kagara
iii. Shaihu Umar M. Abubakar
Tafawa Ɓalewa
iv. Idon Matambayi Malam Muhammadu
Gwarzo
v. Jiki Magayi Malam John Tafida da
Dr. R. M. East
Daga
cikin waɗannan littattafai,
littafin Ruwan Bagaja na M. Abubakar Imam shi ya fi ɗaukar hankalin masu
gudanar da gasar da kuma karɓuwa ga masu karatu. (Yahaya, 1988:95).
Haka
kuma, wannan dalili ne ya ɗauki hankalin mu, inda muka ga ya dace, domin murnar cika
shekara tamanin (80 watau 1933 – 2013) da yin wannan gasa, a yi wani aiki
kan wannan littafi don fito da waɗannan manyan jigajigan fannonin nazarin Hausa. A fito da su
fili kamar yadda wannan mawallafi ya shirya su cikin wannan littafi, ba
tare da tunanin sa na cewa, wata rana wasu manazarta za su yi nazarin wannan
littafi ba, wani ba zai ce dukkan abubuwan da ya shirya a cikin littafin ya yi
su ne da irin wannan tunani.
3. 0
Yadda aka Fito da Tarbiyyar Hausawa Cikin Littafin Ruwan Bagaja
Domin
cim ma burin da aka yi bayani a baya, a matsayina na ɗalibin al’adun Hausawa na
ga ya dace in dubi tarbiyyar Hausawa a mahangar littafin. Tarbiyya kuwa, ta
shafi kiyaye dokokin addini, da biyayya ga shugabanci, da gaskiya da riƙon amana, da sadar da zumunci da taimakon juna, da riƙo da sana’a, da kara da alkunya da nuna jarunta da juriya.
Wannan kuwa ya faru ne saboda mawallafin wannan littafi Alhaji Abubakar Imam
cikakken Bahaushe ne wanda ya yi ƙuruciya, ya girma har
Allah Ya amshi rayuwarsa a ƙasar Hausa. Haka kuma, ya
sami koyarwa da tarbiyyar Hausawa wadda addinin Musulunci da zamananci suka yi
naso cikinta.
3. 1
Kiyaye Dokokin Addini
Tsarin
tarbiyyar Bahaushe ya fara tun daga irin yadda yake kiyaye dokokin abin da yake
bauta wa. Addinin farko na mutanen ƙasar Hausa shi ne addinin
gargajiya, watau bauta wa Iskoki ko mutanen ɓoye. Sakamakon daɗewa ana yin wannan bauta
ya sa ko da al’ummar Hausawa suka karɓi addinin Musulunci, addininsu na gargajiya ya yi naso
cikin addinin Musulunci. A iya gani haka a dukkan rayuwar Bahaushe. Saboda
tarbiyyar kiyaye dokokin addini da Hausawa suke da shi ya sa, idan mutum ya
fuskanci wata matsala yake zuwa wurin malamai don a taimaka masa. Irin wannan
taimako ya haɗa da addu’a da duba wadda ta samo asali daga addinin
gargajiya na Hausawa da sauran hanyoyi.
Ta
wannan fuska, marubucin littafin Ruwan Bagaja ya fito da irin
yadda al’ummar Hausawa suka kiyaye dokokin addini. Misali, a shafi na 4, za a
ga inda saboda kiyaye dokokin addini, ya sa da Saƙimu ya yi mafarkin wani
abu ya fito daga zakarin mijin mahaifiyarsa da ya kashe ya sa shi neman malaman
duba don su yi masa duba su gano masa ma’anar wannan mafarki da ya yi, kamar
haka:
“Ana nan, bayan ‘yan kwanaki da
rasuwar malamin, sai Saƙimu ya yi mafarki, ya ga
malamin a tsaye. Sai ga wani ɗan abu, kamar ɗan dabino, ya fito daga zakarin malamin. Sai ya ga abin nan
yana ta girma har ya kai kamar zaki. Da ya kai haka, sai abin ya faɗa masa ya kashe shi.
Wannan mafarki fa ya dugunzumad da ransa. Da gari ya waye, sai ya tara malamai
don su masa duba”.
Haka
kuma, daga shafi na 4 – 5, saboda yarda da ire-iren ayyukan malaman duba ya sa
Saƙimu ya riƙa ba matan wannan malami
da ya ya kashe guba wadda ta yi sanadiyyar mutuwarsu. Malaman nan sun gaya masa
cewa, daga cikinsu akwai wadda za ta haifi ɗan da zai kashe shi.
“Dukan malamai, kowa ya duƙufa ya zana ya shafe, ya zana ya shafe. Daga nan sai babbansu
ya ce, “Za a haifi wani yaro a gidan nan, cikin matan tsohon nan da ya rasu shi
ne zai kashe ka”.
Duk da kasancewar da farko Saƙimu bai amince da
sakamakon da waɗannan malamai suka ba shi ba. Ya kore su, amma daga baya
saboda nason da addinin gargajiya ya yi a wurinsa wanda ya haifar da kiyaye
dokokin addini a wurinsa, ya sa shi sauya tunaninsa a cikin shafi na 4 – 5
kamar haka:
“Da tsakad dare, Saƙimu ya tashi ya ƙulla wannan ya ƙwance, yana ta juyayi cikin zuciyarsa, yana cewa, “Allah
abin tsoro, malami abin tsoro! Abin da ya fi kyau sai in halaka matan nan huɗu duka masu takaba, don
kada maganar masu dogwayen geman nan ta zama gaskiya. ”
Haka kuma, a shafi na 6, an bayyana irin yadda wasu daga
cikin al’ummar Hausawa suke kaɗaicewa don kiyaye dokokin addini da yin bautar Allah,
Maigirma da ɗaukaka. A wannan shafi an bayyana cewa, Alhaji Imam ya
tarar da wani tsoho wanda ya bayyana masa cewa:
“Ni mutum ne ɗan’uwanka, shekarata
saba’in a nan ina ibada ban taɓa ganin wani mahaluƙi ba sai fa kai. ”
A cikin wannan littafi na Ruwan Bagaja, an ƙara bayyana irin yadda al’ummar Hausawa suke kiyaye dokokin
addini. A iya ganin haka a shafi na 8 inda Alhaji Imam ya isa wani gari na
jahilai mai suna Saburi, da kuma irin karɓar da aka yi masa ta matsayin babban malami, kamar haka:
“Da zuwana na sami wata doguwar
tasbaha, na nufi wajen Sarki, na ce ni malami ne.
Ya ce, “Daga ina?”
Na ce, “Daga ƙasashen Larabawa. ”
Da Sarki ya ji haka, ya yi murna da
zuwana, ya ce, “To ina za ka?”
Na ce, “Nan na zo in riƙa yi muku salla don za a su ku aljanna ku duka domin
adalcinka, ya Sarki. ”
A shafi na 17 ma an ƙara bayyana irin yadda
Bahaushe yake kiyaye dokokin addini, inda aka bayyana cewa:
“Bayan an yi asalatu, sai na tashi na
fito waje, na yi alwalla, na tafi masallaci na bi Liman don neman falalar
jam’i. Da aka ƙare, na yi ‘yan wurudda na gama, na
komo gida. ”
Wannan al’amari na kiyaye dokokin addini kamar yadda aka
fito da su a cikin littafin. Ba su tsaya a nan ba, don kuwa a shafi na 23 – 24,
an ƙara bayyana irin yadda Bahaushe yake
kiyaye dokokin addininsa, kamar haka:
“Tun da tsakad dare, na tashi ina bin
gari ina wa’azi har safe, kowa garin ya ji na kwana hadisi. ”
Haka al’amarin ya ci gaba, inda a shafi na 28, aka ƙara bayyana wannan batu da muke bayani a kan sa, inda aka
bayyana cewa:
“Ina cikin tafiya, har na kai wani
gari wai shi Miska, na sauka gidan wani malami wanda ake ce masa Daula. Don
ibadarsa har mutane su kan yi masa kirari, suna cewa, “Na-Malam Iro masu kwana
salla!”
Saboda kiyaye dokokin addini ya sa al’ummar Hausawa suke
girmama malamai kuma suna ba su ƙima sosai. A cikin wannan
littafi an fito da irin wannan ƙima da Hausawa suke ba
malamai a shafi na 30 – 31. A waɗannan shafuka, an bayyana irin martaba, da ɗaukaka, da girmamawar da
aka yi wa Alhaji Imam saboda ɗaukarsa da aka a matsayin babban malami. Misali, a shafi na
31 buwaya wadda mutanen wannan gari suka ɗauka karama ce ta waliyyai da ya nuna
musu lokacin da ɗiyar Sarki ta rasu, ya isa a ƙara fahimtar irin girmamawar da Hausawa suke ba malamansu
na addini. Ga kaɗan daga cikin ire-iren abubuwan da suka sa mutanen Nasarawa
ba Alhaji Imam girma:
“Sai na wuce su, na yi ta yi, har na
tarad da wani tabki, na tsaya na yi wanka, raina ya komo. Sa’an nan na isa
garin, na tambayi gidan aka nuna mini na shiga masallacin ƙofar gidan, ina jan tasbaha. Jimawa kaɗan sai suka iso. Da na ji
sun iso sai natashi na fita daga masallacin da tasbaha a hannuna, na ce,
“Sannunku da zuwa!”
Waziri da mutanensa, kowa ya rasa abin
da zai ce. Duk sai na ga sun faɗi a gabana sun yi mini sujada.
Na ce, “Kash! Subhana lillahi! Ai sai
Ubangiji a ke wa haka. ”
Saboda kiyaye dokokin addini ya sa idan Bahaushe ya aikata
laifi yake neman gafara daga wurin Allah, Maigirma da ɗaukaka, don ya yafe masa.
Wannan dalili ne ya sa marubucin ya fito da irin wannan tarbiyya ta Bahaushe a
cikin wannan littafi. Ya bayyana cewa, kasancewar Alhaji Imam da Malam Zurƙe sun daɗe suna ɓarna da tu’annati da saɓa wa Allah. Domin kiyaye dokokin
addini ya sa, a lokacin da suka isa birnin Baitul Muƙaddas, sai Malam Zurƙe ya shawarci Alhaji Imam
da su tuba. Ga bayanin abin da suka tattauna;
“A wannan gari mai albarka Malam Zurƙe ya ce mu tuba da irin ayyukammu na saɓo hakanan. Na yarda da
magana tasa, muka tara malamai aka yi mana addu’a don kada Shaiɗan ya sake wasa da
zukatammu. ”
Yana daga cikin tarbiyyar Bahaushe, idan yana neman biyan
wata buƙata, ko idan ya shiga cikin tsanani ya
roƙi Allah don Ya biya masa bukatunsa. A cikin Ruwan
Bagaja, an fito da irin wannan tarbiyya a shafi na 38 – 39, kamar
haka:
“Da ka shiga garin ka yi ta rera
wannan waƙa: ‘Wa yaf’alu fi hukmihi ma
yasha’u. Ta’alal ilahu wa jallal hikam, ’ har ka ɗebo ruwan ka fito. ”
3. 2
Biyayya ga Shugabanci
Tun
kafin shigowar addinin Musulunci ƙasar Hausa, Hausawa suna
da kyakkyawan tsari na shugabanci, inda na ƙasa yake yin biyayya ga na
gaba da shi. Haka kuma, talakawa suna yin biyayya ga sarakunansu. Idan muka
duba cikin Ruwan Bagaja, za a ga wurare masu tarin yawa inda
aka yi bayani a kan irin yadda yake ba nuna cikakkiyar biyayya ga shugabanci.
A farkon wannan littafi marubucin ya buɗe shi da irin tsarin Bahaushe na yin
biyayya ga shugabanni. Dalili kuwa shi ne, a tsarin tarbiyyar Bahaushe, idan baƙo ya sauka a wani gari wanda ba a san shi ba, sai ya je
gidan sarki, ko hakimi, ko dagaci, ko mai’unguwar garin ko ƙauyen don a saukar da shi. A wancan zamani da ake bin irin
wannan tarbiyya an sami zama lafiya da kwanciyar hankali. A iya ganin haka, a
shafi na 1 inda aka bayyana cewa:
“Yana cikin bin ƙasashe, har ran nan Allah Ya sa ya isa wani gari wai shi
Kwantagora, wani babban birni a cikin ƙasar Sudan. Ya isa wajen
Sarkin garin, aka kai shi masauki”.
Irin wannan tsari na biyayya ga shugabanci, wanda yake bayyana
idan baƙo ya sauka a wani gari da ba a san shi
ba, ya fito a wurare da dama.
A dai wannan shafi an ƙara bayyana irin yadda
na ƙasa yake yin cikakkiyar biyayya ga
shugabansa, inda zai zauna tsawon lokaci yana jiran shugabansa.
“Koje Sarkin Labari ya ce musu, “Yana
fitowa yanzu?” Suka ce, “Wa zai fito da shi yanzu tun azahar ba ta yi?” Koje ya
share wuri, ya zauna kan azahar ta yi”.
Idan muka nazarci wannan jawabi da ya gabata, a iya
fahimtar cewa, barorin Alhaji Imam da shi Koje Sarkin Labari, saboda tarbiyyar
biyayya ga shugabanci, sun zauna a ƙofar gidan Alhaji Imam,
har sai da azahar ta yi lokacin da zai fito.
Bisa tarbiyya al’ummar Hausawa mutane ne masu matuƙar biyayya ga shugabanninsu, suna bin umurninsu ta yadda
duk irin aikin da suka sa su za su aikata ko da kuwa irin wanda za a ci
mutuncin wani ne. A shafi na 9, saboda irin wannan tarbiyya ce, ya sa Alhaji
Imam ya sa yara suka yi wa Malam Zurƙe ature suka kore shi daga
wannan gari. Ga yadda al’amarin ya faru.
“Na dubi Malam Zurƙe, na ce wa yara, “Ku yi masa eho da ature. ” Suka bi shi
Eho! Eho! Eho! Daga nan ko ta kan littattafansa bai biya ba, ya yi wajen gari,
yara na jifa. Ya tsere da kyar. ”
3. 3 Gaskiya da Riƙon Amana
Hakika, dukkan al’ummar da take da gaskiya da riƙon amana za ta zauna lafiya. Wannan dalili ne ya sa a
wancan zamani, saboda gaskiya da riƙon amanar Hausawa suka
zauna lafiya. Wannan kuwa ya faru ne, saboda kowa ya tsare gaskiyarsa. Haka
kuma, idan ka kawo ajiya ka ba mutum, ko shekara nawa ka ɗauka, a ranar da ka bukaci
kayanka, za ka tarar da su kamar yadda ka ba da ba tare da wani abu ya ɓata ba. Domin bayyana
muhimmancin gaskiya da riƙon amana, marubucin
littafin Ruwan Bagaja, ya nuna inda Alhaji Imam ya yi ta
gamuwa da matsaloli iri daban-daban saboda rashin gaskiyarsa da ƙin riƙe amanar da aka ba shi.
Misali, a iya ganin haka a shafi na 7, inda ya bayyana wa wani attajiri cewa,
shi babban farke ne kamar haka:
“Idan shanuna sun zo ba ni sayar wa
sai shi kaɗai, ya kama ko wane sa ya
karya yadda yake so, don ni ke da abina. ”
Saboda ire-iren waɗannan romon baka da ya riƙa yi wa wannan attajiri
ne, da kuma irin yadda ya ba shi gaskiya, ya sa Alhaji Imam ya damfari wannan
attajiri, har ya ranci kuɗinsa jaka ɗaya da nufin idan shanunsa sun zo zai sayar masa da araha.
Daga ƙarshe, saboda ba shi da gaskiya, ya
gudu ya bar garin.
Haka kuma, a shafi na 11 – 12, na wannan littafi an bayyana
muhimmanci riƙon amana da kuma irin abin da kan sami
wanda ya ci amana. A wannan shafi, an bayyana inda Alhaji Imam ya haɗu da wani baƙauye kamar haka:
“. . . . . . . . . . . . Ina
cikin tafiya cikin daji, sai na gamu da wani baƙauye, da jaka ɗaya da sule ɗaya da kwabo biyar. Na yi
tambayarsa, duk ya gaya mini labarin yadda ya sami kuɗin, da yadda ya kashe
sule ɗaya da kwabo biyar ɗin. Da zai tsaya ratsi,
sai ya ba ni in riƙe masa, wai shi da abokin tafiya.
Ko da ya fito, ya ce, “Ba ni mu tafi.
”
Sai ni kuwa ba kunya ba tsoro na ce,
“Im ba ka me? Ni da kuɗina. ”
Idan muka nazarci wannan bayani dangane da irin hirar da ta
shiga tsakani wannan baƙauye da Alhaji Imam, za a
fahimci cewa, wannan baƙauye, saboda irin
tarbiyyar da ya tashi da ita ta gaskiya da riƙon amana ne ya sa ya ba
Alhaji Imam ajiyar waɗannan kuɗi nasa. Dalili kuwa shi ne, a cikin zuciyarsa ba ya
tsammanin fuskantar wata matsala idan zai amshi ajiyarsa. A maimakon haka, sai
Alhaji Imam, ya bure idonsa da toka, ya bayyana wa wannan baƙauye cewa, sam shi bai ba shi ajiyar wasu kuɗi ba. Wannan kuɗi na hannunsa da ma nasa
ne. A nan ne marubucin wannan littafi ya bayyana mana cewa, tarbiyyar Hausawa
ta gaskiya da riƙon amana ta fara lalacewa, wanda
al’amarin har ya fara shafar yadda ake gudanar da sha’anin shari’a a ƙasar Hausa. Ya ƙara da bayyana cewa, duk
irin gaskiyar ka, matuƙar ba ka ba Alƙali wani abu ba, idan mara gaskiya ya ba da wani abu, sai
Alƙalin ya juye gaskiyar daga mai gaskiya ya ba marar gaskiya.
Ga yadda riwayar take:
“Wasa wasa dai har abin ya yi girma,
ya kai mu muka runtuma gidan Alƙali. Da ma na ji Alƙalin mai bakin cin rashawa ne. Da muka je ya tambaye ni, na
mai da jawabi kamar gaske. Ya tambayi baƙaushe, mamaki ma ya hana
shi ya faɗi wani abin kamawa”.
“Alƙali ya ce masa, “Kana da
shaidu?”
Ya ce, “A’a, sai Allah da Ma’aiki. ”
Sa’an nan Alƙali ya juyo ya ce mini, “Kai kana da shaidu, samari?”
Na ce, “I, Allah ya gafarta malam, ina
da su da yawa. ”
Ya ce, “Su wa da wa gare ka?”
Na ce, “Malam Ɗalhatu da ɗan’uwansa suna sun shaida, Malam Sule da ɗan ƙanensa Malam Hashimu sun shaida. Bari ta su ma, har autansu
Malam Muhtari yana nan aka yi. Waɗansu mutane ma kamar ɗari masu zuwa da tsakad dare duk za su
shaida!”
“Ko da malam ya ji haka sai ya fahimta
da magana ta. Malam Ɗalhatu da ɗan’uwansa dala biyu ke
nan. Malam Sule da Malam Hashimu kuwa sule da sisi ke nan. Malam Muhtari kuwa
taro ke nan, mutane ɗari masu zuwa da tsakad dare kuwa sule ɗari ke nan. ”
“Watau da tsakad dare zan kawo masa
sule ɗari da shida ba taro idan
ya ba ni gaskiya. To, yanzu zamani ne dai na wanda ba mai gaskiya sai mai sule.
Nan da nan mai bakin cin rashawa ya birkita maganar, ya ba ni gaskiya.
Aka ɗaure baƙauye wata uku don ya sa mini sata. Da dare na kawo wa Alƙali waɗannan, na koma na shiga shagali da sauran”.
Allah ba azzalumin kowa ba ne. Bari mu ga irin sakamakon da
wannan baƙauye zai samu dangane da cin amanarsa
da Alhaji Imam ya yi kamar haka a shafi na 12.
“Ran nan na fita waje, garin shan
iska, sai na tsinto wani murjani. Ashe na ‘yar Sarki ne aka sace ya faɗi. Na kawo kasuwa sayarwa.
ko da aka gan ni da shi sai aka kama ni, aka kai ni gidan Alƙali. Na yi juyin duniyan nan, aka ce ni na sace shi. Aka yi
mini bulala ashirin, aka kai ni gidan yari wata uku. Na tarad da baƙauyen can da na yi wa rikicin kuɗi na sa aka ɗaure shi shekaran jiya. Ko
da muka yi arba ya ce, “Allah Sarki!Alhaki rima. ”
3. 4 Sadar da Zumunci
Bahaushen mutum kafin zuwan wannan zamani a duk inda ya
sami kansa mutum ne mai ƙoƙarin sadar da zumunci. Wannan kuwa ya faru ne sakamakon
irin tarbiyyar da ya tashi da ita wadda ta koya masa ziyartar ‘yan’uwa da
abokan arziki. A nan ma marubucin ya yi ƙoƙarin fito da wannan ginshiƙi na tarbiyyar Hausa.
Misali, a shafi na 37 – 38 na wannan littafi, an fito da muhimmancin sadar da
zumunci wanda yana daga cikin abubuwan da suka ƙara taimaka wa Alhaji Imam samun Ruwan Bagaja. A nan an
bayyana cewa:
“Da farko ma in faranta maka zuciya.
Wan Liman ɗin nan da ka tarad da shi a kogon yana ibada, abokina ne.
Abin da ya gama mu kuwa, wata rana ne
uwata ta tafi yawo har can ƙasar Sudan tana
goyona. Ƙishirwa ta kama ni har fara kuka. Sai
uwata ta tarad da uwar su uban nan naka, Liman, tana ɗibar ruwa. Watau uwar
tsohon nan na dutse da ka gani. Da uwarsu ta ji ina kuka sai ta ce wa uwata,
“Tsaya mana, ki ba yaro ɗan ruwa ya sha. ” Ta tsaya, uwarsu ta ɗauke, ta ba ni ruwa da
kanta.
“Da uwata za ta tashi, sai uwar su
liman ɗin nan ta kawo hure, da
goro, da hannun ruwa, ta ba ta. Ta kawo kwabo biyu ta ba ni, na riƙe kwabo a kowane hannu ina wasa. Tana tsammani uwata mutum
ce. Ba ta san aljana ba ce.
Da uwata za ta wuce, ta tambaye ta
gidansu, ta nuna mata. Bayan kwana uku sai uwata ta zo mata da dare, ta bayyana
mata ko ita wace ce, suka yi abuta. Uwar Liman kuwa tana goyon tsohon nan da ka
gani a kogon dutse.
Iyayenmu suka gama mu abota da muka
girma har yanzu kuwa muna biya juna. Kowane daren Jumma‘a ni kan tafi wurinsa
mu raba dare muna hira. Yau shekarunmu tamanin tamanin ke nan muna ibada cikin
kogo da ni da shi”.
3. 5
Taimakon Juna
A tsarin tarbiyyar Hausawa, taimakon juna yana daga cikin
abubuwan da ke ƙara taimaka wa al’umma ta sami ci gaba
da bunƙasa. cikin wannan littafi na Ruwan
Bagaja, an yi bayani kan muhimmanci aikin taimakon juna. Dalilin irin
wannan aiki ne ya ƙara wa Alhaji Imam ɗaukaka a lokacin da yake
riƙe da sarautar Wawan Sarki. Ga yadda wannan al’amari yake:
“Ana nan ana haka, ran nan sai
babban ɗan Sarki ya tara mu, watau
manyan fadawa, ya ce yana gayyatarmu mu je mu yashe wa iyalansa masai, don watau
bai yarda da kowa ya shiga gidansa ba sai mu yardaddun ubansa. Saboda haka
muka ɗunguma, muka je gidan,
muka fara aiki. Kowa yana yi yana zubad da yawu, don wari. Ni kuwa ina ta waƙa. Cikin waƙan nan tawa na ke zubad da
yawu, ba wanda ya gane abin da nake yi!
Da fa ɗan Sarkin nan ya ga fadawa
na zubad da yawu haka, sai zuciyarsa ta ɓaci. Ya ce musu, “In kashin ya faye
wari, ku bar shi mana ku huta. Wace irin shegantaka ce haka a sa ku aiki kuna
zubad da yawu? Da abinci ne Sarki ya kawo muku da yanzu kuna nan kuna hannu
baka hannu ƙwarya!
Da fa ɗan Sarkin nan ya tunzura
haka, sai ya tafi ya gaya wa ubansa abin da fadawa suka yi masa. Ya ce ni kaɗai ne ban zubad da yawu
ba, sai waƙa na yi ta yi. Da Sarki ya ji haka,
sai ya fusata. Ya sa aka kirawo su duka, ya bi su da ɗai ɗai ya sulluɓe uwa uba. Na ƙwace su da ƙyar. Wannan abin da na yi
fa ya ƙara mini girma ga Sarki da ‘ya’yansa.
”
3. 6 Riƙo da Sana’a
Bahaushe mutum ne wanda yake ba sana’ar da ya gada matuƙar muhimmanci. Wannan dalili ne ya sa a wancan zamani ya
zauna lafiya. Saboda muhimmanci sana’a ne ya sa Bahaushe yake da karin magana
da salon magana waɗanda suke nuna matsayin sana’a a wurin kowace al’umma kamar
haka:
i. Sana’a sa’a rashin sana’a
sata
ii. Sana’a maganin zaman banza
iii. Sana’a goma maganin mai
gasa
da sauransu.
Bisa la’akari da irin wannan tarbiyya ta riƙo da sana’a ne a wurin Hausawa, ya sa marubucin wannan
littafi ya hango muhimmancinsu har ya fito da su cikin wannan littafi a
shafi na 15 kamar haka:
“Duk ‘yan abin hannuna suka ƙare, na rasa abin da zan yi in sami abinci ma. Da dai na ga
abin ya kawo ga haka, sai na fara zuwa su, don tun ina yaro na iya. ”
Haka al’amarin yake, don kuwa a lokacin da Alhaji Imam ya
kai wani gari mai suna Miska, da ɓarayi suka matsa masa don ya sami sauƙin su, sai ya bar masaukinsa na farko ya koma gidan Sarkin
Gardin Kuraye. Ga irin yadda al’amarin ya kasance a shafi na 28 – 29, kamar
haka:
“Da dai na ga ɓarayi sun dame ni da
shigowa, sai na bar unguwar. Na koma gidan wani Sarkin Gardin Kuraye na sauka.
Ina da babban dalilin da ya sa na sauka gidan Sarkin Gardin nan.
Da dai na ji Sarkin Gardin nan ya ce a
ba ni ɗaki in sa kayana, sai na
ce masa, “A’a, ni na fi so in riƙa kwana da kai, in dai
kurayenka suna da takunkumi. ”
Ya ce, “Af! Ai ni ma nan tare da su mu
ke kwana. Me ya sa ka ke son kwana da kuraye?”
Na ce, “Ai tun garinmu na ke sha’awar
kwana da su. Ai ni ma ko gida, gidan Sarkin Gardi na ke barance, shi ya sa na
sauka wurinka. ”
Ya ce, “Madalla. Ashe na gida ne. ”
Bisa la’akari da tarbiyyar Hausawa, an fahimci cewa, kiwo
yana da babban matsayi. Wannan dalili ne ya sa a kowane gida za ka tarar suna
kiwon dabbobi ko tsuntsaye na gida, ko a je daji a kamo domin sayarwa a sami
abin biyan bukatun rayuwa na yau da kullum. Wannan al’amari ya fito sosai a
cikin littafin Ruwan Bagaja, wanda ya ƙara bayyana mana cewa, wannan littafi yana ƙunshe da tarbiyyar Hausawa wadda ta shafi riƙo da sana’a. A iya ganin haka a shafi 32, kamar haka:
“Da na tashi daga nan ban zame ba sai
wani ƙauye ana ce masa Sarai. Na tarad da
mutanen ba su da wata tabi’a sai tarkon aku. In sun kama, sai su yi ta koya
masa magana, su yi ta bin gari suna sayarwa. ”
3. 7 Juriya da Jarunta
A tsarin tarbiyyar Bahaushe yana koya wa ‘ya’yansa juriya
da jarunta yadda a lokacin da ya girma zai iya kare mutuncinsa da na al’ummarsa
da ma na ƙasarsu gaba ɗaya. Idan muka nazarci
wannan littafi na Ruwan Bagaja, za mu ga wuraren da marubucin
wannan littafi ya fito da irin wannan tarbiyya ta juriya. Misali, a shafi 36,
kamar haka:
“Na ƙwaƙwata rairayi, na shiga. Na
yi na yi im mutu, Allah bai nufa. Na nemi wani abu da zan kashe kaina da shi,
na rasa. Ina nan cikin ramin nan ina jiran mutuwa, . . . ”
Idan kuma muka juya wajen jarunta, a nan ma za mu ga
mawallafin wannan littafi ya fito da ita a wurare daban – daban cikin wannan
littafi. Misali, a shafi na 6 cikin wannan littafi, an bayyana irin jaruntar da
Alhaji Imam ya nuna lokacin da ya zo wurin wani dutse cikin ƙungurmin daji, bayan ya yi tafiyar kwana saba’in cikin a
kan hanyarsa zuwa Tambutu. Ga irin jaruntar da Alhaji Imam ya yi, kamar haka:
“Na tasam ma dutse haiƙan, ko da na isa gindin dutse, sai na ga wani babban kogo,
na yi tsammani ba a rasa ruwa cikinsa. Saboda haka, na kutsa kaina ciki, na
shiga. Can na yi zurfi da tafiya, sai na ji an ce, “Kai! Mutum ko aljan?” Da
jin hakanan, sai na kaɗu, hantata ta ɗauki rawa.
Na yi ta maza dai na ce, “Mutum ne. ”
Daga nan fa sai na ga wani tsoho ya taso mini tukuf da shi, yana da tasbaha a
hannunsa. Ya tambaye ni labarina, na kwashe masa duk, tun daga farko har ƙarshe. ”
Haka kuma, a shafi na 36 na wannan littafi Alhaji Imam
ya ƙara nuna jarunta a lokacin da yake
cikin rairayi lokacin da wasu aljannu suka ɗauko wani ɗan Adam, kamar haka:
“. . . sai na ga waɗansu aljannu guda biyu
sun ɗauko wani ɗan Adam. Suka suka sauke
shi nan kusa da ni kaɗan, suka tona rairayi kamar shan ɗaki. Sai na ji babban ya
ce, ”Bi hurmati Sulaimanu Ibnu Dawuda, iftah!” Sai na ga ƙasa ta buɗe, suka shiga da mutumin. . . . . . . . . . Can sai na ga
sun fito, sun ce ”Bi hurmati Sulaimanu Ibnu Dawuda, igliƙ. Sai na ga ƙasa ta rufe.
Wucewarsu ke da wuya sai na fito, na
tafi wurin, na share rairayin da suka mayar, na ce, ”Bi hurmati
Sulaimanu Ibnu Dawuda, iftah!” Sai na ga ƙofa ta buɗe, na kutsa kai na shiga. Ko da mutumin nan da aka rufe ua
gan ni, sai ya taso ya faɗi gabana, ya ce, “Don Allah ka yi mini rai!” Na tambaye shi
sunansa da kuma inda ya fito, duk ya kwashe ya gaya mini. Sai na ji ashe dai
wannan nan nawa ne Saƙimu, agolan ubammu, wanda
ya kashe shi, ya sa kuma a kashe iyayemmu mata don mafarkin can da na gaya muku
ya yi na ɗan dabino. ”
“Ko da na gane haka, sai maganar
fassarar mafarkin malaman nan ta faɗo mini. Na duba gaba gare mu kaɗan sai na ga wani takobi
mai kuben zinari. Na ɗauka na zare shi, sai na ga an rubuta kalmar shahada a
gefensa. Na dubi mutumin nan na gaya masa ni ko wane ne. Na ce masa ya tuna da
fassarar mafarkin da ka yi masa? Na kuma gaya masa yadda aka yi har aka haife
ni, da yadda na tashi duka. Ko da ya ji haka sai ya zaburo mini. Na sa takobin
nan na ɗauke kansa. Na ce, “Kafin
a zo a kashe ni na rama wa baba. ”
3. 8 Kara da Alkunya
Bisa al’ada da kuma tarbiyya an fahimci cewa, Bahaushe
mutum ne mai nuna matuƙar kara da alkunya a
dukkan al’amarin rayuwa, domin kuwa yana yin dukkan biyayya ga abokin
mahaifinsa, ko abokin wansa, da dukkan wanda ya girme shi. Shi kuma babba yana
iya riƙe ƙannensa da ‘ya’yansu da
‘ya’yan dangi na kusa da na nesa, da ma waɗanda ba a gama kome da su ba. Idan kuma wata hidima ta
shafe shi ko wani na kusa da shi, ko kuwa don neman suna, yana iya shiga bikin
da bai shafe shi ba ya yi ruwa ya yi tsaki don a san da shi. Haka kuma, saboda
kunya, za a tarar a wasu lokuta wasu abubuwa waɗanda ka iya cuta masa, amma sai ya
kauda kai daga gare su. Marubucin littafin Ruwan Bagaja, ya
yi ƙoƙarin fito da wannan ginshiƙi na tarbiyyar Hausawa a cikin wannan littafi. Misali, a
shafi na 3, saboda kara ta sa Malam Na-Bakin-Kogi mahaifin Alhaji Imam, ya riƙe Saƙimu wanda agola ne a
wurinsa, kamar haka:
“Amma ko da shi ke malamin nan ba shi
da ɗa na cikinsa, yana da wani
agola, shaiɗani, ana kiransa Saƙimu, kome uban nan nawa ya yi masa uwar ba ta godewa, shi
yaron ba shi godewa. ”
Saboda muhimmanci kara ga Bahaushe ne ya sa ƙarami yake ɗauke wa manya bugu, ko kuwa ya yi musu aikin da ba sa iya
yi, ko da suna iya yi saboda alkunya sai ya karɓa ya yi musu. Idan kuma na fita kunya
ne, sai ya sayar da ƙarfinsa don ya fitar da su
kunya. An fito da irin wannan tarbiyya ta Hausawa cikin wannan littafi a shafi
na 6, inda saboda tozartawar da Sarki ya yi wa Liman wanda shi yake auren
mahaifiyar Alhaji Imam kuma ya ɗauke shi kamar ɗan da ya haifa da cikinsa, ya sa Alhaji Imam ya sayar da
ransa, ya kuma ɗauki niyyar sai ya samo Ruwan Bagaja don ya fitar da Liman
daga wannan kunya da ya ji kamar haka:
“Ko da na ji baba ya ce haka, sai
raina ya ɓaci, hankalina ya tashi. Da komawata gida, sai na ɗauki ‘ya sandata, shiga
gida, nanemi gafara ga iyayena, na ce za ni yawon duniya. ”
Don ƙara ƙarfafa wannan niyya tasa ta yi wa Liman kara, duk da
kasancewar an bayyana wa Alhaji Imam irin matsaloli da wuyar da zai fuskanta
wajen neman Ruwan Bagaja wanda ba hannun mutane yake ba, a hannun aljunnu yake,
bai nuna kasala ba. Daga ƙarshe ma a shafi na 6 – 7,
ya bayyana cewa, sai dai ya mutu wajen neman Ruwan Bagaja, kamar haka:
“Da ya gama labarinsa na ce, “To, tun
da dai akwai shi a duniya, sai im mutu gun nemansa. Don Liman ba shi ya haife
ni ba, ba ni bari a kunyatad da shi. ”
Haka kuma, a shafi na 10 cikin wannan littafi, irin wannan
al’amari ya faru inda aka bayyana cewa, saboda irin yadda Alhaji Imam ya shiga
cikin hidimar bikin ɗan Sarkin Yamel ya sa ya sami ɗaukaka sosai a wannan
gari, ya kuma ƙulla abota da ɗan Sarki wanda aka yi wa
biki, kamar haka:
“Bayan na ƙara ‘yan kwanaki sai na isa wani gari mani’imci wai shi
Yamel. Ko da na fuskanto garin sai na yi ta jin ganguna da kalangai suna tashi,
su kakaki, da farai, da algaitu, sai busa su a ke yi. Shagali dai ba kama
hannun yaro. Ina tafiya sai na ga wani yaro yana ta gudu za shi wurin biki. Na
kira shi na ce. “Kai samari, yau garin lafiya?”
Yaron ya ce, “Mowar Sarki aka kawo wa
mata yau. ”
Na ce, “Daga ina?”
Yaron ya ce, “Yar sarkin Ƙaryatun Ni’ima ce aka gama su. ”
“Ko da na shiga garin, ban ko zauna ba
sai ƙofar fada wajen da a ke biki. Na shiga
biki, na yi ruwa na tsaki, kamar ƙanena aka sa a lalle. Nan
da nan duk na shahara ga maroƙa, suka tambayi sunana. Na
ce, “Alhaji Imam. ” Ana biki da dala dala. Amma ni fam guda guda, na ke yi”.
“Wannan shagali da na yi ya sa Sarki
ya yi maraba da ni Muka yi abota da ɗan Sarki, dare kaɗai ya ke raba mu”.
“Gisuwa ko ina daga gidajen fadawa, da
attajirai, da malamai da sauran manyan gari. Da haka fa duk na azzama cikin
garin ƙasar. Saboda haka a wurina masu laifi
ke kamun ƙafa. Masu son sarauta gare ni suke
nemanta”.
Idan muka nazarci wannan bayani da ya gabata, za mu fahimci
cewa, Alhaji Imam ya sami ɗaukaka a birnin Yamel saboda irin kara da ya nuna a wurin
bikin ɗan Sarki duk da ba a san
shi ba. Watau ya shiga cikin bikin inda ya yi ruwa ya yi tsaki kamar ana
bikin ƙanensa. Wannan kuwa ya faru ne, saboda
a tsarin tarbiyyar Bahaushe ta gargajiya, wadda ta yi horon idan wata hidima ta
sami ‘yan’uwa ko abokan arziki, za su zo a yi hidimar da su don ƙara nuna kara da alkunya.
Ba a nan wannan al’amari na nuna kara ya tsaya ba, don kuwa
Sarkin Aljannu da kansa ya yaba da irin karar da Alhaji Imam ya nuna wa Liman
duk da kasancewar ba shi ya haife shi ba a shafi na 37, kamar haka:
“Na gaya masa abin da ya kawo ni tun
daga farko har ƙarshe ban ɓoye masa kome ba, har da
labarin Saƙimu wana. Ya yi mamaki, ya ce, “Lalle
ka cika ɗa, tun da ka sai da ranka don uban wani. ”
4. 0 Kammalawa
Hausawa na yi wa saniya kirari da suke cewa, “Nagge daɗi goma ba na zubarwa. ”
Haka wannan al’amari yake idan aka danganta wannan karin magana da
ire-iren ƙunshiyar da take cikin littafin Ruwan
Bagaja. Dalilin da ya sa na ambaci haka kuwa shi ne, dukkan wanda ya
nazarci wannan littafi zai tarar yana ƙunshi da abubuwa masu
tarin yawa waɗanda suka shafi dukkan rayuwar Hausawa ta gargajiya, wadda
ta sami nason addinin Musulunci da kuma zamananci. Haka kuma, wannan littafi
ya ƙunshi wasu abubuwan waɗanda suka shafi tarihi, da
labarin ƙasa, da tafiye – tafiye waɗanda suka bayyana halin
zamantakewar Hausawa. Kamar yadda aka gani a bayanan da suka gabata na wannan
takarda, an yi ɗan ƙoƙarin kawo wani ɓangare na al’adun Hausawa kamar yadda wannan littafi
na Ruwan Bagaja, ya hango su, watau tarbiyyar Hausawa. A
wannan mahanga, an kawo bayanai waɗanda suka bayyana tarbiyyar Hausawa dangane da yadda aka
fito da ita cikin wannan littafi wadda ta shafi kiyaye dokokin addini, da
biyayya ga shugabanci, da gaskiya da riƙon amana, da sadar da
zumunci, da taimakon juna, da riƙo da sana’a, da kuma
juriya da jarunta.
Manazarta
Al-Bukhari, M. I. (Ba
Ranar Bugu) Al-Sahihul Bukhari, Beirut-Lebanon: Dar-al-Fikr.
Alhassan, H. da Wasu, (1982) Zaman
Hausawa. Zariya: Institute of Education Press, ABU.
Muhammadu Bello, U. Ɗ. (Ba
Ranar Bugu) Fassarar Maƙala Mai Taken Usul al-Siyasa, Babu Sunan
Wanda ya Fassara ta Zuwa Harshen Ingilishi.
Emarah, M. R. (1430 AH, 2009) Fassarar
Littafin ‘Al-Kbae’r (The Major Sins) Zuwa harshen
Ingilishi, El-Mansoura – Egypt, Dar Al-Manarah.
Gumi, A. M. (1979/1399A.
H. ) Tarjamar Ma’anonin Alƙur’ani Zuwa Harshen Hausa.
Beirut-Lebanon: Dar-al-Arabia.
Gusau, A. R. (2004) Faɗakar da Al’umma a kan Riƙo da Sana’a, Fassarar Littafin Tanbitul
Ummati Alal Tikhadhil Hirfati, Wanda Muhammadu Sambo Ɗan Ashafa ya Wallafa. Gusau: Farin Batu Digital Press.
Ibrahim, M. S. (1982)
”Dangantakar Al’ada da Addini:Tasirin Musulunci kan Rayuwar Hausawa ta
Gargajiya, Kundin Digiri na Biyu. Kano: Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya,
Jami’ar Bayero.
Imam, A. A. (1966) Ruwan
Bagaja. Zariya:NNPC.
Isah, Z. (2006) “Gaskiya a
Tunanin Hausawa”, Kundin Digiri na Farko. Zariya: Sashen Nazarin Harsunan
Nijeriya da Afirka, Tsangayar Fasaha, Jami’ar Ahmadu Bello.
Sallau, B. A. “Tarbiyyar
Hausawa a Matsayin Ginshiƙi na Samar da Ingatacciyar
Al’umma”, Takarda da aka Gabatar a Babban Taron Ƙasa na Farko, Wanda Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya,
Jami’ar Bayero, Kano, ta Gudanar a kan Harshe da Adabi, da Al’adu, Daga Ranar
Litinin 14 Zuwa Laraba 16 ga Watan Janairu, 2013.
Smith, M. G. (1957)
"The Hausa System of Social Status", in Africa Vol. ƊƊƁII. No. 1.
Shu’aibu, M. (2003)
“Gurbin Gaskiya Cikin Adabin Hausa”, Kundin Digiri na Biyu. Sakkwato: Sashen
Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.
Yahaya, I. Y. (1988), Hausa a Rubuce: Tarihin Rubuce-Rubuce Cikin Hausa. Zariya: NNPC.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.