Ticker

6/recent/ticker-posts

Taskace Da Adana Wakokin Hausa A Rubuce Domin Amfanin Gobe

Taskace Da Adana Waƙoƙin Hausa A Rubuce Domin Amfanin Gobe

Daga

Farfesa Bashir Aliyu Sallau
(Sarkin Askar Yariman Katsina Hakimin Safana)
Sashen Koyar da Hausa
Jami’ar Gwamnatin Tarayya Dutsin-Ma
Jihar Katsina-Nijeriya 

 

Tsakure

Dukkan abin da ake son ya zama mai inganci dole a taskace shi, kuma a adana shi yadda zai zama mai amfani gobe. Waƙoƙin Hausa sun daɗe ba tare da samun ingantaccen adani a rubuce ba musamman waƙoƙin baka da rubutattun waƙoƙi waɗanda aka rera kafin da kuma cikin Ƙarni na 19.  Dalili kuwa shi ne, babu wasu hanyoyin na yin ɗab’i kafin da kuma cikin Ƙarni na 19. Shigowar Turawa ƙasar Hausa a farkon Ƙarni na 20 da kafa makarantu da kwalejoji da jami’o’i da kuma maɗaba’u sun taimaka samun hanyoyin wallafa waƙoƙi musamman rubutattu waɗanda aka rubuta da Hausa Ajami ko aka fassara daga Larabci ko wasu harsuna da kuma waɗanda aka rubuta da Hausa ta hanyar amfani da haruffan Romanci. Wannan al’amari ya taimaka matuƙa wajen adana da taskace rubutaccin waƙoƙi a rubuce da waƙoƙin baka na Hausa da kuma waƙoƙin baka na zamani waɗanda ake amfani da kayan kiɗa na zamani wajen rera su. Munufar wannan takarda shi ne ta bibiyi tarihi da asalin samuwar waƙa a ƙasar Hausa da rabe-raben waƙoƙin Hausa da hanyoyin da aka bi wajen taskace su da adana su a matsayin littattafi ko Diwani don amfanin gobe. Hanyar da aka bi wajen gudanar da wannan bincike ita ce, waiwayen ayyukan da magabata suka gudanar a fannin waƙoƙin Hausa waɗanda suka taimaka aka taskace su a wannan zamani. Daga ƙarshe wannan bincile ya gano ire-iren gudummuwar da gwamnati da hukumomin gwamnati da ma waɗanda ba na gwamnati ba, da kuma makarantu da jami’o’i da maɗaba’u na gwamnati da masu zaman kansu na cikin gida da na waje suka ba da wajen taskace da adana waƙoƙin Hausa a rubuce a wannan zamani. 

Gabatarwa

Shirya waƙar baka ta Hausa da rera ta daɗaɗɗen al’amari ne a ƙasar Hausa, amma rubuta waƙa sabon al’amari ne da ya samu sakamakon shigowar Larabawa da karɓar addinin Musulunci da Hausawa suka yi. Wallafa rubutacciyar waƙa da waƙar baka ta Hausa a matsayin bugaggar ƙasida ko bugaggen littafi ko Diwani da kuma yin cikakken nazarinsu ya samu ne sakamakon shigowar Turawa da kawo ilimin zamani a ƙasar Hausa. Dangane da haka, nazarin Hausa a matsayin fannin ilimi ya kasu zuwa manyan ɓangarori guda uku waɗanda suka haɗa da Nazari Nahawu da Nazarin Al’adu da kuma Nazarin Adabi. Dukkan waɗannan ɓangarori uku na nazarin Hausa, nazarin adabi musamman rubutacciyar waƙa ce ta fara samun karɓuwa da tagomashi a tsakanin masu rubutu da nazarin Hausa a Ƙarni na 20. Wannan kuwa ya faru ne sakamakon karɓar addinin Musulunci wanda ya buɗe kofar koyon rubutu da karatu a wajen Hausawa tun cikin Ƙarni na 13 da na 14. Daga bisani wasu ɗalibai da masana harshen Larabci cikin Hausawa suka sami dabara da hikima wadda ta kai su ga sarrafa haruffan Larabci zuwa harshen Hausa da sunan rubutun Ajami (Ibrahim, 1982: 82-85). Rubutacciyar waƙar Hausa ta fara samun karɓuwa da ɗaukaka a tsakanin Hausawa a cikin Ƙarni na 19 lokacin da bayan jihadin Shehu Usmanu Ɗanfodiyo. A wancan lokaci Shehu Usmanu Ɗanfodiyo da wasu magoya bayansa sun rubuta waƙoƙi masu yawa cikin Hausa Ajami ko fassara wasu zuwa Hausa don yin wa’azi ko faɗakarwa ga mabiyansu da yaɗa addinin Musulunci ga al’ummomin da suke zaune a ƙasar Hausa (Bosso, 2010: ɗiɗ). Daga cikin waɗanda suka riƙa taimaka wa Shehu Usmanu Ɗanfodiyo wajen rubuta waƙoƙi cikin Hausa Ajami ko fassara su daga Larabci zuwa Hausa Ajami, akwai ƙanensa Abdullahi Ɗanfodiyo da ɗansa Muhammadu Bello da ‘yarsa Nana Asma’u da Dikko ɗan Bagine da Muhammadu Tukur da Isan Kware da sauransu.

A wancan lokaci dukkan waɗannan waƙoƙi da hannu aka rubuta su ba su sami bugawa irin ta ɗab’i ba, sai a Ƙarni na 20 lokacin da Turawan Mulkin Mallaka suka kawo ilimin zamani da dabarun wallafa rubutattun ayyuka. Kafa Kwalejin Abdullahi Bayero ta Kano ƙarƙashin Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya, wadda a yau ake kira Jami’ar Bayero ta Kano, da kuma kafa wasu hukumomi waɗanda suka haɗa da Hukumar Fassara wadda daga baya aka sauya mata suna da aiki ta koma Hukumar Talifi, da Hukumar NORLA, sai kuma Kamfanin Buga Littattafai na Arewacin Nijeriya (NNPC) da kanfanin Gaskiya, sun taimaka matuƙa wajen wallafa waƙoƙin da aka rubuta a Ƙarni na 19 da Ƙarni na 20. Daga baya kuma an sami wasu kamfanoni na cikin gida da kuma na ƙasashen waje waɗanda suka riƙa wallafa waƙoƙi da aka rubuta da Hausa Ajami ko da Hausa da aka yi amfani da haruffan Romanci.

Rubutu da wallafa rubutattun waƙoƙin Hausa da waƙoƙin baka na Hausa ya sami ƙarin cigaba da tagomashi a Ƙarni na 21. Wannan kuwa ya faru ne sakamakon sha’awa da ta ƙaru tsakanin matasa masu karatu a Makarantun Islamiyya a inda aka riƙa koya wa ɗalibai waƙoƙin tauhidi da yabon Allah, Maigirma da ɗaukaka, da bege da yabon Annabi Muhammadu, tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a gare shi, musamman a lokacin Maulidi. Wannan al’amari ya taimaka wajen samuwar shahararrun sha’irai waɗanda bayan waƙoƙin tauhidi da yabon Annabi, sai suka ƙara da yi wa wasu mutane ko wasu al’amuran rayuwa waƙoƙi. Wasu daga cikin waɗannan sha’irai, domin su ƙara armashi ga waƙoƙinsu suna amfani da hanyoyin sadarwa na zamani irin Sitidiyo da ake saka kaɗe-kaɗe na gargajiya ko na zamani ko tafi da hannu don su tafi tare da waƙoƙinsu.

Haka kuma, a wannan Ƙarni na 21 an ƙara samun wata dama wadda ta buɗe hanya ga marubuta da masana adabin Hausa adana waƙoƙin baka na Hausa da rubutattun waƙoƙin Hausa da waƙoƙin da ake rerawa a Sitidiyo zuwa manyan kundaye da ake kira Diwani, watau littafin da ya tattara waƙoƙi, musamman na mutum ɗaya (Ƙamusun Hausa, Jami’ar Bayero, 2006:106).

Dangane da haka, maƙasudin wannan takarda shi ne ta duba muhimmancin adana da taskace waƙoƙin Hausa a rubuce, musamman waɗanda aka fara wallafawa a matsayin littattafai tun daga shekara ta 1953 zuwa 1983 da kuma Diwanin Waƙoƙin Baka na Hausa Juzu’i na 1-6, waɗanda Farfesa Sa’idu Muhammad Gusau ya wallafa da kuma Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA) wanda Farfesa Salisu Ahmad Yakasai da Abu Ubaida Sani suka wallafa da kuma Diwanin Wasu Waƙoƙin Malam Abubakar Kantama wanda Adamu Mainasara ya wallafa.

Waiwaye kan Asalin Samuwar Waƙa a Ƙasar Hausa

Masana adabin Hausa sun bayyana cewa waƙar Hausa a Ƙarni na 21 ta rabu zuwa kaso uku waɗanda kowane kaso yana da ƙananan rassa waɗanda suke ɗauke da saƙonni iri daban-daban. Kaso na farko na waƙar Hausa shi ne waƙar baka ta Hausa, kaso na biyu shi ne rubutacciyar waƙar Hausa, daga nan sai waƙar Fiyano wadda ake rera ta a Sitidiyo.

Yana da matuƙar wuya a ce ga lokacin da Bahaushe ya sami dabarar tsara waƙar baka da rera ta, amma masana irin su Gusau, 2003: 5-9, sun kawo wasu hasashe waɗanda suka ba da haske wajen samuwar waƙar baka ta Hausa. Hasashen na tsammanin cewa:

Ø  Waƙar baka ta Hausa ta samo asali ne daga wani maroƙi da ake kira Sasana. An ce, shi Sasana asalinsa mutumen Asiya ne, daga baya wasu daga cikin ‘ya’yansa da jikokinsu suka yi wo ƙaura har suka shigo ƙasar Hausa. Wannan dalili ne ya sa ake yi wa maroƙa da mawaƙan baka na Hausa laƙabi da bani-Sasana.

Ø  Hasashe na biyu an bayyana cewa, waƙar baka ta Hausa ta samo asali ne daga bautar gargajiya da Hausawa suka bauta wa iskoki ko mutanen ɓoye. Lokacin bauta suna yi wa waɗannan iskoki zuga ta hanyar kirari da kaɗe-kaɗe domin neman biyan bukatu daga gare su. Wai ta wannan hanya ce kiɗa da waƙa ya samu a wajen Hausawa.

Ø  Wani hasashen kuma ya bayyana cewa, an sami waƙar baka ta Hausa daga tsofaffin daulolin Afirika ta Yamma wato Ghana da Mali da Songhai. Wannan ra’ayi ya bayyana cewa, tun daga lokacin daular Mali har zuwa ta Songhai sarakunan waɗannan dauloli suna da makaɗan fada waɗanda suke yi musu kiɗa da waƙa na zuga da yabo da yin zambo ga maƙiyansu da abokan hamayyarsu. An bayyana cewa, ikon daular Songhai ya malalo har zuwa cikin wasu sassa na ƙasar Hausa musamman ɓangaren yamma. Wannan dalili ne ya sa mafi yawancin makaɗan fada na ƙasar Hausa aka fi samun su daga ƙasar Hausa ta yamma kamar Argungu da Gobir da Zamfara.

Ana amfani da manya da ƙananan turaku wajen gina waƙoƙin baka na Hausa waɗanda suka haɗa da:

ü  Turken yabo

ü  Turken zuga

ü  Turken yabo mai tafiya da zuga

ü  Turken zuga mai tafiya da yabo

ü  Turken zambo

ü  Turken faɗakarwa

ü  Turken tarihi

ü  Turken ta’aziyya

ü  Turken roƙo

ü  da sauransu (Gusau, 2008: 376-390)

Mawaƙan baka na Hausa na amfani da waɗannan turaku wajen isar da saƙo ko saƙonni a cikin waƙoƙinsu don zuga ko yaba wa waɗanda suke yi wa waƙa. Haka kuma, suna isar da wani muhimmin saƙo zuwa ga al’umma kan wasu al’amuran rayuwa don yin hannun-ka-mai-sanda ko jawo hankalin al’umma kan abubuwan da suka dace a yi da waɗanda ba su dace a yi ba. A wasu waƙoƙin baka na Hausa za a tarar tun daga farkon ɗan waƙa har zuwa ɗa na ƙarshe, mawaƙi ya tsaya kan turke ɗaya ba tare da shigo da wani turke ba, amma a wasu waƙoƙin za a tarar wasu turakun suna shiga cikin babban turken da aka gina waƙa da shi don a ƙara wa waƙar armashi. Farfesa Sa’idu Muhammad Gusau na Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero ta Kano yana gaba-gaba cikin masana adabi da suka ba da gudummuwa wajen ƙirƙiro hanyoyi ko dabarun nazarin waƙar baka ta Hausa. Dangane da haka ne, ya wallafa littafi mai suna, Jagoran Nazarin Waƙar Baka. Daga na kuma sai Farfesa Abdullahi Bayero Yahya na Sashen Koyar da Harsuna, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo Sakkwato. Shi ma a littafinsa Salo Asirin Waƙa ya fito da hanyoyin masu yawa da za su taimaka wa mai nazarin waƙar baka ta Hausa.

Daga cikin mawaƙan baka na Hausa akwai:

·         Ibrahim Narambaɗa Tubali Isa

·         Salihu Jankiɗi Rawayya

·         Aliyu Ɗandawo

·         Kurna Maradun

·         Musa Ɗanƙwairo

·         Mamman Shata Katsina

·         Ɗanmaraya Jos

·         Kassu Zurmi

·         Haruna Uji Gandun Sarki Hadejiya

·         Muhammadu Bawa Ɗan’anace

·         Mamman Sagalo Nijar

·         Iro Mai Komo Kurfi

·         Idi Ɗan Galma Musawa

·         da sauransu ((Gusau, 2008: 163-185))

Ita kuma rubutacciyar waƙar Hausa ta samo asali ne sakamakon shigowar Wangarawa da Larabawa waɗanda suka kawo addinin Musulunci ƙasar Hausa. Karɓar addinin Musulunci da mafi yawancin Hausawa suka yi ya taimaka masu wajen koyon rubutu da karatun Larabci wanda daga baya aka ƙirƙiro sarrafa haruffan Larabci zuwa Hausa Ajami. Ingantattun bayanai sun bayyana yadda Shehu Usmanu Ɗanfodiyo da mabiyansa suka rubuta waƙoƙi cikin Hausa Ajami don yin wa’azi da yaɗa addinin Musulunci da koya rera su ga almajirai da makafi da ke yawo suna bara da su cikin sigar wa’azi (Ɗangambo, 2007: 1). Masana sun raɗa wa waɗannan waƙoƙi suna Waƙoƙin Ƙarni na 19, kuma suna ɗauke da jigo ko saƙon tauhidi da wa’azi da yaɗa addinin Musulunci da yabon Annabi Muhammadu, tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a gare shi, da yabon wasu waliyyai ko salihan bayin Allah waɗanda ake son yin koyi da ayyukansu masu kyau.

Rubutacciyar waƙar Hausa ta ƙara samun bunƙasa sakamakon shigowar Turawa ƙasar Hausa da suka kafa makarantun boko a cikin Ƙarni na 20, waɗanda suka koyar da rubutu da karatu ta hanyar amfani da haruffan Romanci. Kafa Kwalejin Abdullahi Bayero a Kano wadda a yau ake kira Jami’ar Bayero ta Kano ya taimaka sosai wajen rubuta da nazarin rubutattun waƙoƙin Hausa. Wannan kuwa ya faru saboda, wannan Kwaleji wadda daga baya ta koma cikakkiyar Jami’a, ita ce makaranta ko cibiya ta farko a duk faɗin Nijeriya da aka fara koyar da karatun Hausa (Ɗangambo, 2007: 2). Rubutattun waƙoƙin Hausa waɗanda aka riƙa rubutawa da haruffan Romanci ana kiran su da sunan Waƙoƙin Ƙarni na 20, kuma jigonsu da saƙon da suke isarwa ga al’umma ya ɗan sha bamban da jigo da saƙon Rubutattun Waƙoƙi na Ƙarni na 19. Wannan kuwa ya faru ne saboda sun fi mayar da hankali kan al’amuran duniya waɗanda suka haɗa da jigo kan siyasa da faɗakarwa da soyayya da yabo da zuga da sauransu. Manyan masana adabin Hausa irin su Farfesa Ɗalhatu Muhammad da Farfesa Ɗandatti Abdulƙadir da Farfesa Abdulƙadir Ɗangambo sun bayar da gagarumar gudummuwa wajen ƙirƙiro hanyoyi ko dabarun nazarin rubutacciyyar waƙar Hausa. Littafin Farfesa Abdulƙadir Ɗangambo Ɗaurayar Gadon Feɗe Waƙa (2007) ya fito da matakai da hanyoyin da za a yi nazarin rubutacciyar waƙar Hausa.

Daga cikin marubuta waƙoƙin Hausa akwai:

§  Mujaddadi Shehu Usmanu Ɗanfodiyo

§  Sarkin Musulmi Muhammadu Bello

§  Nana Asma’u ‘yar Shehu Usmanu Ɗanfodiyo

§  Dikko Ɗanbagine

§  Sarkin Zazzau Aliyu Ɗan Sidi

§  Aliyu Namangi

§  Mu’azu Haɗejiya

§  Sa’adu Zungur

§  Aƙilu Aliyu

§  Mudi Sipikin

§  Baba Maigyaɗa Agege

§  Barmo Birkila Katsina

§  Lawal Ɗan Halilu Katsina

§  Shehu Maigidaje Funtuwa

§  Malumman Matazu

§  da sauransu.

Kaso na uku na waƙoƙin Hausa su ne waƙoƙin Sitidiyo waɗanda suka samo asali daga waƙoƙin samartaka. Waƙoƙin samartaka bisa asali samari da ‘yan mata ne suke rera su da fatun baki, ana kuma adana su da ka. Yana da matuƙar wuya a ce ga lokacin da aka fara waƙoƙin samarta a ƙasar Hausa, domin kuwa ana tsammanin sun kai kimanin shekaru dubu ɗaya ana aiwatar da su (Gusau, 2008 :345).

Waƙoƙin samartaka suna da nau’o’i daban-daban waɗanda suka haɗa da:

ü  Waƙoƙin saurayi da budurwa na soyayya.

ü  Waƙoƙin ango da amarya.

ü  Waƙe-waƙen kuruciya na samari waɗanda suke tafiya da kiɗan disko.

ü  Waƙe-waƙen kuruciya na ‘yan mata waɗanda suke yi lokacin bukukuwa.

ü  Waƙe-waƙen yabon Annabi Muhammadu, tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a gare shi, musamman lokacin Maulidi ((Gusau, 2008: 345).

Domin ƙara armashi ga waɗannan waƙoƙi ana haɗa waƙoƙi na samarta da tafa hannu don su ba da amon da ake buƙata. Sannu a hankali aka gano amfani da kayan kiɗa na gargajiya na Hausawa waɗanda suka haɗa da kalangu ko ganga ko kuma kazagi. Sakamakon shigowar Larabawa da Turawa an sami wasu kayan kiɗa na zamani waɗanda suka haɗa da mandiri da fiyano da jita. Wasu samarin sai suka riƙa haɗa kayan kiɗa na gargajiya da na zamani, misali a haɗa kalangu da jita da sarewa ko fiyano da shantu ko goge ko kuntigi ko molo da sauransu (Gusau, 2008 :347).

A ƙasar Hausa Makaɗa Bala Miller yana daga cikin waɗanda suka fara assassa rera waƙar Hausa da kiɗan Fiyano. Sai kuma wata mawaƙiyar Bayarabiya mai suna Funmi Adams wadda ita ma ta riƙa rera waƙoƙin Hausa ta amfani da kayan kiɗa na Turawa da suka haɗa da jita da fiyano da tasoshi da kuma ganguna. Bayan waɗannan makaɗa akwai wasu irin su Sa’adu Bori makaɗi mutumen Jamhuriyar Nijar da kuma Nasiru Ustaz waɗanda suka riƙa rera waƙoƙin Hausa ta amfani da kayan kiɗan Turawa.

Wannan sabon salon kiɗa da waƙa ya sami karɓuwa wajen matasan Hausawa maza da mata, kuma Kamfanin Iyantama Multi Media ya taimaka wajen bunƙasa wannan salon kiɗa da waƙa, don kuwa shi ne ya fara yin kiɗa na fiyano yana haɗa shi da waƙoƙin soyayya da na amarya da ango da sauransu. Sannu a hankali sai aka riƙa amfani da waɗannan waƙoƙi da kiɗan fiyano ana saka su cikin finafinan Hausa.

A yau, a iya cewa wannan sabon salon kiɗa na fiyano ya karaɗe dukkan faɗin ƙasar Hausa, domin kuwa matasa masu yawan gaske sun rungume shi a matsayin sana’a wadda suka dogara kanta don biyan bukatun rayuwarsu ta yau da kullum. Ga wasu daga Cikinsu:

Aminu Ladan Abubakar Alan Waƙa

Mudassiru Ƙassim

Abubakar Sani Ɗanɗago

Adam A. Zango

Sani Danja

Sadi Sidi Sharifai

Dauda Kahutu Rarara

Baban Chinedu

Maryam A. Baba

Binta Labaran (Fati Nijar)

Ali Jita

Sanusi Anu Sabuwar Unguwa Katsina

Auwal Bashir Aliyu (Malam A)

Taskace da Adana Waƙoƙin Hausa a Rubuce Jiya da Yau

Hukumar Adana Ayyukan Adabi ta Arewacin Nijeriya (NORLA) ce ta fara adanawa da taskace rubutattun waƙoƙin Hausa a shekara ta 1953 inda ta wallafa wata waƙa wadda aka fassara mai suna Zuhudu. Wannan Hukuma ta ci gaba da wallafa wasu ƙirƙirarrun waƙoƙi ko waɗanda aka fassara. Ga wasu daga cikinsu:

Waƙoƙin Mu’azu Haɗeja1955

Waƙoƙin Sa’adu Zungur1955

Gaskiya Maiɗaci ta Salihu Kwantagora1955

Waƙoƙin Hausa 1957

Waƙoƙin Mudi Sipikin1959

Imfiraji 1-9   Aliyu Namangi1958

Gangar Wa’azu  (Kamfani Gaskiya)1968

Waƙar Tarihin Rikicin Nijeriya Y. A. BichiNNPC 1973

The Ma’amare of Shehu Usman Ɗanfodio: Ajami Teɗt

and Roman Transcription Uni. of London, SOAS1977

Waƙa A Bakin Mai Ita (1-2) CSNL/BUK1978

Zaɓaɓɓun Waƙoƙi Na Da Da Na Yanzu

D. Abdulƙadir (Kamfanin Nelson) 1980

Alƙalami a Hannun Mata Hauwa Gwaram NNPC 1983

Waƙoƙin Noma, Ƙungiyar Marubuta da Manazarta

Waƙoƙin Hausa, Hukumar Fassara da Al’adu, Sakkwato1983

Daga shekara ta 1953 zuwa shekara ta 1983, Hukumar NORLA da Kamfanin Gaskiya da Kamfanin Buga Littattafai na Arewacin Nijeriya (NNPC) da wasu kamfanoni masu zaman kansu na cikin gida Nijeriya da na ƙasashen waje sun wallafa littattafai guda sittin (60) na ƙirƙirarrun waƙoƙin Hausa ko waɗanda aka fassara daga wasu harsuna (Yaro, 1988: 234-236).

Daga shekarar 1983 zuwa yau an sami ƙarancin samuwar wallafa littattafan waƙoƙin Hausa a matsayin ɗab’i, amma an sami wani cigaba sakamakon samuwar kwalejojin ilimi da jami’o’i waɗanda suka riƙa gudanar da nazarin waɗannan rubutattun waƙoƙi da aka wallafa da waɗanda ba a wallafa ba a matsayin kundin kammala karatu. Ire-iren waɗanda ba a wallafa ba, sai aka riƙa saka su a ƙarshen kundi a matsayin rataye. Duk da haka, an wallafa wasu rubutattun waƙoƙin amma ba su kai yawan waɗanda aka fara wallafawa ba, misali:

ü  Alfiyyar Mu’azu Sani ta Ɗaya zuwa ta Biyar, inda aka waƙe Tsarin Sauti da Tasarifin Hausa a Waƙe da da Ginin Jimlar Hausa a Waƙe da Karorin Harshen Hausa da sauran fannonin nazarin Tsarin Sauti da Nahawu.

ü  Salihu Jankiɗi Sarkin Taushi Farfesa Sa’idu Muhammad Gusau ya sake wallafawa a shekara ta 2002, a ƙarshen littafi an kawo rataye da wasu waƙoƙinsa.

ü  Jagoran Nazarin Waƙar Baka, Farfesa Sa’idu Muhammad Gusau ya wallafa shi a shekara ta 2003, a ƙarshen littafi an yi rataye da wasu waƙoƙin Makaɗa Ibrahim Narambaɗa Tubali Isa.

ü  Waƙoƙin Alhaji Mamman Shata, Diwani na Ɗaya, Hukumar Binciken Tarihi da Kyautata Al’adu ta Jihar Katsina, an wallafa shi a shekara ta 2003.

ü  Waƙoƙin Baka a Ƙasar Hausa: Yanaye-Yanayensu da Sigoginsu, Farfesa Sa’idu Muhammad Gusau ya wallafa shi a shekara ta 2008, a ƙarshen littafin an yi rataye da waƙoƙin wasu mawaƙan baka na Hausa.

ü  Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa, Aliyu Muhammad Bunza, an wallafa shi a shekara ta 2004.

ü  Narambaɗa, Aliyu Muhammad Bunza ya wallafa shi a shekara ta 2009, a ƙarshen Littafin an yi rataye da wasu waƙoƙin Ibrahim Narambaɗa Tubali Isa.

ü  Kassu Zurmi da Waƙoƙinsa, Ahmad Magaji ya wallafa shi a shekara ta 2016. A Rataye na Ɗaya an kawo wasu waƙoƙin Kassu Zurmi.

ü  da sauransu

. Haka kuma, waɗannan makarantu da wasu hukumomi na gwamnati da ma waɗanda ba na gwamnati ba, sun riƙa shirya gasar rubuta waƙoƙin Hausa inda aka riƙa wallafa waƙoƙin da suka yi nasara, misali gasar rubuta waƙoƙin Hausa da aka gudanar a Argungu da Daura. 

 Sakamakon wannan namijin ƙoƙari da waɗannan marubuta waƙoƙin Hausa suka yi na rubuta waɗannan waƙoƙi, ya sa gwamnati ta hanyar hukumominta, da wasu hukumomi waɗanda ba na gwamnati ba, da wasu masu hannu da shuni ɗaukar nauyin wallafa waɗannan waƙoƙi aka mayar da su littattafai waɗanda ake amfani da su har a wannan zamani. Haƙiƙa wannan ƙoƙari da aka yi, ya taimaka wa adabin Hausa musamman waƙoƙin ta hanyar taskace su aka adana su domin amfanin al’ummar wannan zamani da waɗanda suke tafe ta yadda za a sami ilimin duniya da lahira ko don nishaɗi ta hanyar rubutacciyar waƙa ko waƙar baka ta gargajiya da waƙar baka ta zamani waɗanda aka taskace a rubuce.

Taskace Waƙoƙin Hausa da Adana su a Matsayin Diwani

Bayan wallafa waƙoƙin Hausa a littattafai da kundayen bincike na kammala karatu da kuma takardun ƙara wa juna ilimi da mujallu da ƙasidu da aka daɗe ana yi musamman a Ƙarni na 20, an sami cigaba a Ƙarni na 21 inda wasu masana suka ga ya dace a taskace wasu waƙoƙi don adana su yadda ba za su ɓata ba. Farfesa Sa’idu Muhammad Gusau na Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero ta Kano, shi ya fara ɗaukar gabarar gudanar da wannan muhimmin aiki. Daga shekara ta 2009 zuwa shekara ta 2022 ya wallafa Diwanin Waƙoƙin Baka na Hausa guda shida waɗanda suka kawo nau’o’in waƙoƙin baka na Hausa irin daban-daban daga rabe-raben mawaƙan baka na Hausa na jiya da na yau. Daga nan kuma a shekara ta 2021, Farfesa Salisu Ahmad Yakasai da Abu Ubaida Sani sun wallafa Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar ALA. A wannan shekara ta 2023 an sami wani Diwanin mai suna, Diwanin Wasu Waƙoƙin Malam Abubakar Kantama wanda Adamu Mainasara ya wallafa da sauransu.

Diwanin Waƙoƙin Baka Na Hausa: Juzu’i na Ɗaya

Wannan Diwani yana ɗauke da matanoni na wasu waƙoƙin baka waɗanda wasu shahararrun mawaƙan baka na Hausa suka rera. An kasa wannan Diwani zuwa manya babuka biyu. Babi na ɗaya yana ɗauke da waƙoƙin fada waɗanda aka rera wa Sarakuna ko masu riƙe da wata sarauta ko hakimai ko dagatai da shahararrun makaɗan fada suka rera da kuma waƙar Dr. Mamman Shata wadda ya rera wa Sarkin Daura Alhaji Muhammadu Bashar. Ga jadawalin gindin waɗannan waƙoƙi kamar haka;

Wari Mai Zari Gobir – Waƙar Sarkin Gobir Bawa Jangwarzo

Kara Buzu Mai Kan Kuwa – Waƙar Sarkin Kabin Argungu Sama

Abubakar Akwara Sabon Birni – Waƙar Sarkin Gobir Umaru Shawai

Muhammadu Dodo Maitabshi – Waƙar Sarkin Musulmi Hassan ɗan Mu’azu

Ibrahim Gurso Mafara – Waƙar Sarkin Mafara Abubakar Barmo

Salihu Jankiɗi Rawayya – Waƙar Sardaunan Sakkwato, Alhaji Amadu Bello

-          Sarkin Kano Alhaji Abdullahi Bayero

Aliyu Ɗandawo – Waƙar Arɗon Shuni Muhammadu

Waƙar Sarkin Kabi Muhammadu

Sarkin Kabi Muhammadu Argungu

Sarkin Kabin Argungu Muhammadu Sama

Ibrahim Narambaɗa Tubali – Sarkin Gobir na Isa Amadu

Waƙar Sardaunan Sakkwato, Alhaji Ahmadu Bello wadda take da gindin waƙa:

:Ya riƙa da hankali Bello mai tawakkali

: Ɗan Hassan na Sarkin Raɓa giyen Mujaddadi

Mamman Inyaga Argungu – Waƙar Sarkin Kabi Muhammadu Mera

Idi Ɗangiwa Zuru – Waƙar Sarkin Sudan na Kwantagora Alhaji Sa’idu

Iyan Zazzau

Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris

Sarkin Taushin Katsina Alhaji Muhammadu – Waƙar Sarkin Haɗejiya Haruna

Waƙar Sarkin Daura Muhammadu Bashar

Waƙar Sarkin Zazzau Aminu

Waƙar Sardaunan Sakkwato Sir Ahmadu Bello

Alhaji Musa Ɗanƙwairo Maradun – Waƙar Alhaji Ahmadu Bello Sardauna

Waƙar Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero

Waƙar Sarkin Daura Alhaji Muhammadu Bashar

Waƙar ‘Yandoto Tsahe Alhaji Aliyu II

Waƙar Sardaunan Sakkwato Alhaji Ahmadu Bello

Waƙar Sarkin Muri Alhaji Ummaru Abba

Waƙar Ciroman Katsina, Janar Hassan Usman Katsina

da wasu waƙoƙinsa da yawa.

Alhaji Sa’idu Faru – Waƙoƙin Sarkin Musulmi Muhammadu Macciɗo

Umaru Mai sa’a Tubali Isa – Waƙar Magajin Shinkafi Umaru Naguraguri

Waƙar Sarkin Musulmi Abubakar na uku

Sani Aliyu Ɗandawo – Waƙoƙin Sarkin Yawuri Alhaji Muhammadu Tukur

Sarkin Daura Muhammdu Bashar

Turakin Zazzau Alhaji Muhammadu Aminu

Sarkin Gombe Alhaji Shehu

Musa Ɗandada Sabon Birni – Waƙoƙin Sarkin Gobir Salihu Sabon BirniAlhaji Sa’idu Maidaji Rambaɗawa Sabon Birni – Waƙar Sarkin Zazzau Shehu IdrisSarkin Sabon Birni Alhaji Muhammadu Bawa

Innar Gobir Sabon Birni

Sarkin Katsinan Gusau Alhaji Muhammadu Kabir Ɗanbaba

Sarkin Bazai Jangeru Alhaji Muhammadu

Abu Ɗankurma Maru – Waƙar Banagan Maru Ibrahim

Sabon Garin Mayanci Maikano

Abdu Inka Bakura – Waƙar Sarkin Musulmi Abubakar III

Bala Tambaya Jankiɗi Gusau – Waƙoƙin Sarkin Katsinan Gusau Muhammadu

  Kabir Ɗanbaba

Muhammadu Sanƙira Ɗangiwa Zuru – Waƙar Dabai Alhaji Aliyu

Ibrahim Ɗanmaraya Daura – Waƙar Tarihin Sarakunan Daura

   Daga Bayajidda zuwa 1972

Sarkin Kotso Abdulrahman – Waƙar Sarkin Musulmi Abubakar III

Sarkin Kano Alhaji Muhammadu Sanusi

Alhaji Dr. Mamman Shata Katsina - Waƙoƙin Sarkin Daura Muhammadu

Bashar

Waƙar Sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris

Waƙar Sarkin Bauchi Alhaji Suleman Adamu

Waƙar Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero

A babi na biyu na wannan Diwani an kawo waƙoƙi gamagari waɗanda wasu mawaƙan fada da wasu mawaƙa jama’a suka rera wa wasu mutane da wasu al’amuran rayuwa a ƙasar Hausa.

A taƙaice a wannan Diwani Juzu’i na Ɗaya an kawo waƙoƙin baka guda 143 waɗanda mashahuran mawaƙan baka na fada da wasu mawaƙan baka suka rera. Farfesa Sa’idu Muhammad Gusau ya saurare su a tsanaki ya taskace su a rubuce, sannan aka adana su a wallafaffen littafi don amfanin gobe.

Diwanin Waƙoƙin Baka: Juzu’i Na Biyu

Shi kuma Diwani na biyu ya taskace waƙoƙin baka na Hausa na mawaƙan gargajiya masu amfani da kayan kiɗa na gargajiya da kuma mawaƙan zamani waɗanda suke amfani da kayan kiɗan fiyano da jita a sitidiyo. An raba wannan Diwani zuwa rukunoni biyu kamar haka:

Rukuni na Ɗaya ya kawo waƙoƙin Hausa na wasu mawaƙa waɗanda suka haɗa:

Alhaji Dr. Mamman Shata Katsina- Waƙoƙi 10

Sarkin Kotson Kano Alhaji Abdulrahman-Waƙoƙi 2

Alhaji Musa Ɗanƙwairo Maradun -Waƙa 1

Alhaji Sa’idu Faru-Waƙa 1

Alhaji Ɗanmaraya Jos-Waƙoƙi 15

Alhaji Abdu Wazirin Ɗanduna-Waƙa 1

Alhaji Rabo Ango Yabo-Waƙoƙi 3

Magajiya Ɗanbatta- Waƙoƙi 5

Alhaji Muhammadu Bawa Ɗan’anace-Waƙa 1

Abdu Kurna Maradun-Waƙa 1

Yakubu Muhammad- Waƙoƙi 2

Musbahu Muhammad Ahmad-Waƙoƙi 2

Auwalu Hussaini Ƙofar Mazugal- Waƙoƙi 4

Muhammadu Ɗanƙurji- Waƙa1

Babangida Kakadawa Gusau- Waƙoƙi 10

Musa Ƙanen Yalo Maigurmi-Waƙoƙi 10

‘Yanbiyu Sabuwar Ƙasa-Waƙoƙi 4

Sarkin Taushin Kano Alhaji Bala. -Waƙoƙi 2

A rukuni na biyu an taskace wasu waƙoƙin kamar haka:

Alhaji Musa Ɗanba’u-Waƙoƙi 10

Uwaliya Mai’amada-Waƙoƙi 10

Ibrahim Ɗangulbi-Waƙoƙi 3

Alhaji Sani Sabulu Kanoma-Waƙoƙi 9

Alhaji Musa Ɗanƙwairo Maradun-Waƙoƙi 10

Alhaji Shehu Ajilo Ɗanguzuri-Waƙoƙi 10

Alhaji Abdulrashid Ibrahim Mai’asayyaro-Waƙoƙi 2

Aminu Ladan Abubakar Alan Waƙa-Waƙa 1

Nazifi Asnanic-Waƙa 1

Malam Ashana Ɗankama- Waƙa 1

Is’haƙa Hamza Unguwar Mu’azu-Waƙa 1

Murja Baba-Waƙoƙi 10

Ali Makaho-Waƙoƙi 3

Garba Maitandu-Waƙa 1

Haruna Uji-Waƙoƙi 3

Alhaji Dr. Mamman Shata Katsina-Waƙoƙi 6

Abu Ɗankurma Maru-Waƙoƙi 6

Hajiya Yalwa-Waƙa 1

Nazir Muhammad Ahmad, Sarkin Waƙa-Waƙoƙi 3

Almustafa S. El-Amin-Waƙa 1

Hassan Ɗanzabuwa-Waƙa 1

Zayyanu Aƙilu Aliyu-Waƙa 1

Auwalu Nababu Ibrahim-Waƙoƙi 4

Hajara ‘Yargado Mai’amada. -Waƙa 1

A jimlace, a wannan Diwani an taskace da adana jimlar waƙoƙi 372.

Diwanin Waƙoƙin Baka: Juzu’i na Uku.

A wannan Diwani an taskace tare da adana matanonin wasu waƙoƙin Alhaji Dr. Mamman Shata Katsina waɗanda ya rera wa wasu rukunonin mutane da wasu al’amura da suka faru a ƙasar Hausa ko wajen ƙasar Hausa. Waɗannan waƙoƙi da aka kawo, ba a kawo su a Diwani na Ɗaya da na Biyu ba. Shi ma wannan Diwani kamar waɗanda suka gabace shi an raba shi zuwa kashi biyu.

Kashi na farko ya kawo bayani kan wasu muhimman abubuwa dangane da Mamman Shata waɗanda suka haɗa da:

Wasu abubuwan lura a rayuwar Shata

Shata a waƙar baka

 

Kashi na biyu ya duba wasu rukunoni na matanonin wasu waƙoƙin Mamman Lawal Shata waɗanda suka haɗa da:

Waƙoƙin Allahu

- Allah mai aradu mai tarnatsa mai kwaranƙwatsi

- Ya mai sama mai ƙasa Allah

Waƙoƙin Duniya

- Ayyaraye duniya labari

- Inyanyere cene Aradu

Waƙoƙin Annabawa da Waliyyai

- Na tsaya ga Annabi Muhammadu

- Domin Sayyidina Tijjani

Waƙoƙin Masu Sarauta

Sarakuna

- Sarkin Musulmi Bubakar

- Kwana lafiya mai Daura (a)

- Kwana lafiya mai Daura (b)

- Lafiya Zaki

- Mai Daura Bashar ɗan Sanda

- Ado San Kano ɗan Abdu

- Alhaji Sarkin Zazzau Shehu

- Mai Bauchi Sulemanu Adamu

- Sarkin Misau Mamman Manga

- Sarkin Jama’are Amadu

- Zaki Sarkin Haɗeja Maje

- Allah Jiƙan Bahago ɗan Amadu

-Na gode Sule Jikan Korau

- Allah Jiƙan Jibrin mai Gwari

 

Hakimai da Iyayen Ƙasa

- Jikan Dikko Sarkin Arewa

- Mai Rano Garba Autan Bawo

- Ɗankabo Jarmai Mamman

- Tukur Jikan Nadabo (Bakori)

- Sarkin Yamma Muhammadu Tukur (Faskari)

- Malami Sarkin Sudan Shehu

- Haji Bawa Gilban Jibiya

- Sule Jikan Korau

- Idi na Shehu Baban Tukur Makama (Bakori)

- Ya Riƙa sai a bar mai (Hakimin Kaita)

 

Masu Muƙaman Sarauta

- Sardauna Bahago ɗan Hassan

- Sardauna Amadu Gwarzon Giwa

- Sardauna Kakanka Ɗanfodiyo

- Sadauki Shehu Magajin Mamman (Sardauna)

- Malam Amadu Bello

- Rai ya Daɗe Ummaru Ciroma

- Sasa’u na Korau ɗan Abdu

- Tijjani Hashim Ɗan Iya

- Iro Sarkin Malamai

- Wakilin Tasha Sakkwato Garba

- Allah Ya Jiƙan Ciroman Gwambe

- Habu na Habu

- Malam Bawa Magajin Doka

- Abu Kaita Sarkin Malamai

- Sarkin Bori Sule

- Haji Habibu Gado-da-Masu

 

Fadawan Sarki

- Hassan Sarkin Dogarai

 

Waƙoƙin Malamai

- Sannu Malam mai Sasa ɗan Ali

- Malam ɗan Malam Nafi’u

- Malam Babba na Ƙofar Gabas

 

Waƙoƙin Attajirai

- Haji Garban Bichi ɗan Shehu

- Habu Garban Bichi Baban Audu

- Haji Musa Guza na Mamuda

- Ɗanmaraya mai Kayan Mota

- Wo Alhaji Amadu Cancangi

- Tsoho Abdullahi Zariya

- Mammada ɗan Sambo

- Alhaji Mamman ɗan Sambo

- Ɗan Abdulƙadir Garba Ja

- Haji Ummaru ɗan Habu Getso

- Na gode wa Abu ɗan Shehu

- Malam Muɗɗaha ɗan Raka

- Na gode wa Haji Sambajo

- Baba Habibu Fari Alhaji

- Alhaji ɗan Tijjani Wili

- Habu na Binta da ‘Yar Auta

- Gaishe ka Uba Lida na Kano

- Alhaji Baƙo Inusa

- Ado ɗan Dolo Habubakar

- Ina na Alin Bukar Makoɗa

- Sannu na Maiɗankwali Kurata

 

Waƙoƙin Sojoji

- Ku je ku huta farar Hula

- Allah ya Jiƙan Murtala Muhamman

- Allah ya Jiƙan Janar Murtala

- Janar na Mairo giwa

- Allah ya Jiƙan UK Bello

 

Waƙoƙin Shugabannin Gwamnati

- Allah ya Jiƙan Jammal Abdulnasir

- Allah ya Jiƙan Abubakar Tafawa Ɓalewa

- Haji Iro Babangida

- Bibi Faruku na Allah

- Ya Allah ya Jiƙan Akintola

 

Waƙoƙin Ma’aikatan Gwamnati

- Alhaji Sani Zangon Daura

- Mai Daga Magajin Mamman

- Ɗan Alhaji ya Abba Siri-Siri

- Kwamishina Sabo Jama’are

- Ɗansanda D. P. O Audu

- Na gode wa Amadun Gaya

- Allah Jiƙan Ɗahiru Modibbo

 

Waƙoƙin Masu Siyasa

- Aminu Kano Malam na Gwammaja

- Sanata Isa Kacako

- Ɓaɓura ɗan Mamman Najuju

- Mainasara Ribaɗon Yola

 

Waƙoƙin Masu Sana’a

- Ummaru ɗan Ɗanduna na Gwandu

- Idi na Tajo mai Saniya

- Alhaji Mamman na ‘Yangurasa

- Sarki Mijin ‘Ya Sarki Labaran

- Jirgin Sama za ya Tashi Ƙoli ka Tsere na Laraba

 

Waƙoƙin Mata

- A’i Kyaftin

- Na Gode Goshin Ɗangude

- Jikar Mairo Munari

- Don Assibin Ɗanmusa

- Gwamma Malama

- Hajjo A’i ‘Yartsohuwa

- Mamman Kyauta da Niyya ta Kwan

- Hajiya Inno Ɗiyar Amadu

- Allah ba ya ba ka: Malama Barira Abule

- Hauwa Maituwo Matar Lado

- Hauwa Maituwa Innar Dije

- Yarinya Lami Shagamu

- Hajiya Indon Musawa

 

Waƙoƙin Sauran Jama’a

- Na Gode Yakumin Shendam

- Alhaji Tijjani Ƙiru

- A Gaishe ka Hassan Hadi na Kano

- Allah ya Jiƙan Habibu Fari

- Allah ya Jiƙan Habu ABCD

- Alhaji Garba (Ke Bushiya)

- Sadauki Shehu Magajin Mamman

 

Waƙoƙin Faɗakar da Al’umma

- Na ga Jahilci Wurin Karuwai

- Ku wa Allah Mata ku yi Aure

- Don Sallah da Salatil-Fati

- Mu tashi mu Farka ‘yan Arewa

- Ku ‘Yan yara Gumi na Nake ci

- Noma Aikin ‘Yan arewa

- Da Akwai Daɗi Zaman Ƙauye

- ‘Yan arewa mu bar Bacci

- Mu Gargaɗi mai Gina Ramin Mugunta

- Kuɗi a Kashe su ta Hanya mai Kyau

 

Waƙoƙin Abubuwan Rayuwa

- Kumbo Afolo Ilabin

- Muna C. T. Ɓ Kano

- Allah Raya Jihar Katsina

- Nijeriya an yi Jaha-Jaha

 

Waƙoƙin Dabbobi da Garuruwa

- Dawa da Giwa Ikon Allah

- Alo-Alo mai Ganga ya Gode (Jega)

- Kowaj je Yamai yai Kallo

 

Waƙoƙin Tafiye-Tafiye

- Shata Baƙon Amirika

- Kowa zai Shiga Dajin Rugu

 

Waƙoƙin Koɗa kan Shata

- Alo-alo mai Ganga ya Gode (a)

- Alo-alo mai Ganga ya Gode (b)

- Alo-alo mai Ganga ya Gode (c)

- Haka nan ne Mamman Ƙanen Idi wan Yalwa

 

Waƙoƙin Shata na Asauwara

- Ahayye Alewa

- Ai Niyya Samari

A Diwani Juzu’i na Uku an kawo waƙoƙin Shata 143 cikin shafuka 493

 

Diwanin Waƙoƙin Baka: Juzu’i na Huɗu

Diwanin Waƙoƙin Baka na Hausa: Juzu’i na Huɗu ya taskace tare da adana wasu waƙoƙin Alhaji Musa Ɗanƙwairo Maradun Sarkin Kiɗan Sarkin Maradun ta Jihar Zamfara. Shi ma wannan Diwani kamar waɗanda suka gabace an kasa shi zuwa rukunoni biyu.

A rukuni na farko an kawo cikakken bayani a kan tarihi da rayuwar Alhaji Musa Ɗanƙwairo tun daga haihuwarsa a shekara ta 1909 da mahaifansa da ƙuriciyarsa da ire-iren gudummuwar da ya ba da wajen kiɗa da waƙa ta baka. An kuma kawo bayani kan ƙungiyarsa ta waƙa da matansa da ‘ya’yansa. Daga ƙarshe aka kawo bayani kan rasuwarsa a shekara ta 1991.

A kashi na biyu an kawo matanonin wasu waƙoƙinsa da waɗanda ya rera wa rukunonin al’amma da wasu abubuwa waɗanda suka shafi rayuwar al’umma ta yau da kullum. A taƙaice a wannan kashi an kawo waƙoƙi waɗanda suka haɗa da:

Waƙoƙin Noma

Waƙoƙin Iyayen Ƙasa da Hakimai

Waƙoƙin Masu Riƙe da Muƙaman Sarauta

Waƙoƙin Sarakuna

Waƙoƙin Shugabannin Gwamnati

Waƙoƙin Malamai

Waƙoƙin Attajirai

Waƙoƙin Jam’iyyun Siyasa

Waƙoƙin Faɗakar da Al’umma

Waƙoƙin Masu Sana’a

Waƙoƙin Wasa Wasu Makaɗa

 

Diwanin Waƙoƙin Baka na Hausa Juzu’i na Huɗu yana ɗauke da waƙoƙi guda 100 waɗanda aka taskace su tare da adana su a rubuce cikin shafuka 461.

Diwanin Waƙoƙin Baka : Juzu’i na Biyar

Diwanin Waƙoƙin Baka Juzu’i na Biyar ya taskace tare da adana matanonin wasu zaɓaɓɓun waƙoƙin makaɗan baka. Shi ma wannan Diwani an kasa shi zuwa manyan rukunoni biyu.

A rukuni na farko an taskace tare da adana matanonin wasu waƙoƙin fada da wasu waƙoƙi gama-gari daga mawaƙa daban-daban waɗanda mafi yawansu an kawo wasu waƙoƙinsu a Diwani na Ɗaya zuwa Diwani na Huɗu. Daga cikinsu akwai:

Abdu Inka Bakura

Muhammadu Dodo Maitabshi

Sani Mamman Inyaga Argungu

Aliyu Gurso Talatar Mafara

Sa’idu Maidaji Sabon Birni

Sa’idu Faru

Idi Ɗangiwa Zuru

Ibrahim Gurso Talatar Mafara

Alhaji Bala Sarkin Kotson Sarkin Kano

Ibrahim Narambaɗa

Alhaji Dr. Mamman Shata Katsina

Alhaji Isa Gawo-Haraɗo (Mamman Gawo)

Auwalu Nahabu Ibrahim

Makaɗiya: Hajiya ‘Yargado Mai’amada

Hajiya Sa’adatu Barmani Coge

Bawa Namiji Jega

Haruna Uji Haɗeja

Sani Ɗan’indo Gusau

Alhaji Ɗanjuma Ɗanƙwairo Maradun

Malam Ashana Ɗankama Kano

Nura S. Fada

Amadu Mailauni Bakura

Iliyasu Ɗan’umma Unguwar Lalle Makaɗin Noma

Aliyu Gadanga Gusau

Audu Yaro Maƙarfi

 

A rukuni na biyu kuma an taskace tare da adana matanonin wasu waƙoƙin da mawaƙan baka na Hausa na gargajiya da na zamani suka rera wa Farfesa Sa’idu Muhammad Gusau. Daga cikinsu akwai:

Kirarin Farfesa Gusau daga bakin Sanƙiran Aliyu Gadanga (Ibrahim Imo)

Aliyu Gadanga Gusau

Babangida Kakadawa

Aminu Ladan Abubakar Alan Waƙa

Sani Ɗan’iya Ayagi

Sarfilu Umar Zarewa Ɗanbaiwa

Ibrahim Bello Billy’O

Maryam Fantimoti

Muftahu Umar Muhammad

Shehu Ajilo Ɗanguzuri

Abdul Jos na Sarkin Waƙa Naziru

Abba Abdulƙadir Shu’aibu (Abban Baba)

Alhaji Imamu Muhammad Sanusi Ɗanƙwairon Sarkin Katsina

 

Shi ma wannan Diwani an taskare tare da adana wasu zaɓaɓɓun waƙoƙin baka na Hausa guda 179 a rubuce cikin shafuka 378.

Diwanin Waƙoƙin Baka: Juzu’i na Shida

 

Diwanin Waƙoƙin Baka na Hausa Juzu’i na Shida, Farfesa Sa’idu Muhammad Gusau ne tare da Aminu Ladan Abubakar Alan Waƙa suka wallafa shi. Wannan Diwani ya taskace tare da adana matanonin wasu waƙoƙi da Aminu Ladan Abubakar ya rera wa wasu shaihunan malamai waɗanda suka haɗa manyan Farfesoshi da wasu Farfesoshin da Doktoci a fannonin ilimi daban-daban, amma masana da manazarta Hausa sun fi yawa.

Wannan Diwanin ba kamar waɗanda suka gabaci ba, domin kuwa shi an kasa shi zuwa rukunoni huɗu. Rukuni na farko ya taskace tare da adana cikakken tarihin Aminu Ladan Abubukar da ire-iren gwagwarmayar rayuwa da ya yi har ta kai shi matsayin da yake a yau.

Rukuni na biyu kuma ya taskace tare da adana matanonin wasu waƙoƙin da Aminu Ladan Abubakar ALAN WAƘA ya rera wa wasu shaihunan Malamai waɗanda suka haɗa:

Emiratus Farfesa Ambassador Ɗandatti Abdulƙadir

Emiratus Farfesa Abdulƙadir Ɗangambo

Farfesa Ahmadu Bello Zariya

Farfesa Sa’idu Muhammad Gusau

Farfesa Abdallah Uba Adamu

Farfesa Salisu Ahmad Yakasai

Farfesa Aliyu Muhammad Bunza

Farfesa Magaji Tsoho Yakawada

Farfesa Ibrahim Muhammad Abdullahi Malumfashi

Farfesa Yusuf Muhammad Adamu

Farfesa Jibril Aminu

Farfesa Umar Fate

Farfesa Ango Abdullahi

Farfesa Isa Mukhtar

Farfesa Gaji Fatima Ɗantata

Dr. Hauwa Bugaje

 

Babi na uku na wannan Diwani ya taskace tare da adana bitar littafin da aka rubuta kan Aminu Ladan Abubakar ta hanyar:

Sake Waiwayen Tarihin Rayuwar Alan Waƙa a Taƙaice

Wasu Matakan Zubin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar

Wasu Darusan Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar, Baharun Waƙa

 

Shi kuma babi na huɗu ya taskace tare da adana bayani kan Makaɗan Hausa Jiya da Yau, inda aka duba:

Wane ne Makaɗin Baka na Hausa

Ire-Iren Rerawar Makaɗan Baka na Hausa

Matsayin Kiɗa da Waƙa a Rayuwar Hausawa.

 

A jimlace an taskace tare da adana waƙoƙin Shaihunan Malamai guda goma sha shida a wannan Diwani, kuma wani abin ban sha’awa shi ne, an ƙawata wannan Diwani da hotunan Alan Waƙa da wasu iyalansa da kuma wasu waɗanda ya rera wa waƙa.

 

 

Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

Kamar Diwanin da ya gabaci wannan an taskace tare da adana wasu waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar a rubuce, amma a wannan karon wani Shaihun Malami ne tare da ɗalibinsa suka yi wannan aiki. Abin nufi a nan, wannan Diwani, Farfesa Salisu Ahmad Yakasai na Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo Sakkwato, ne tare da Abu Ubaida Sani na Sashen Koyar da Ilimin Harsuna na Jami’ar Gwamnatin Tarayya ta Gusau, suka taskace tare da adana matanonin wasu waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar ALA. Diwanin yana ƙunshe da babuka goma sha uku, kamar haka:

Babi na Ɗaya: Aminu Ladan Abubakar

A wannan babi bayan gabatarwa an kawo cikakken bayani kan tarhin rayuwar Ala tun daga haihuwarsa da dalilin sanya masa sunan ALA da mahaifansa da kakanninsa da aure da iyalansa da iliminsa da gwagwarmayar rayuwa da ra’ayinsa game da rayuwar yau da kullum. Daga nan aka kammala babin.

Babi na Biyu: ALA a Duniyar Waƙa

Shi kuma wannan babi bayan gabatarwa an kawo bayani kan lokaci da dalilin fara waƙar Ala da waƙar da ya fara ta farko da bayani kan ko Ala yana da ubangida da gwagwarmayarsa a duniyar waƙa da irin ɗaukakar da Allah Ya yi masa da yadda yake shirya waƙa da kyaututtukan da ya samu da muradin Ala da koken Ala da lokutan ƙunci a rayuwar Ala da fargabar Ala da wasiyar Ala da ire-iren rubuce-rubucen ilimi da aka yi kan Ala. Sannan sai aka kammala babin.

Babi na Uku: Waƙoƙin ALA Masu Jigon Ilimantarwa/Wa’azi/Faɗakarwa

An fara da gabatarwa daga nan aka kawo jerin waƙoƙi irin su: Bara a Kufai da Jami’a Gidan Bankashi da Yana Giza-Gizo da Baba Ina Za Ka da ni da Waƙar Ilimi da Maɗaci da Marainiya da Sakarkari da Rayuwa a Duniya tana Ban Tsoro da Murnar Salla ta Gari da Waiyo Kaico da Mutuwa da Almuhajura da Ɗanjarida da Aure Ibada da Jami’a Gidan Wuya da Ɗan Barno da Hangen Dala da Uba da Noma da Kushewa da Rama Cuta Ba Laifi Ne Ba da Gobe Alƙiyama da Kukuma da Sababin Mutuwa da Adali da Cutar Taɓin Hankali da Ɗamarar ko ta Kwana da Jami’a Gidan Ban Kashi ta Biyu da mu Zauna Lafiya. Daga ƙarshe aka kammala babin.

Babi na Huɗu: Waƙoƙin ALA na Siyasa

Gabatarwa ce ta buɗe wannan babi, sai kuma aka taskace tare da adana wasu waƙoƙin ALA masu dangantaka da siyasa, kamar: Allah kaɗa guguwar Sauyi da Kira ga Gwamnoni da Dashen Mai Shuka Kainuwa Hawa Mulkin Yaro da Zaɓe da Tallafi da Baubawan Burmi da Kamaye da Makomar Arewa da Allah Ya Maimaita da Buɗaɗɗiyar Wasiƙa da Waiwaye da Walle-Walle da Raba Gardama da Your Eɗcellency da Malam Ibrahim Shekarau Allah Maimaita da Sardaunan Mubi Mai Girma da Garkuwa Na Matasa Doktoro Yahaya Adoza da Ɗan Bello Yahaya Gwamna Mai Jihar Kogi da Gwamnan Jama’a Bindo da Gwamna Bindo Gwamnan Adamawa da Farar Aniya Alamin Nasara da Mu Kaɗe Kumfar Ruwan Kogi da Bubuƙuwa da Bargon Rufa da Ɗaurin Gwamai. Sai Kammalawa.

Babi na Biyar: Waƙoƙin ALA masu Jigon Soyayya

Da gabatarwa aka buɗe wannan babi daga nan sai aka jero waƙoƙin ALA masu jigon soyayya waɗanda suka haɗa da: Angara da Fuju’a da So Ƙawalwalniya da Kibiya da Kalmar So da Amina da Tsohuwa ta Illela. Sannan sai aka kammala babin.

Babi na Shida: Waƙoƙin ALA na Sarauta

An fara da gabatarwa sai kuma aka taskace tare da adana waƙoƙin ALA masu jigon sarauta waɗanda suka haɗa da: Sarkin Zazzau Shehu Idrisu da ta Ado Mai Kano Mai Martaba da ta Jaɓɓama Marafa Abubakar, sai ta garin Zazzau da ta Tamburan ’Yan Maza: Nuhu Mamman Sunusi, sai ta Sarkin Bauchi Ka Gama Lafiya da ta Santuraki Ali Ado Bayeronmu da ta Na Laraba Gogarma da Waƙar Sadaukin Lafiya Maigirma da ta Abubakar Na Laraba da ta Nasiru Ɗan Dano da ta Bebejin Zazzau Haji Ahmad da ta Usman Kogunan Gamawa da ta Attahiru Abdurrazak Bunun Borgu da ta Borgu Kingdom da ta Ciroma Nasiru Ado Bayero da Gimbiya Mero Tanko Almakura da ta Uban Musulmi Sultan Sa’adu Abubakar da waƙar Bakan Dabo da waƙar Takawa da waƙar Sarakunan Fulani da waƙar Mai Tagwayen Masu. Daga nan sai aka kammala wannan babi.

Babi na Bakwai : Waƙoƙin ALA na Yabo/Jinjina

Gabatarwa ce ta buɗe wannan babi. An biyo da jerin waƙoƙin ALA na yabo da jinjina. An fara da kawo waƙar Farfesa Yakasai, sai Taken Maza Burutai, sai ta Kwamishinan ‘Yan Sanda Faruk Usman Ambursa, sai waƙar Ruhanai da ta Galadima Udubo da waƙar Farfesa Sa’idu Muhammad Na Gusau da ta Amainar Mama da ta Yahuza ɗan Sadisu Madobi da ta Nana Faɗima da ta Janaral Murtala Mazan Jiya da ta ‘Yan Mazan Faman Nijeriya da ta Janar Mustafa ta Ɗaya da Manjo Almustafa ta biyu da ta Ɗiya Maza Ɗaukar Farko Baba da ta Mai Nasara Burutai da Ƙara Haƙuri Burutai da waƙar ;Yan maza Gidan Soja da ta Mashal Sadiƙu da kuma Mashal Siddiƙu Dogarin Ƙasata da Waƙar Ginshiƙin Adabi da ta Hamshaƙin Sadauki da ta Hashim Ubale da ta Farfesa Ango Abdullahi da waƙar Hindu Ta Bunun Bargu da ta Karibu Ɗantata da waƙar Muhammadu Muftahul Futuhati da waƙar Rabbu Yarje da waƙar Ganganko da ta Sharu Sulaimanu Jadda da ta Nuhu Uba Kura da ta Malam Amadu Mai Rauhanai da waƙar Uwar Iyaye A’isha. Daga nan sai aka kammala wannan babi.

Babi na Takwas: Waƙoƙin ALA na Ganin Dama

A wannan babi an fara da gabatarwa, sannan aka kawo jerin waƙoƙin da Ala ya yi na ganin dama waɗanda suka haɗa da; Momi Ummina da Al’adun Hausa da Ala: Basasa da Zariya Gidan Ilimi da Kano Tumbin Giwa da Duniya Tana Ruɗa Ni da Dutse Gadawur da Mahaukaciya da Zuciya da Kyauta da Astagfirullah da Lafiya da Sakkwaton Usmanu da Alan Waƙa Zai Koma Gida da Nasarun Minallahi Sojojin Nijeriya da Madina Gidan Ma’aiki da Addu’a Ga Masoyana da Gidan Soja Ginshiƙin Yaƙi da Hajji Garin Manzon Allah da Zuciya ta Auri Tunanina da Bazazzagiya da Baubawa da Mashigin Kano da Jakadiya da Makauniya da Du’a’i da Bayi da Astagfurullah. Daga nan sai aka kammala babin.

Babi na Tara: Waƙoƙin Ala na Talla

Aminu Allah ya yi waƙoƙin tallata wasu abubuwa don al’umma su fahimci muhimmanci su. A wannan babi an taskace tare da adana wasu waƙoƙi da Ala ya yi wa wasu abubuwa don tallata su a idon duniya. Shi ma wannan babi an buɗe shi da gabatarwa. An jero ire-iren waƙoƙin da Ala ya yi na tallata wasu abubuwa waɗanda suka haɗa da: Waƙar tallata Amana Rediyo da AM FM da CTB da Liberty ‘Yanci Kaduna da BBC Hausa da Inuwar Marubata Jihar Arewa Da Hausa da Inuwar Marubuta. An kammala babin.

Babi na Goma: Waƙoƙin Ala Masu Jigon Aure

An fara da gabatarwa daga nan aka jero ire-iren waƙoƙin da Aminu Ala ya rera masu ɗauke da jigon aure waɗanda suka haɗa da: Tambarin Masoya da Ayyuriri Amarya Ango da Alhaji Surajo Abubakar Ango Na Farida da Auren Usman Lawan da Zainabu Abdullahi da Muhammadu Tukur Ango Na Fatima da Bikin Fadeela da Alalo-Alalo Masoya da Tambarin Amarsu Da Ango da Auren Maryama da Aminu da Auren Dr. Dakta Abdullahi da Bara’atu da Maryama Gimbiyar Mata da Murnar Aure. Daga nan sai aka kammala babin.

Babi na Goma Sha Ɗaya : Waƙoƙin Ala Masu Zagin Kasuwa

An fara da gabatarwa. An ci gaba da kawo waƙoƙin Ala masu zagin kasuwa waɗanda suka haɗa da: Raƙumi da Gilashi da Hasbunallahu wa Ni’imal Wakilu. Daga nan sai aka kammala babin.

 

Babi na Goma Sha Biyu: Waƙoƙin Ala na Ta’aziyya

Kamar sauran babukan da suka gabace shi an fara da gabatarwa. An kuma Cigaba da kawo waƙoƙin da Ala ya yi na ta’aziyya waɗanda suka haɗa da: Mutuwa Rigar Kowa da Ta’aziyyar Maitama da ‘Ya’yan Sarki Ado Bayero da Ta’aziyyar Mai Martaba Alhaji Ado Bayero. Daga nan sai aka kammala wannan babi.

Babi na Goma Sha Uku: Waƙoƙin Ala na Ɗaukaka

An fara da gabatarwa daga nan aka kawo jerin waƙoƙin ɗaukaka da Allah Ya yi wa Aminu Ladan Abubakar waɗanda suka haɗa da: Ɗaukaka Abar Gudu Abar Nema da Hikima Taguwa da Lu’u-Lu’u da Sharara wadda ta ƙunshi fannonin rayuwa daban-daban ta fuskar Rukunin Tarihi da Rukunin Gwagwarmaya da Rukunin Shahara Tsantsa da Rukunin Ƙalubale da Rukunin Nasara. Wannan babi shi ne na ƙarshe a wannan Diwani.

A jimlace a wannan Diwani an taskace tare da adana waƙoƙi guda ɗari da saba’in da tara (179) a cikin shafuka ɗari biyar da sittin da shida (566).

Ƙalubale Gare ku Ɗalibai da Manazarta Waƙoƙin Hausa

Haƙiƙa, waɗannan ayyuka da suka yi sun jefa wa ɗalibai da manazarta adabin Hausa babban ƙalubale. Idan muka dubi Diwanin Farfesa Sa’idu Muhammad Gusau tun daga na Ɗaya zuwa na shida za a fahimci ya ci ƙarfi taskace da adana waƙoƙin baka na Hausa musamman na gargajiya da na zamani. Haka shi ma Diwanin Farfesa Salisu Ahmed Yakasai da Abu Ubaida Sani sun taskace mafi yawa daga cikin waƙoƙin da Aminu Ladan Abubakar ya rera. Duk da haka, akwai sauran aiki da ya kamata a ƙara a kai. Misali, idan muka dubi waƙoƙin da aka kawo a ɓangaren waƙoƙin baka na Hausa na gargajiya akwai wasu Mawaƙan waɗanda ba a taskace aka adana ayyukansu ba. Daga cikinsu akwai waƙoƙin:

 Ƙwazo Bagega Sarkin Kotson Sarkin Zamfaran Anka

Ɗanƙwairon Gwambe

Amadu Monkey Katsina

Darda’u Sarkin Kotson Katsina

Kotsoma Sarkin Kotson Ɗan Yusufa Bindawa

Alhaji Nabanjo Sarkin Kotson Makaman Katsina Hakimin Bakori

Ɗangiwa ‘Yarlilo Makaɗan Yariman Katsina

Ɗahiru Kakkaɓi

Makarai Ɗan Yakubu

Mamman Nabuta Ɓaɓura

Ɗangwalolo

Sale Gambara

Naburdugau Mai Yar Ganga

Mu’azu Ɗan’alalo Damagaram

Iro Maikomo Kurfi

Idi Ɗangalma Musa

Haruna Sarkin Kotso Musawa

Makaɗa da mawaƙan sana’o’in gargajiya na Hausawa

Makaɗa da mawaƙan maza

Waƙoƙin samartaka na samari da ‘yanmata na gargajiya

Waƙoƙin daka da niƙa da daɓe

Waƙoƙin bara na almajirai da makafi

Waƙoƙin tashe

Waƙoƙin roƙon ruwa

Waƙoƙin kadaba lokacin da matar bamaguje za ta fita takaba

da sauransu.

A ɓangaren rubutaccin waƙoƙin Hausa akwai sha’irai masu yawa waɗanda suke da rubutaccin waƙoƙi masu yawa waɗanda ba a taskace su a rubuce ba, suna nan ajiye a rubutun biro ko bugun tafireta ko bugun kwamfyuta. Daga cikin su akwai:

Barmo Birkila Katsina

Baba Maigyaɗa Agage

Shehu Maigidaje Funtuwa

Malam Lawal Ɗan Halilu Katsina

Malumman Matazu

Bello Shehu Alkanci

Abdullahi Adamu Dukki Kangiwa

Aliyu Umar Kafin-Hausa

   da sauransu.

 

Haka kuma, ta fuskar mawaƙa masu amfani da kayan kiɗa na zamani akwai su da dama waɗanda suka haɗa da:

Dauda Kahutu Rarara

Baban Chinedu

Sanusi Anu Sabuwar Unguwa

Justice Abubakar Jemo

Malam Yahaya Makaho

Adam A Zango

Sani Danja, da sauransu.

Shawarwari

Dukkan kyawon al’amari ko muninsa matuƙar ana bin shawara al’amarin zai ƙara kyau wanda kuma yake da muni zai yi gyaru ya yi inganci. Danagane da taskace da adana waƙoƙin Hausa a rubuce yana d a matuƙar muhimmanci a wannan zama a ƙara haɗa hannu da ƙarfe wajen ƙara inganta hanyoyin da za su ƙara taimakawa a ƙara taskace da adana waƙoƙin Hausa a rubuce musamman waɗanda har yanzu wannan ƙoƙari bai kai kansu ba.

Shawara ta farko ita ce, yana da matuƙar muhimmanci ga gwamnatoci su cigaba da tallafawa wa masu nazari da taskace da adana waƙoƙin Hausa don gudanar da nazarin waƙoƙi da wallafa su domin amfanin gobe.

Ya dace hukumomin bincike da adana tarihi da adabi na jihohi da suke arewa- maso-yamma, wato ƙasar Hausa su tabbatar da sauke nauyin da aka ɗora masu na bincike da adana da taskace ayyukan tarihi da fasaha da al’adu da adabin al’ummomin jihohinsu a wallafa su domin amfanin gobe.

Haka kuma, jami’o’i waɗanda suke koyar da darasin Hausa su ƙara wa ɗalibansu himma wajen taskace waƙoƙin Hausa a matsayin jinga ko kundin digiri na farko. Idan aka tattara sau da yawa sai hukumar gudanarwa ta jami’a ko wani mai sha’awar taskace waƙoƙin Hausa ko wata hukuma wadda ba ta gwamnati ba su ɗauki nauyin wallafa su don amfani gobe.

Ya dace attajirai da duk wani mai hali su taimaka wajen adana da taskace waƙoƙin Hausa ta hanyar ɗauki nauyin wallafa su.

Wannan shawara zan miƙa ta ga waɗannan malamai namu da suka fara aikin wallafa Diwanin Waƙoƙin Hausa, musamman Malam Adamu Mainasara da kar ya gajiya, ya tashi tsaye yadda wannan Diwani da ya fara ya zama Juzu’i na Ɗaya. Abin nufi ya dace ya fara shirin taskace Diwani na Biyu da na Uku da na Huɗu da dai sauransu. Dalili kuwa shi ne, na saurari waƙoƙin Abubakar Kantama masu yawan gaske, na tabbata a yanzu ana iya wallafa Diwani goma na waƙoƙinsa.

Kammalawa

Yabon gwani ya zama dole, kuma matuƙar ana son yin suna dole a hana ido barci, don kuwa sai dare ya yi ake sayar da fatar kura a sayi ta bunsuru. Bisa ɗan abin da aka kawo dangane da taskace da adana waƙoƙin Hausa tun daga shekara ta 1953 zuwa yau, za a amince da ni cewa, gwamnatoci da hukumomi na gwamnati da ma waɗanda ba na gwamnati ba da makarantu da kwalejoji da jami’o’i da ƙungiyoyi na cikin gida Nijeriya da na ƙasashen da ɗaiɗaikun masana da manazarta da ɗalibai sun bayar da gagarumar gudummuwa wajen taskace da adana waƙoƙin Hausa a rubuce cikin littattafai ko kundaye ko mujallu ko ƙasidu ko jaridu ko kuma a wallafa irin ta Diwani. A nan ya zama dole a gode masu saboda gudummuwar da suka ba da wajen taskace da adana waɗannan waƙoƙi waɗanda kafin ɗaukar wannan mataki wasu waƙoƙin hanyar taskace su da adana su ita ce ta rubuta su da hannu yadda ba za su yawaita ba, hasali ma suna iya salwanta ta hanyoyi daban-daban. Wasu kuma ana ƙoƙarin hardace su. Shigowar Turawa ta sa an sami wata dabara ta naɗar sautin muryoyin mawaƙan a saka su a faifan garmaho ko kaset ko CD ko memory da sauransu. Gudummuwar Malamanmu irin su Farfesa Abdulƙadir Ɗangambo da Farfesa Sa’idu Muhammad Gusau da Farfesa Abdullahi Bayero Yahya da Farfesa M. A. Z. da Sani da Farfesa Aliyu Muhammad Bunza da Farfesa Salisu Ahmad Yakasai da Farfesa Ahmad Magaji da Abu Ubaida Sani da Adamu Mainasara sun taimaka matuƙa ainun wajen taskace da adana waƙoƙin Hausa masu ɗimbin yawa a wallafe a wannan Ƙarni na 21. Ya zama dole a ƙara jinjina masu da sa masu albarka da roƙon Allah Ya sa su gama da duniya lafiya, sannan kuma Ya yi masu sakayya da Aljanna Firdausi.

 

 

Manazarta

Bosso, M. A. (2010) Nazarin Ajami Cikin Hausa, Don Makarantu Manya da Ƙanana, Minna: @Hasbunallah Printers.

Bunza, A. M. (2004) Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa, Lagos: Ibrash Islamic Publication Centre LTD.

Bunza, A. M. (2009) Naramnaɗa, Lagos: Ibrash Islamic Publication Centre LTD.

Ɗangambo, A. (2008) Gadon Feɗe Waƙa, Zaria: Amana Publishers Limited New Kano Road, Kaduna State.

Ɗangambo, A. (2008) Rabe-Raben Adabin Hausa (Sabon Tsari). Zaria: Amana Publishers Limited New Kano Road, Kaduna State.

Gusau, S. M. (2002), Salihu Jankiɗi Sarkin Taushi, Kaduna: Baraka Press.  

Gusau, S. M. (2003), Jagoran Nazarin Waƙar Baka, Kano: Benchmark Publishers Limited.

Gusau, S. M. (2008), Waƙoƙin Baka A Ƙasar Hausa: Yanaye-Yanayensu da Sigoginsu, Kano-Nigeria: Benchmark Publishers Limited.

Gusau, S. M. (2009) Diwanin Waƙoƙin Baka, Zaɓaɓɓun Matanoni na Waƙoƙin Baka na Hausa, Kano: Century Research and Publication.

Gusau, S. M. (2014) Diwanin Waƙoƙin Baka, Juzu’i na Biyu, Kano: Century Research and Publication.

Gusau, S. M. (2018) Diwanin Waƙoƙin Baka: Juzu’i na Uku, Matanonin Wasu Waƙoƙin Wasu Waƙoƙin Alh. Dr. Mamman Shata Katsina, D. Litt; MON, Sanyinnan Musawa, Kano: Century Research and Publication.

Gusau, S. M. (2019) Diwanin Waƙoƙin Baka, Juzu’i na Huɗu, Wasu Waƙoƙin Alhaji Musa Ɗanƙwairo Maradun (1099-1991) Sarkin Kiɗan Sarkin Maradun Jihar Zamfara, Kano: Century Research and Publication.

Gusau, S. M. (2020) Diwanin Waƙoƙin Baka, Juzu’i na Biyar, Matanonin Wasu Zaɓaɓɓun Waƙoƙin Makaɗan Baka, Kano: WT Press, Commercial Printing &Publishing, No. 266, Sudawa, waizaonline@gmail. com

Gusau, S. M. da Abubakar, A. L. (2022) Diwanin Waƙoƙin Baka, Juzu’i na Shida, Matanonin Waƙoƙin Wasu Shaihunan Malamai: Emiratus da Farfesoshi da Doktaci na Aminu Ladan Abubakar, ALAN WAƘA, Kano: WT Press, Commercial Printing &Publishing, No. 266, Sudawa, waizaonline@gmail. com

Hukumar Binciken Tarihi da Kyautata Al’adu (2003) Waƙoƙin Alhaji Mamman Shata: Diwani na Ɗaya: Katsina: Government Printer.

Ibrahim, M. S. (1982), “Dangantakar Al’ada da Addini: Tasirin Musulunci kan Rayuwar Hausawa”. Kundin Digiri na Biyu. Kano: Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero.

Ƙamusun Hausa na Jami’ar Bayero (2006) Wallafar Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya, Kano: Jami’ar Bayero.

Magaji, A. (2016) Kassu Zurmi da Waƙoƙinsa, Ibadan: Spectrum Books Limited.

Sani M. A. Z. (2002) Alfiyyar Mu’azu Sani 1-5, Kano: Benchmark Publishers Limited/Gidan Dabino Publishers.

Yakasai, S. A da Sani, A. U (2021) Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar ALA, Kano: Amal Printing Press.

Yahaya, I. Y. (1988), Hausa a Rubuce: Tarihin Rubuce-Rubuce Cikin Hausa, Zariya: NNPC.

Yahya, A. B. (2016) Salo Asirin Waƙa, Sokoto: Guaranty Printers, Tudun Wada Area, Adjecent Tudun Wada Guest Inn.

www.amsoshi.com

Post a Comment

0 Comments