Ticker

6/recent/ticker-posts

Haba Ke Kuwa.....😭😥🤦"

Nashiga juyin juyayi
Da rashin lafiya da laulayi
Na rasa yadda zanyi
Kuka duka nayi
Tace dani ta chanza ra'ayi
Maza maza insan nayi
Na kama wani layi

Gaba daya ta sani Layi
Tace yanxu Umar take yayi
Na rasa laifin me nayi
Abunda ya kamata fa nayi
Lefe da komai duka nayi
Da seya mata salula yar yayi
Hatta ankon biki duka ni keyi😥

A watan Yuni a farkon sa
Yarinyan nan tamin ƙusa
Akan Umar ɗan musa
Ya dauke ta suka nausa
Chan Kaduna-rigasa
Sunka barni da juyin masa.

Haba ke kuwa Hafsa
Akanki fa na ƙosa
Sonki a rai yaimin fusa
Yanzu rayuwata kin rusa
Akan Umar ɗan musa
Duk don yamiki busa
Har aurena kika fasa
Nima wataran zan bunƙasa
Amma bani yiwa kowa ƙusa
Dan kuwa nasan zafinsa.

Nifa yanxu na fusata💪
Kuban hakuri kona tafi gunta😂
Ta biyan kudina da wayata
Tunda ta daina kaunata
Tayi waje road dani a ranta
Duk akan ɗan mai mota
Nima wataran zan mallake ta
Motar nan nashiga gaban ta
Idan Allah yaso in seye ta..

Shin mata sunada alkibla?
Duk da wasu nada kamala
Da nitsuwa da nau'in hankula
A lamarin mata fa ana kula
Don ko wasu bassu hamdala
Idon su yana kan mai dola
Mara silalla shine bola

A lamarin mata na gabata
Nayi laushi na hankal ta
Tun a lokacin da akai bikin ta
Na ɗau darasi a daga halayen ta
Da dai nace babu kamar ta
Allah ka ɗebemin kewar ta
Na zaƙulo wanda ta fita
Diri, fara kalan gaban mota.

Lalle nayiwa so shukan dusa
Balle yai tsiro har yai fusa
Waza ta ban zuma in lasa?
Da ruwan kauna don NA ƙosa
Gani a kwance har ƙasa
Ban motsi ina bukatar tausa😎

(C)AUWAL ISMAIL KUMO

Post a Comment

0 Comments