Ticker

6/recent/ticker-posts

Ayar Tambaya (?)

Citation: Maikwari, H.U. & Sani, A. (2020). Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa. Zaria: Ahmadu Bello University Press Ltd.

About Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa

432. Kowace tambaya da aya aka yin ta,

 Don a sanar da wanda duk za ya karanta,

 Ya zama wajibi da aya ka rubuta,

 Can ƙarshenta zan kula nan aka sa ta,

  Sai an sa ta tambaya za ta fitowa.

433. In ka yi tambaya gabanin amsawa,

 In niyyarka tambaya ga rubutawa,

 Jimla za ta zo a tsarin Hausawa,

 Can ƙarshenta za ta zo da alamtawa,

  Ayar tambaya a nan za ta fitowa.

 

434. In ka saka ta tambaya ta cika ke nan,

 Ka gamsar da wanda za ya karatun nan,

 In ya lura za ya gan ta rubutun nan,

 Ba uzuri gare shi kuma ma da sannan,

  Ba sauran abin faɗi sai amsawa.

 

435. Ga misali ka ce: “Ina za ku mutane”?

 Kun yi dako-dako, haba kai ku yi zaune,

 Kuma kun yamutse, ku yo jerin gwane,

 Na yi kira gare ku ƙauye da birane,

  Me ke sa ana kira ba ku fitowa?

 

436. Wa zai rena malami ba sauna ba?

 Sai ko wanda bai yi gadon ɗa’a ba,

 Kai malam yi hattara girmama babba,

 Bi shi ka kyautata, da ɗa’a kuma duba,

Wa ka gudun ubansa bai son tsinewa?

 

437. Wa ke yin ruwan sama bayan Rabbi?

 Malam na da tambaya “Wa yaɗ ɗau carbi?”

 Ko an sa ma wagga kaza ƙwan zabbi?

Gyashi[1] ba a yin sa sai an cika tumbi,

  Wa zai yi shi in ciki bai ɗauka ba?

 

438. Wane ne da wacce koko da waɗanne?

 Kun ƙyale ni ko gidan babu mutane?

 Ko ka ji ana faɗin Aliyu waliyi ne?

 Shin ka samu wanga zance ga mutane?

Wa yac ce? Da waf faɗa? Dinga kulawa.

 

439. Lura gaɓa guda takan ɗau ayar nan,

 Shi ma ya taho cikin dokokin nan,

 Sannan kuma in ka duba kalmar nan,

 Kwai ma’ana gareta ga fa misali nan,

Tamkar wa? Da me? Ga mai son ganewa.

 

440. Matuƙar tambaya ka yo sai ka uzurta,

 Aya za ka sa wurin don ka alamta,

 Sai ka taho ka duba tsari ka saka ta,

 Ba uzurin da zai hana sai ka rubuta,

  Saka aya wurinta don tantancewa.



[1] “Gashi” daidai yake da kalmar “gyatsa.” Fitar iska mai ƙara daga ciki bayan an ƙoshi da abinci.

Post a Comment

0 Comments