Ticker

6/recent/ticker-posts

Shin Zan Iya Auran Ƙanwar Matata

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Malam, shin ko mutum zai iya auren kanwar matarsa bayan ya saketa sai ya auri ƙanwarta, alhali kuma yayar tana da rai?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Abin da Allaah ya hana shi ne: A haɗa yaya da ƙanwa a lokaci guda:

...وَأَنْ تَجْمَعُوا بَيْنَ الْأُخْتَيْنِ إِلَّا مَا قَدْ سَلَفَ ۗ ...

Kuma (an haramta muku) ku haɗa a tsakanin mata ’yan uwa biyu, sai dai abin da ya riga ya gabata. (Surah An-Nisaa’i: 23).

Malamai suka ce: Haɗawa a tsakanin ’yan uwa biyu a wurin aure haram ne: Ko shaƙiƙai ne, ko li-abbai, ko kuma li-ummai ne. Haka kuma ko ta danganen jini ne, ko kuwa ta shayarwa ne suka zama yan uwan. (Fat-hul Baariy).

Sannan kuma ko kafin tarewarsu ne aka gano haka, ko kuma a bayan an yi tarewa ne, saboda gamammen saƙon da ke cikin Ayar! (Al-Mughnee).

Don haka, ba shi halatta mutum ya haɗa mata biyu ’yan uwan juna a wurin aure, sai dai in da farko ya rabu da ɗayar, kafin ya auro ɗayar. Sannan idan rabuwar ta hanyar saki ne, to ba zai iya auro waccan ba har sai wadda ya saka ta ƙare iddarta. Amma in ta hanyar rasuwa ce, to yana iya ɗaura aurenta ko a ranar rasuwar ce, in ji malamai. (Tamaamul Minnah: 3/58).

WALLAHU A'ALAM

Sheikh Muhammad Abdullaahi Assalafiy

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/IerSx3AH0ZSJyHIuIYfqds

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments