Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Saurayin Da Ya Sadu Da Budurwarsa Tana Cikin Haila

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

As-Salaam Alaikum Wa Rahmatul Laah. Don Allaah, menene hukuncin saurayin da ya sadu da budurwarsa alhali tana cikin jinin haila?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah Wa Barakaatuh.

Da farko dai ya saɓa wa dokar Ubangijinmu Ta’aala da ya ce:

وَلَا تَقۡرَبُوا۟ ٱلزِّنَىٰۤۖ إِنَّهُۥ كَانَ فَـٰحِشَةࣰ وَسَاۤءَ سَبِیلࣰا ٢٣۝

Kuma kar ku kusanci zina. Haƙiƙa! Ita alfasha ce, kuma mummunar hanya ce.

(Surah Al-Israa’i: 32)

Shi kuwa wannan ba kusantar ce kaɗai ya yi ba, aikatawa ma ya yi!

Kuma ya saɓa wa dokar Allaah Ta’aala da ya ce:

قُلۡ هُوَ أَذࣰى فَٱعۡتَزِلُوا۟ ٱلنِّسَاۤءَ فِی ٱلۡمَحِیضِ وَلَا تَقۡرَبُوهُنَّ حَتَّىٰ یَطۡهُرۡن

Sai ku nisanci mata a cikin wurin haila, kuma kar ku kusance su har sai sun tsarkaka.

(Surah Al-Baqarah: 222)

Wannan dokar fa asali ga mazajen da aka ɗaura musu aure da matan ne, auren Sunnah a bisa ƙaida da dokokin addinin musulunci. To, ina kuma ga wanda ba a ɗaura masa aure da yarinyar ba, ya lallaɓa ba da amincewa ko yardan iyayenta ko waliyyanta ba, ya keta wannan dokar? Laifinsa ya fi girma nesa ba kusa ba!

Kuma ya saɓa wa Allaah Maɗaukakin Sarki a inda ya ce:

وَٱلَّذِینَ یُؤۡذُونَ ٱلۡمُؤۡمِنِینَ وَٱلۡمُؤۡمِنَـٰتِ بِغَیۡرِ مَا ٱكۡتَسَبُوا۟ فَقَدِ ٱحۡتَمَلُوا۟ بُهۡتَـٰنࣰا وَإِثۡمࣰا مُّبِینࣰا

Kuma waɗanda suke cutar da muminai maza da mata ba da wani haƙƙi ba, to haƙiƙa! Sun ɗauki nauyin wani ƙiren ƙarya da zunubi mabayyani.

(Surah Al-Ahzaab: 58).

A ƙarƙashin wannan ayar, yanzu wannan mutumin ya cutar da yarinyar, da iyayenta da danginta da sauran muminai!

A taƙaice mai aikata wannan ɗanyen aikin lallai ya san cewa manyan haƙƙoƙin ne masu yawa a kansa, kamar haka:

1. Haƙƙin Allaah Ubangijin Halittu wanda ya halicce shi kuma ya hana shi wannan laifin, kuma amma ya bi son-zuciyarsa da shaawar ransa, ya saɓa dokokin ta fuskoki masu yawa.

2. Haƙƙin ransa da jikinsa waɗanda ya cutar da su ta hanyar wannan saɓon, domin a ƙarshe su za su ɗanɗani duk azabar da hakan zai janyo masa tun daga nan duniya har zuwa makoma lahira.

3. Haƙƙin ita kanta budurwar, musamman idan shi ne ya yaudare ta, ya janyo raayinta har ta goya masa baya suka yi wannan taaddancin. Ina kuma idan fyaɗe ya yi mata da ƙarfi?!

4. Haƙƙin iyayen budurwar da sauran danginta da yan uwanta, saboda lalata musu yarinya da ya yi. Da kuma zubar musu da mutuncin gida, da ɓata musu suna da ya yi, musamman idan asirin abin da ya yi ya tonu.

5. Haƙƙin iyayensa da iyalinsa - in yana da su, waɗanda wannan abin zai baƙanta musu rai, ya zubar musu da mutunci a idon jamaa, idan abin ya bayyana daga baya a cikin alumma.

6. Haƙƙin yayansa da jikokinsa waɗanda za a cigaba da ambatonsu ko kallonsu da wannan laifin da Ubansu ko Kakansu ya yi, wanda hakan zai zubar musu da mutunci a cikin al’umma.

7. Haƙƙin sauran maɓarnata da za su biyo baya, waɗanda za su yi koyi da shi a cikin aikata irin wannan aikin har zuwa Ranar Ƙiyama, musamman idan suka samu labarinsa.

Allaah ya ƙara kare mu.

Don haka ne Allaah Ta’aala ya yanke mummunan hukunci mai kaushi mai tsanani a kansa:

A zaunar da shi a gaban jama’ar musulmi masu Imani, bayan gama bincike da samun izini daga Alƙalin Musulunci, a yi masa buloli guda ɗari, ba tare da nuna wani tausayi ba. Allah Ta'aala ya ce:

الزَّانِيَةُ وَالزَّانِي فَاجْلِدُوا كُلَّ وَاحِدٍ مِنْهُمَا مِائَةَ جَلْدَةٍ ۖ وَلَا تَأْخُذْكُمْ بِهِمَا رَأْفَةٌ فِي دِينِ اللَّهِ إِنْ كُنْتُمْ تُؤْمِنُونَ بِاللَّهِ وَالْيَوْمِ الْآخِرِ ۖ وَلْيَشْهَدْ عَذَابَهُمَا طَائِفَةٌ مِنَ الْمُؤْمِنِينَ ٢۝

Mazinãciya da mazinãci, to, ku yi bũlãla ga kõwane ɗaya daga gare su, bũlãla ɗari. Kuma kada tausayi ya kãma ku game da su a cikin addinin Allah idan kun kasance kunã yin ĩmãni da Allah da Rãnar Lãhira. Kuma wani yankin jama'a daga mũminai, su halarci azãbarsu. (Surah An-Nuur: 2)

Wannan idan bai taɓa yin aure ba kenan. Amma in kuwa ya taɓa yin aure, to hukuncinsa shi ne: A haƙa rami zuwa gwiwarsa ko mararsa a saka shi a ciki, sannan a yi ta jifan sa da duwatsu har sai ya mutu.

(Sahih Al-Bukhaariy: 6633, 6634)

Idan kuma ya tsira a nan duniya, ba a yi masa wannan hukuncin ba, to sai ya yi shirin karɓar sa a Lahira, sai dai in ya tuba, tuba ta gaskiya kafin zuwan mutuwarsa.

Don haka, mafita gare shi a nan kafin zuwan mutuwarsa ita ce:

Ya yawaita tuba da istigfari a bisa sharuɗɗa da ƙaidojin da malamai suka shimfiɗa a kan haka. Ya mayar da hankali ga kulawa da ayyukansa na farilla da Allaah ya wajabta masa, sannan kuma ya yawaita ayyukan nafila. Sannan ya yi ƙoƙarin neman gafara da yafiya daga duk mahalukan da ya cutar da su ta wannan aikin. Idan kuma abin ya gagara saboda nisantarsu daga gare shi, kamar idan sun rasu, to sai ya yi ta yi musu adduar alheri, yana roƙa musu gafarar zunubansu.

Ana fatan da haka sai Allaah Ta’aala ya karɓi tubansa, ya yafe masa dukkan laifuffukansa.

Allaah Ta’aala ya yafe mana dukkan kura-kuranmu gaba-ɗaya.

WALLAHU A'ALAM

Muhammad Abdullaah Assalafiy

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments