Ticker

6/recent/ticker-posts

Saurayinta ya ce Ta Dinga Kissing Dinsa

TAMBAYA (02)

Fatan katashi lpy yauwa dama inaso namaka wata tambaya akwai wata kawata tanada saurayi kuma yanasonta itama haka Amma daga baya seyafara bujiromata dawasu abubuwa misali idan yaxo sungama zance seyace setayi kissing nashi kokuma hugging nashi itakuma bataso shine take fadamin nabata shawara rabuwa zatai da shi kokuma meyakamata tayimasa yadaina

AMSA:

USMANNOOR: To da farko dai muna addu'a Allah ya shiryi wannan saurayi nata domin kuwa wannan ba dabi'a ce mai kyau ba

Abin na lura anan shine daya daga cikinsu kokuma gaba dayansu sun gina soyayyarne akan tafarkin son kai, ma'ana basu miqawa Allah zabi ba ta hanyar yin addu'ar neman zabin Allah SWT wato ISTIKHARA, kamar yanda Jabir Bin Abdullah ya rawaito hadisin da isnadi mai kyau (Addu'ar tazo a cikin littafin Hisnul Muslim wallafar marigayi Shaikh Sa'ed Alqahtany), domin kuwa duk wanda zaiyi addu'ar ISTIKHARA da zuciya daya bazai bige da irin wannan ashararancin ba, domin kuwa hakan daga shaidan ne, yayi amfanida son zuciyarnan da aka gina soyayyar akai

Na 2 kuma akwai tasirin so, wanda shine yasa qawartaki ta kasa rabuwa da shi har saita tambayi shawararki, a yanzun haka son da take nuna masa yakai mataki na 3 a cikin matakai 5 a fahimtar wasu al'ummar. Matakin 1. shine kaga mutum ya birgeka amman kana wucesa saika mantashi. Na 2 shine wanda idan ka hadu da shi halinsa ya burgeka saikaji kana sonshi koda kuwan ba aurensa zakayiba. Na 3 kuma gaba daya zaizamana baka son rabuwa da shi koda kuwan yana aikata laifi saboda kana masa kwadayin shiriya, ma'aurata sunfi bayyana wannan. Na 4 kuma son da mukeyiwa Annabi SAW wanda anason yafi son kowanne mutum, sannan na 5 kuma na karshe son da mukeyiwa mahaliccinmu wato Allah SWT

Kuskuren da tayi anan shine, ta dauki mataki na 3 wato son da ma'aurata suke a junansu alhalin ita saurayintane kawai, shiyasa take shakkar rabuwa dashi. Anan yakamata tasanardashi cewar bazan iya kissing ko hugging nakaba domin kuwa Allah SWT ya ce a cikin Suratun Nur ayata 3

( الزَّانِي لَا يَنكِحُ إِلَّا زَانِيَةً أَوْ مُشْرِكَةً وَالزَّانِيَةُ لَا يَنكِحُهَا إِلَّا زَانٍ أَوْ مُشْرِكٌ ۚ وَحُرِّمَ ذَٰلِكَ عَلَى الْمُؤْمِنِينَ )

النور (3) An-Noor

Mazinãci bã ya aure fãce da mazinãciya kõ mushirika, kuma mazinãciya bãbu mai aurenta fãce mazinãci kõ mushiriki. Kuma an haramta wannan a kan mũminai.

Sannan kuma Allah ya ce a cikin Suratul Isra ayata 32:

( وَلَا تَقْرَبُوا الزِّنَا ۖ إِنَّهُ كَانَ فَاحِشَةً وَسَاءَ سَبِيلًا )

الإسراء (32) Al-Israa

Kuma kada ku kusanci zina. Lalle ne ita ta kasance alfãsha ce kuma tã mũnãna ga zama hanya

Mu fahimtafa bawai kada mu aikataba, saboda girman laifin saiyace KADA MU KUSANCETA, to kinga anan baima kamata ya ce rungumeshi kokuma tayi kissing dinsaba, domin kuwa a matsayinmu na Bani Adama, Allah ya haliccemu kuma yasaka sinadarin adrenaline (hormones) a jikinmu wanda a duk sanda jinsin dayanmu yahadu da na daya to hakan zai janyo sha'awa har yakaiga fadawa tarkon Zina (indai ba ga ma'aurataba masu raya sunnan Annabi SAW ba), shiyasa akace kada ku kusanci Zina

Ma'anar kissing shine, goga lebe akan leben wani domin tabbatarda tsantsar soyayya kokuma qauna, anan shi saurayinnata bayyana mata yayi bawai tabbatarwaba kuskuren kenan, kamata yayi ya tabbatarda yana sonta tayi kissing din idan ya aureta amman sai ya bayyana ma'ana yanasonta da Zina bawai da aureba. Ma'anar hugging kuma shine rungume mace ko namiji wanda ba muharramiba shi wannan kanin Zina ne domin indai za a kira Kissing da gambo to Zina da Hugging twins ne. Kuma akwai Sahihin Hadisin da Annabi SAW ya ce: Da dayanku ya hada hannu da mace (gaisuwa) gwara ya zauna akan garwashi

Dangane da batun kissing kuma, ya tabbata a cikin Hadisi Sahihi Nana Aisha (RA) tace: "Manzon Allah SAW yakasance yana sumbatar iyalansa a duk sanda ya shigo gidansa".

Haka kuma Urwah RA ya rawaito daga Nana Aisha RA tace masa: "Annabi SAW ya sumbaci daya daga cikin matansa". Sai Urwah RA ya tambayi Nana Aisha RA: "Ko dai kece wadda ya sumbata (kissing) ?" Sai Nana Aisha RA tayi murmushin (Wanda haka ke nuni da ita Ma'aiki SAW yayiwa kiss

(Hadisin yana cikin Sunan al-Tirmidhi 86, Sunan abu-Dawud 181 da kuma Sunan al-Nasa'i 170)

Wannan shine abin da yawancin mazajen yanzu suka kasa koya shiyasa aketa samun rashin fahimta dakuma yawaitar sakin aure akai-akai, kissing matarka yana nufin tabbatarda so da qaunar da kake mata, da baka sonta ai da bazaka biya sadakintaba, amman duk anyi watsi da Sunnar Annabi SAW shiyasa muketa shan wahala a rayuwarmu. Idan wani magidancin ya ce kai akwai kunyafa nayi kissing matata kuma raini na iya shiga tsakaninmu to sai muce masa a ba wanda yakai Annabi SAW kunya (Kamar yanda ya tabbata a cikin Seerah) kuma maimakon zubewar qima saidai hakan ya qara janyo so da qauna a tsakani

Wannan kenan, fatan magidanta zasu dinga dabbaqa wagga Sunnah

Mafita ga shi wancan saurayinnata anan shine yakamata a sanardashi dalilin dayasa ma har yake bukatar tayi masa hakan (kissing din) wanda yana cikin ilimin addinin Islam wanda kimiyya ta tabbatarda hakan, cewar qwaqwalwar mutum ta rabu kaso 4. Na 1: Temporal-lobe wanda shine wajenda yake tattara saqon haddace abu, koyon abu, koyon yare da daukar sauti idan yakasance mai yawan sauraren kide-kidene saurayinnaki saiya daina domin kuwan suna tasiri kuma suna kai mutum ga aikata Zina. Na 2: Parietal-lobe wajenda yake tattara tabawa, karatu, shauqi, gane fuska, gane lokaci, motsawa, hangen nesa, idan shauqinsa yakai wani mataki to zai dinga bayyana sha'awarsa anan kinga dalilin dayasa yayi batun tayi hugging dinsa kenan

Na 3: occipital-lobe wanda yake gane kalar abu, girman ko qanqanta, gane nisa ko tazarar abu, adana saqonnin gani, idan suna zance ta matso kusa da shi to shaidanne na ukunsu haka idan mai sha'awar kallon abin da aka haramtane to anan yakan tasirantu da ya rungumeta kokuma kissing dinta. Na 4: frontal-lobe wanda akafi sanida forelock shine gaban goshin mutum wajenda Allah ya tsarawa qwaqwalwar mutum ta adana, nutsuwa, tunani, hukunci, kawarda matsala, hangen gaba, halayya, dabi'a, aikin zunubin da yake aikatawa dakuma qaryar da mutum yakeyi, kamar yanda Allah SWT ya bamu labarin halayyar maqaryacinnan Abu Jahal maqiyin Musulunci da sukai zamani da Annabi SAW a cikin Suratul Alaq "14) Ashe baisaniba Allah yana gani ? 15) A'aha ! Lallene idan bai hanuba, lallene za Mu ja gashin makwarkwada (fore-lock) 16) Makwarkwada makaryaciya, mai laifi (Frontal-lobe), to anan sai a sanardashi wannan saurayinnata ta hanyar tura masa wannan ilimin daganan muna saran zai yiwa kansa karatun ta nutsu ya koma ga Allah ya daina bukatar hakan

A karshe, shawarar da zan bawa kawarnan taki shine: Ta ilimantar da shi ta sanardashi girman zunubin hakan, ta kwadaitardashi cewar so take su kasance tare har a cikin Aljannah gidan da babu tsufa ballantana mutuwa, idan ya dauka Alhamdulillah haka muke so amman idan ya nuna bazai dau shawararba sai kawai ta rabudashi, tayi addu'ar Allah ya zaba mata saurayi Nagari domin kuwan ya tabbatar mata da cewar shi din ba Nagari baneba

Wallahu ta'ala a'alam

Aturawa yan uwa musulmi maza da mata domin mu amfana da ilimin baki daya

Amsawa:

✍️Usman Danliti Mato (Usmannoor_As-salafy)

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

WHATSAPP👇

https://chat.whatsapp.com/Fc3hX6HoDt65aKhhKOiDpX

https:///

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments