Ticker

6/recent/ticker-posts

Kayan Gadon Mamaci

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalaamu Alaikum Wa Rahmatul Laah. Kayan aikin girki da maigida ya rasu ya bari ana amfani da su, kamar su gishiri da maggi da ashana da kananzir ko gas da abin da dangance su, ko su ma sun shiga cikin kayan gado?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laahi Wa Barakaatuh.

Kayan gado sun haɗe dukkan kayayyakin da mamaci ya mallaka ne manya da ƙanana, kamar waɗannan abubuwan:

1. Tsabar kuɗaɗe da su ke cikin bankuna da waɗanda su ke ajiye a cikin shaguna da cikin gida, ko waɗanda su ke a hannun waɗansu a matsayin bashi, har da waɗanda su ke cikin aljihunsa.

2. Kadarorin da ya mallaka, kamar gidaje da jirage da motoci da filaye da gonaki da dabbobi da tsuntsaye da masana’antu da kamfanoni da ofisoshi da shaguna ko rumfunan kasuwa da sauransu.

3. Tufafin da ya mallaka ɗunkakku da waɗanda ba ɗunkakku ba, kamar riguna manya da ƙanana da wanduna da huluna da zannuwa da ɗankwalaye da takalma da safuna da agoguna da zobba da gajerun wanduna da ‘singlets’ da rigar nono da hijabai da mayafai da sikel da ɗan kamfai da sauransu.

4. Kayan amfani a cikin ɗakunansa, kamar akwatuna da gadaje da katifu da matasan-kai da zannuwan gado da mayafai ko barguna da labulayya da kujeru da tebura da shimfiɗu da tabarmi ko ledar ƙasa da agogunan bango da na tebura da sauransu.

5. Kayan ado da kwalliya da ya mallaka irinsu: Sabulan wanka da wanki da mayukan shafawa da na kitso da turarukan shafawa da na fesawa da na wuta, kuma da kwalli (tozali) da gazal ko ja-gira da sarƙa da warwaro da yan kunne da sauransu.

6. Kayan da yake amfani da su a cikin gida, kamar randuna da bokatai da bahuna da kwanduna da tukwane da kwanuka da kofuna da farantai da cokula manya da ƙanana da masu yatsu da ludaya da wuƙaƙe da adduna da gatura da faretani da garmuna da turamen daka da blenders da gas cookers da stoves da ashana ko lighters da sauransu.

7. Kayan abincin da ya bari a ‘store’, kamar su: Masara da shinkafa da wake da gari da dankali da taliya da man girki da nama da kifi da madara, da kayan miya irin su: Albasa da tumatiri da tattasai da atarugu da yaji da gishiri da maggi da kanwa da daddawa, da ganyayyaki irin su: Alayyaho da latas da zogale da rama da sauransu.

8. Sauran na’urorin da ya mallaka kamar su: Kayan kallo da rediyo manya da ƙanana, na saurare da masu hoto, da naurar komfuta da wayoyin hannu da kayan wuta irinsu: Injin janareto da dutsen guga da injin wanki da fridge da freezer da naurar dafawa ko gasawa ko dumama abinci, da sauran irinsu.

9. Kayan haskakawa da ƙawata ɗakunan gidajensa, kamar su: Ƙwayayen lantarki da tocila da fitillun kan tebur da na bangaye da fankoki da esi da sauransu.

10. Kayan karatu da rubutu da ya mallaka, kamar su: Tebura da kujeru da littaffan karatu da na rubutu da alƙaluma irin su birori da markers da alluna da fensirori da ruloli da failoli da sauransu.

Duk waɗannan su ne ake tattarawa da zaran mamaci ya rasu a ware su a gefe. Ba za a bari wani ya yi amfani da wani abu daga cikinsu ba, sai daga bayan an gama raba wa magadansa, a bayan an gama biyan bashinsa da kuma wasiyyar da ya yi.

Amma idan akwai larura, kamar ta tsananin buƙatar son yin amfani da wani abu daga cikin waɗannan irin kayayyakin a wurin wani daga cikin magadan, ko kuma akwai tunanin za su iya lalacewa idan ba a yi amfani da su ba, malamai sun yarda cewa a yi amfanin da su. Amma kuma lallai a lissafe su, ta yadda idan an zo rabon gadon za a yi bayanin su, kuma a cire su daga cikin kason dukiyar wanda ya yi amfani da su. Sai dai ko idan sauran ’yan uwa masu gadon mamacin sun yafe masa.

Shiyasa malamai suke son a gaggauta batun rabon gadon mamaci, a bai wa kowane mai haƙƙi haƙƙinsa, kar a bari wani abu ya salwanta daga cikin hakan.

WALLAHU A'ALAM

Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/Du5LNx31U9hDi6RQbbrzgW

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments