TAMBAYA (14)❓
Assalamualaikum. Barka da shan ruwa. Pls ina da
tambaya ne pls. Wani bawan Allah ne yake min complain sosai akan yana mafarki
mara dadi sosai. Wai yana gida sai shanu su biyo shi Su yi ta dukan kofar gidan
da kahon su, wai sai sun shigo shikuma yai ta kuka yana addu'ah, Sai ya shiga
dakinsa ya rufe. Shikuma macijin a kan window yake sai ya shige Wani rami. Pls
we need your response ASAP. It's getting out of control
AMSA
USMANNOOR: Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa
barakatuh. Alhamdu lillahi rabbil alamin wassalatu wassalamu ala rasulillah wa
ala alihi wa sahbihi ajma'in. Da farko dai ya kamata mu san mafarki kala nawa
ne ? Domin kuwan sanin rabe raben fassarar mafarkan zai bude kofar sanin
maganin mummunan mafarkin da yakeyi.
Annabi SAW ya ce: "Mafarki mai kyau (ru'ya)
daga Allah SWT ne, mummunan mafarki kuma (hulm) daga shaidan ne, don haka duk
wanda ya ga abin da baya so a mafarki, sai yayi tofa sau 3 a bangaren hagunsa
ya nemi tsarin Allah, ba abin da zai sameshi" (Sahih al-Bukhari, 3118)
A musulunci mafarki kala 3 ne, na farko shine
mafarki wanda yake na al'ada, misali: idan mutum ya ci abinci saiya kwanta bai
sha ruwa ba, to zai iyi mafarki gashinan a kusada teku kokuma korama yanata
shan ruwa kokuma ya tsinci kansa yana shan pure water ko wani abu makamancin
wannan. Wannan irin mafarkan babu wata illa ga mutum dukda dai kowanne irin
mafarki yanada irin ma'anarsa
Saikuma mafarki na 2 shine na alkhairi akan wani
albishir da akewa mutum ana kiran wannan mafarkin "ru'ya", misali:
mafarkin Aljannah kokuma wata korama, mafarkin ganin Manzon Allah SAW (Kitabu
Al-ru'ya littafi na 29 hadisi mai lambata 5639 wanda Jabir bin Abdullahi ya
karbo hadisin cewar Manzon Allah SAW ya ce: "Duk wanda ya ganni a mafarki
to hakika ni ya gani, saboda shaidan baya irin shigata a mafarki"), haka
kuma zaka iya yiwa wani mafarki kamar ka ga abokinka a mafarki yana dawafi a
Kaaba bayan wani lokaci kuma sai Allah cikin ikonSa kuma kaga ya kirasa Hajji
ko Umra.
Watannin baya da tsakar rana na taba mafarkin
matar abokinmu ta haihu, inata nemansa nayi masa albishir nace masa kuma yayi
kyauta, bamu hadu ba sai bayan kwana 3, muna haduwa na fada masa yayi matukar
farin cikin sannan ya cemin amman yayi mamaki saboda yau kwana 3 kenan da
zuwansu asibiti aka gano tana dauke da juna biyu. Kuma nima kwana 3 din da ya
wuce dinne dai nayi wannan mafarkin. Idan ba ikon Allah ba, ta yaya haka zata faru
? (Allah ya sauke ta lafiya)
Irin wadannan mafarkai na bushara ne daga Allah
SWT
Na karshe kuma na 3 shine mafarki mummuna kokuma
na sharri, shikuma ana kiransa da "hulm" misali: zai iya mafarkin ana
masa azaba da wuta, kokuma, dannau ya danne mutum, kokuma dabba ta biyoka
(misali mafarkin shanu suna tunkushinka kokuma micizai suna saranka), wadannan
duk daga shaidan ne. Kuma anayiwa mutum mafarki, akwai sanda na taba mafarki
wani abokin karatuna an biyoshi anata dukansa har saida ya karye, lokacinda na
farka na fada masa nace yayi sadaka saboda neman kariya, kullum da safe sai ya
bada sadakar kosai
A satin sai wannan iftila'in ya faru amman ba
akanshi ba, cikin ikon Allah sai karayar ta sauka akan wani abokin karatunnamu
daban, mashin ya bugeshi ya karye, so kaga anan fassarar mafarkin da nayi ta
fito kuma sadakar kosan nan da yake itace ta zame masa garkuwa
Abin da yake kawo mafarki mummuna "hulm"
yanada alaqa da mantawa dakuma sakaci na rashin azkar din kwanciya bacci kamar
yanda Manzon Allah SAW ya koyardamu
Imam Muslim ya rawaito hadisi wanda aka karbo daga
Samura bin Jundab ya ce duk lokacin da Annabi SAW ya idar da sallar asuba yakan
juyo da fuskarsa mai albarka garemu sannan ya ce: "Shin akwai wani a
cikinku wanda yayi mafarki a jiya da daddare" ? (Kitabu Al-ru'ya littafi
na 29 hadisi na 5652)
Ana son mutum ya saba da aikata wadannan sunnonin
guda 7 kamar haka:
1) Ka fadawa abokinnaka ya dinga alwala cikakkiya
kafin ya kwanta saboda hadisin da yake a cikin sahih Muslim mai lambata 2710
cewar wani sahabi ya ce: Annabi SAW ya ce "Duk sanda zaku bacci to kuyi
alwala kamar dai ta sallah, sannan ku kwanta da tsagin dama
2) Ya dinga karanta Amanar Rasulu kafin ya kwanta.
An karbo daga Abu Mas'ud ya ce Annabi SAW ya ce: "Duk wanda ya karanta
ayoyin karshe na Suratul Baqara to sun isar masa" (Sahih Al-Bukhari 5009)
3) Ya dinga kakkabe shimfidarsa, saboda Hadisin
Abu Hurairata RTA wanda Manzon Allah SAW ya bada umarnin a dinga kakkabe abin
kwanciya kafin ayi bacci saboda mutum baisan menene abin da ya sauka akan
shimfidarsa ba lokacin da bayanan (Bukhari 6320 da Muslim 6714a)
4) Ya dinga karanta azkar. An karbo Hadisi daga ya
ce Nana Fatima RA tazo wajen Annabi SAW ya bata baiwa wadda zata tayata aiki,
sai Ma'aiki SAW ya ce: "Bana baki abin da yafi baiwa ba ?" Saiyace:
"Kafin ki kwanta bacci ki dinga karanta Subhanallah 33, Alhamdulillah 33
saikuma Allahu Akbar 34" Sayyadina Ali RTA ya ce: "Tun da naji wannan
(garabasa) ban taba fashin kwanciya ba face saina karantasu" Sai wani
sahabi ya ce ko a daren yakin Siffin saida ka karantasu sai Sayyadina Ali RTA
ya ce ko a daren yakin Siffin (Bukhari 5362 da Muslim 2727a)
5) Ya dinga kwanciya da tsagin dama. Saboda
hadisin da Hudaifatul Yamani RTA ya karbo cewar duk sanda Annabi SAW zai kwanta
bacci yakan saka hannunsa na dama a kuncinsa sannan ya ce: "Allahumma
bismika amutu wa'ahya" Sannan kuma idan ya tashi sai ya ce:
"Alhamdulillahil lazi ahyana ba'ada ma'amatana wa'ilaihinnushur"
(Hadisin yana cikin Sahihul Bukhari mai lambata 6314)
6) Maybe abokin naka yana kwanciyar ruf da ciki
ne. Akwai hadisi wanda Abu Dharr Al-Gifari RTA ya karbo ya ce: "Akwai
lokacinda Ma'aiki SAW yazo wucewa sai ya ganni nayi kwanciyar ruf da ciki sai
yasa kafarsa mai albarka ya zungureni ya ce: "Ya Junaidib ! Wannan itace
irin kwanciyar yan wuta" Sahih (Darussalam) Ibn Majah 3724
7) Ya dinga karanta Ayatul Kursiyyu kafin ya
kwanta bacci. Saboda kissar abin da ya faru tsakani Abu Hurairah da Shaidan
wanda a karshe dai Shaidan ya bawa Abu Hurairah ayoyin kariya (Ayatul Kursiyyu)
cewar idan Abu Hurairah din ya karanta to Allah zai turo Mala'ika yayi gadinsa
babu Shaidanin da zaizo kusa da shi har gari ya waye. Har Ma'aiki SAW ya ce:
"Shaidan ya fadi gaskiya duk da dai makaryaci ne" (Bukhari 2311)
A karshe inason a sanar da shi cewar ya cire duk
wani hoto da yake a jikin bangon dakin da yake kwana, hoto wanda yake a rataye
na mutum ne ko zane haka, kamar irin zanen tsuntsaye/mage/shanu ko cartoon
characters haka kokuma irin hotunan nan na enlargement saboda munsan dai
hadisin da Sayyadina Ali RTA ya karbo cewar;
Watarana ya gayyaci Annabi SAW walima lokacin da
yazo sai yaga hotuna a gidan Sayyadina Alin saiya juya baya zai koma, sai ya ce
masa: "Ya Ma'aikin Allah ! Ran mahaifina da mahaifiyata fansa gareka,
saboda me zaka koma ?" Sai Annabi SAW ya ce: "Lallai da akwai labule
a gidan kuma a jikin labulen da akwai hoto, kuma mala'iku basa shiga gida wanda
akwai hoto" (Na fito da wannan hadisi ne daga cikin littafin Zad Al-Ma'ad
na Imam Ibn Al-Qayyim Aljauziyya Rahimahullah wanda ya kafa hujjar hadisin da
riwayar Ibn Majah 2/323 da Abu Ya'ala a musnad dinsa sannan kuma hadisin sahihi
ne wanda Ibn Majah ne marawaicinsa)
Akwai wata fira da na taba jin wani Aljani ya ce
suna hawa kan hoto dukda dai yawancin Aljanu akwai su da zuqi ta malli amman
idan kayi comparing hadisin can zakaga cewar indai har mala'iku bazasu shigo
gida mai hoto ba to tabbas kam Aljanu sun samu wajen fakewa, maybe hakan yasa
suyita tsoratarda abokinnaka a mafarki silar hotunan da suke a makwancin nasa
kamar yanda suka taba tsoratarda wata dalibata bayan magariba taga wani Aljani
ya fito daga jikin drawing dake bangon kitchen din gidansu ya biyota ta kwalla
ihu ta shige dakin mamansu, sai da safiya tayi aka goge drawing din saboda kowa
ya kasa gogeshi a daren jiya. Nace mata ta yawaita karanta azkar na safiya da
maraice
Allah ya kiyayemu daga sharrin kawunanmu dakuma
sharrin Aljanun dake rayuwa tare damu, Amin
Subhanakallahumma wabi hamdika ash'hadu anla ilaha
illa anta, astaghfiruka, wa'atubi ilayk
WALLAHU TA'ALA A'ALAM
Aturawa yan uwa musulmi maza da mata domin mu
amfana da ilimin baki daya musamman ma a wannan zamanin wanda gidaje dai dai ne
da babu hoto a ciki
Amsawa:
✍️Usman
Danliti Mato (Usmannoor_As-salafy)
Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku
kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/IerSx3AH0ZSJyHIuIYfqds
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.