Ticker

6/recent/ticker-posts

Karin Magana Bayan Zuwan Musulunci

Zuwan addinin Musulunci ƙasar Hausa ya yi tasiri a aikin adabinsu lokacin da addini ya shigo Hausawa suka sami ilimin karatu da rubutu wanda ya kara nuna cewa harshen Hausa rayayye ne da haka ne hudu ta shiga aka gina karin maganganun masu ƂarƂishin larabci da bayanin Adinin Musulinci bisa tafarki mai inganci. Misali:1. Abin da ka raba kafiri da musulmi sallah
2. Alfijir ba shi bayyana sau biyu
3. Allah ba ka dole.
4. Allah gatan kowa.
5. Allah mai hukunci da Adalci
6. Ana barin ba sallah holoƙo.
7. Ana yabonka salla ka kasa alwala.
8. Annabawa masoyan Allah ne
9. Bisa rangwame ga Allah, tuba.
10. Don lada ake yin sallah
11. Kowa ya yi sallah da karatun bakinsa.
12. Kowane allazi da nashi amanu.
13. Salati naka lada tawa.
14. Ta malam ba ta wuce amin.
15. Watan azumi a sha kallo.

www.amsoshi.com

Post a Comment

0 Comments