Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Yin Gori

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

As-Salaam Alaikum Wa Rahmatul Laah. Malam, mutumin da ya samu wani abu: Dukiya ko matsayi ko wani aiki da sauransu ta hanyar wani mutum ko da taimakonsa, sai kuma daga baya wannan ɗin ya rinƙa yi masa gori. Ina hukuncin wannan a addini?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah Wa Barakaatuh.

A cikin Alqur’ani Suratul Baqarah, Aya: 264 Allaah Ta’aala ya ce:

يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا لَا تُبْطِلُوا صَدَقَاتِكُمْ بِالْمَنِّ وَالْأَذَىٰ كَالَّذِي يُنْفِقُ مَالَهُ رِئَاءَ النَّاسِ وَلَا يُؤْمِنُ بِاللَّهِ وَالْيَوْمِ الْآخِرِ ۖ ...

Ya ku waɗanda suka yi Imani! Kar ku ɓata sadakokinku da gori da cutarwa, kamar wanda ke ciyar da dukiyarsa domin yin riya ga mutane, kuma ba ya yin imani da Allaah da Ranar Lahira.

Daga wannan ayar malamai suka nuna cewa:

1. Ma’anar Mannu (gori) shi ne: Nuna girman matsayin mai bayar da sadakar a kan wanda aka ba shi sadakar.

2. Ma’anar Azaa (cutarwa) kuwa shi ne: Kamar mai bayar da sadakar ya gaya wa wasu mutane cewa: Ni na bai wa wane sadakar abu kaza. Domin idan wanda aka ba sadakar ya ji, zai cutu.

3. Sadaka a nan tana iya haɗawa da duk wani aikin alheri da aka yi wa mutum, kamar taimaka masa don ya samu wani matsayi, misali.

4. Yana daga cikin siffar musulmi mai imani ya nisanci yin gori da cutarwa ga duk wanda ya ba shi sadaka.

5. Barin yin gori da cutarwa a kan sadaka yana daga cikin ayyukan da suke ƙara wa musulmi Imaninsa.

6. Yin gori da cutarwa ga wanda aka ba shi sadaka yana daga cikin ayyukan da suke raunana imanin musulmi.

7. Yin gori a kan wani abin sadaka da mutum ya bayar haram ne, domin Allaah Ta’aala ya hana yin hakan.

8. Faɗin cewa: Kar ku ɓata sadakokinku da gori ya fi faɗin cewa: Kar ku yi gori tasiri a cikin zuciya. Wannan ya nuna balaagha da ƙwarewar Alqurani a wurin magana.

9. Yin gori da cutarwa yana ɓata ladan sadakar da mutum ya yi, saboda maganarsa cewa: ‘Kar ku ɓata sadakokinku’.

10. Yin gori da cutarwa yana daga cikin manyan kaba’irai na zunubi, saboda ya kamanta masu yin sa da masu riya, marasa cikan imani da Allaah da Ranar Lahira.

11. Masu yin riya kuma marasa imani da Allaah da Ranar Lahira su ne munafukai, waɗanda Imani bai zauna a cikin zukatansu ba. 

12. Munafukai kuwa kamar yadda ya faɗa a cikin Alqur’ani ne:

إِنَّ ٱلۡمُنَـٰفِقِینَ فِی ٱلدَّرۡكِ ٱلۡأَسۡفَلِ مِنَ ٱلنَّارِ وَلَن تَجِدَ لَهُمۡ نَصِیرًا

Haƙiƙa! Munafukai su ne a ƙarshen kadarkon wuta na-ƙasa, kuma ba za ka taɓa samun mataimaki gare su ba. (Surah An-Nisaa’: 145).

Kuma ya tabbata a cikin Sahih Muslim (106) daga hadisin Abu-Zarr (Radiyal Laahu Anhu) cewa Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce:

Mutane uku Allaah ba zai yi magana da su ba a Ranar Al-Qiyama, ba zai dube su ba, ba zai tsarkake su ba, kuma suna da azaba mai raɗaɗin gaske: Mai sakin tufafinsa ƙasa da idon-sawu, da mai yin gori, da mai sayar da kayan sayarwansa da rantsuwar ƙarya.

Allaah ya kiyashe mu.

Wal Laahu A’lam.

Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments