Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Sauraron Waka

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalaamu Alaikum Wa Rahmatul Laah. Muna tambaya a kan maganar wani malami da ake yaɗawa a cikin social media a kwanakin nan cewa: ‘Wajibi ne mutum - ko malami ko ba malami ba - ya riƙa jin waƙa kowace iri, wacce ransa yake so. Menene gaskiyar wannan maganar a sharia?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laahi Wa Barakaatuh.

Ma’anar waƙa dai a wurin malamai ita ce: Tsararriyar magana mai amsa-amo. Tun dayake ita magana ce, to akwai kyakkyawa kenan a cikinta kuma akwai mummuna, kamar yadda muka yi bayani a akan "SANAAR WAƘA" Kuma At-Tabaraaniy a cikin Al-Awsat ya riwaito daga Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) da wani isnadin da Al-Albaaniy ya inganta shi saboda tattaruwan hanyoyinsa cewa: Ita waƙa tana matsayin magana ce: Kyakkyawarta kamar kyakkyawar magana ce, mummunarta kuma kamar mummunar magana ce. (Sahih Al-Adabil Mufrad: 664).

Don haka, cewa wajibi ne a riƙa jin kowace irin waƙa ba daidai ba ne, kuskure ne mummuna a fili.

Dalili a kan haka kuwa:  Allaah Ta’aala ya ce:

وَٱلشُّعَرَاۤءُ یَتَّبِعُهُمُ ٱلۡغَاوُۥنَ ٤٢٢۝

Kuma su mawaƙa, ɓatattu (sheɗanu ko mutanen banza) ne suke bin su. (Surah As-Shu’araa’: 224)

أَلَمۡ تَرَ أَنَّهُمۡ فِی كُلِّ وَادࣲ یَهِیمُونَ ٥٢٢۝

Ba ka gani ba ne cewa su a cikin kowane kwari na magana suna yin ɗimuwa. (Surah As-Shu’araa’: 225)

وَأَنَّهُمۡ یَقُولُونَ مَا لَا یَفۡعَلُونَ ٦٢٢۝

Kuma su suna faɗin irin abin da ba su aikatawa. (Surah As-Shu’araa’: 226)

إِلَّا ٱلَّذِینَ ءَامَنُوا۟ وَعَمِلُوا۟ ٱلصَّـٰلِحَـٰتِ وَذَكَرُوا۟ ٱللَّهَ كَثِیرࣰا وَٱنتَصَرُوا۟ مِنۢ بَعۡدِ مَا ظُلِمُوا۟ۗ وَسَیَعۡلَمُ ٱلَّذِینَ ظَلَمُوۤا۟ أَیَّ مُنقَلَبࣲ یَن.قَلِبُونَ ٧٢٢۝

Sai dai waɗanda suka imani kuma suka aikata ayyuka na-gari kuma suka ambaci Allaah da yawa kuma suka ɗauki fansa a bayan an zalunce su, kuma waɗanda suka yi zalunci za su san a wace majuya ce a ƙarshe za su juya. (Surah As-Shuaraa: 227)

Wannan ya nuna: Mawaƙa iri biyu ne:

1. Nau’in farko su ne waɗanda ya siffata su da siffofi uku: Sheɗanu ko mutanen banza ne suke bin su, suna yin ɗimuwa a cikin maganganunsu, kuma suna yin ƙarya a cikin maganganun.

2. Na-biyu kuma su ne: Waɗanda ya siffata su da siffofi uku su ma: Imani da Aikata ayyuka na-gari, da ambaton Allaah da yawa, da kuma ɗaukar fansa a kan wanda ya zalunce su.

Ya tabbata a cikin Sahih Muslim daga hadisin Abu-Sa’eed Al-Khudriy (Radiyal Laahu Anhu) ya ce, muna tafiya wata rana tare da Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) sai ya ji wani mawaƙi yana rera waƙa, sai ya ce:

« خُذُوا الشَّيْطَانَ أَوْ أَمْسِكُوا الشَّيْطَانَ لأَنْ يَمْتَلِئَ جَوْفُ رَجُلٍ قَيْحًا خَيْرٌ لَهُ مِنْ أَنْ يَمْتَلِئَ شِعْرًا »

Ku damƙe sheɗanin! Ko: Ku kama sheɗanin! Gara a cika cikin mutum da ruwan maruru mai cin jikinsa (hanta ko huhu) da a cika shi da waƙa. (Sahih Al-Bukhaariy: 6155, Sahih Muslim: 6032)

Malamai suka ce:

(هو) مَحْمُولٌ عَلَى مَنْ أَقْبَلَ عَلَى الشِّعْرِ، وَاشْتَغَلَ بِهِ عَنِ الذِّكْرِ، وَتِلَاوَةِ الْقُرْآنِ، وَطَاعَةِ اللَّهِ تَعَالَى، وَعَلَى الشِّعْرِ الْقَبِيحِ الْمُتَضَمِّنِ لِلْكَذِبِ، وَالْبَاطِلِ كَذِكْرِ الْخَمْرِ وَمَحَاسِنِ النِّسَاءِ الْأَجْنَبِيَّاتِ، وَنَحْوِ ذَلِكَ.

Wannan hadisin ana ɗaukarsa a kan wanda ya mayar da himma da ƙoƙarinsa ga waƙar ce, ya shagaltu da ita ya bar zikirin Allaah da tilawar Alqurani da ɗa’ar Allaah Ta’aala. Da kuma wanda ya shagaltu da mummunar waƙar da ta ƙunshi sharara ƙarya da sauransu. Ko waƙar da ta tattaru a kan ambaton giya ko kyawun siffofin matan da ba muharramai ba da sauransu. (Ad-Waaul Bayaan: 6/105)

Shiyasa Al-Bukhaariy ya kawo wannan hadisin a ƙarƙashin babin da ya raɗa wa suna:

باب مَا يُكْرَهُ أَنْ يَكُونَ الْغَالِبُ عَلَى الإِنْسَانِ الشِّعْرُ حَتَّى يَصُدَّهُ عَنْ ذِكْرِ اللَّهِ وَالْعِلْمِ وَالْقُرْآنِ

Babi: A kan abin da aka ƙyamata cewa: Waƙa ta zama it ace mai rinjaye a kan mutum har ta kange shi daga ambaton Allaah da ilimi da Alqurani.

Wannan kuwa shi ne galibin siffofin mawaƙa a yau, da masoyansu da mabiyansu, sai dai waɗanda Ubangiji ya tausaya wa, kuma su ’yan kaɗan ne. Allaah ya ƙara mana shiriya.

Haka kuma a kan irin wannan waƙar ce dai Allaah Taaala ya ce:

 وَمِنَ ٱلنَّاسِ مَن یَشۡتَرِی لَهۡوَ ٱلۡحَدِیثِ لِیُضِلَّ عَن سَبِیلِ ٱللَّهِ بِغَیۡرِ عِلۡمࣲ وَیَتَّخِذَهَا هُزُوًاۚ أُو۟لَـٰۤىِٕكَ لَهُمۡ عَذَابࣱ مُّهِینࣱ ٦۝

Kuma daga cikin mutane akwai wanda yake sayen lalataccen labari domin ya ɓatar da mutane daga bin hanyar Allaah ba da wani ilimi ba, kuma yana ɗaukar su abin yin izgili, waɗannan suna da azaba na wulaƙanci. (Surah Luqman: 6)

وَإِذَا تُتۡلَىٰ عَلَیۡهِ ءَایَـٰتُنَا وَلَّىٰ مُسۡتَكۡبِرࣰا كَأَن لَّمۡ یَسۡمَعۡهَا كَأَنَّ فِیۤ أُذُنَیۡهِ وَقۡرࣰاۖ فَبَشِّرۡهُ بِعَذَابٍ أَلِیمٍ ٧۝

Kuma idan aka karanta masa ayoyinmu sai ya juya da baya yana mai nuna girman kai, kamar dai bai ji su ba, kamar a cikin kunnuwansa akwai nauyi. To ka yi masa albishir da azaba mai raɗaɗi. (Surah Luqman: 7)

Sannan kuma hadisi ya tabbata daga Sahabi Abu-Umaamah Al-Baahiliy (Radiyal Laahu Anhu) daga Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce:

« لاَ تَبِيعُوا الْقَيْنَاتِ ، وَلاَ تَشْتَرُوهُنَّ ، وَلاَ تُعَلِّمُوهُنَّ ، وَلاَ خَيْرَ فِى تِجَارَةٍ فِيهِنَّ ، وَثَمَنُهُنَّ حَرَامٌ ، فِى مِثْلِ هَذَا أُنْزِلَتْ هَذِهِ الآيَةُ : ( وَمِنَ النَّاسِ مَنْ يَشْتَرِى لَهْوَ الْحَدِيثِ لِيُضِلَّ عَنْ سَبِيلِ اللَّهِ) إِلَى آخِرِ الآيَةِ ».

Kar ku sayar da zabiya (mata mawaƙa daga cikin bayi), kuma kar ku sayo su, kuma kar ku koyar da su, babu wani alheri ga yin cinikinsu, kuɗin cinikinsu haram ne. A cikin irin wannan ne aka saukar da wannan ayar: (Kuma daga cikin mutane akwai wanda yake sayen lalataccen labari domin ya ɓatar da mutane daga bin hanyar Allaah) har zuwa ƙarshsen ayar. (Sahih At-Tirmiziy: 2553).

Kuma an tambayi Ibn Mas’ud (Radiyal Laahu Anhu) a kan wannan ayar sai ya ce:

الْغِنَاءُ، وَالَّذِي لَا إِلَهَ إِلَّا هُوَ، يُرَدِّدُهَا ثَلَاثَ مَرَّاتٍ

Waƙa ce. Ina rantsuwa da wanda babu abin bautawa da gaskiya sai dai shi! Ya maimaita hakan har sau uku. (Tafseer At-Tabariy: 18/534-535)

Haka shi ma Ibn Abbaas (Radiyal Laahu Anhu) ya faɗa. (Tafseer At-Tabariy: 18/535)

Sannan shi kuma Al-Imaam Qataadah (Rahimahul Laah) ga abin da ya ce a kan ayar:

وَاللَّهِ لَعَلَّهُ أَنْ لَا يُنْفِقَ فِيهِ مَالًا، وَلَكِنِ اشْتِرَاؤُهُ اسْتِحْبَابُهُ، بِحَسْبِ الْمَرْءِ مِنَ الضَّلَالَةِ أَنْ يَخْتَارَ حَدِيثَ الْبَاطِلِ عَلَى حَدِيثِ الْحَقِّ، وَمَا يَضُرُّ عَلَى مَا يَنْفَعُ

Wallahi! Me yiwuwa ba sai ya kashe ko kwabo ba. Amma dai sayensa shi ne: Ƙaunarsa da sonsa. Ya kuwa ishi ɓacewa da lalacewa ga mutum ya zaɓi mummunan labari a kan labarin gaskiya, kuma ya zaɓi abin da yake cutarwa a kan abin da yake amfanarwa. (Tafseer At-Tabariy: 18/534)

Sannan kuma Al-Imaam At-Tirmiziy (Lamba: 2373) ya riwaito hadisin Imraan Bn Husayn (Radiyal Laahu Anhu) wanda Al-Albaaniy ya sahhaha shi cewa: Manzon Allaah Annabi Muhammad (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce:

« فِى هَذِهِ الأُمَّةِ خَسْفٌ وَمَسْخٌ وَقَذْفٌ »

A cikin al’ummar nan za a samu girgizar ƙasa da shafe mutane da jifa da duwatsu daga sama.

Da aka tambaye shi yaushe ne hakan zai auku? Sai ya ce:

« إِذَا ظَهَرَتِ الْقَيْنَاتُ وَالْمَعَازِفُ وَشُرِبَتِ الْخُمُورُ »

Idan zabiyoyi (’yan mata mawaƙa) da kayan kiɗa suka bayyana, kuma aka sha giyoyi. (Sahih Al-Jaami’: 4273).

Jama’a! Tun da akwai waɗannan nassoshin kuwa ta yaya za a iya amincewa da irin wannan maganar daga irin wannan malamin, a daidai lokacin da al’umma take fama da irin waɗannan mawaƙan maɓarnata:

(i) Masu mayar da waƙar ita ce sanaarsu da suke rayuwa a kanta!

(ii) Masu haɗa waƙar da muryoyin mata da suke lanƙwasa ta don motsar da shaawa!

(iii) Masu bayanin ayyukan haram da ƙawata su, kamar soyayya da siffata sassan jikkunan mata da maza a cikin waƙoƙinsu! Da sauransu!

Allaah ya sawwaƙe.

Su kansu waƙoƙin da suka halatta ma akwai matsalar kauce wa ƙaida yanzu a cikinsu. Alal misali, mu yi nazarin hadisin Aishah (Radiyal Laahu Anhu) mai cewa:

دَخَلَ رَسُولُ اللَّهِ - صلى الله عليه وسلم - وَعِنْدِى جَارِيَتَانِ تُغَنِّيَانِ بِغِنَاءِ بُعَاثٍ فَاضْطَجَعَ عَلَى الْفِرَاشِ وَحَوَّلَ وَجْهَهُ فَدَخَلَ أَبُو بَكْرٍ فَانْتَهَرَنِى وَقَالَ مِزْمَارُ الشَّيْطَانِ عِنْدَ رَسُولِ اللَّهِ - صلى الله عليه وسلم - فَأَقْبَلَ عَلَيْهِ رَسُولُ اللَّهِ - صلى الله عليه وسلم - فَقَالَ « دَعْهُمَا » فَلَمَّا غَفَلَ غَمَزْتُهُمَا فَخَرَجَتَا »

Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya shigo wurina alhali akwai waɗansu yara mata ƙanana suna yin waƙar ranar yaƙin buaath, sai ya kwanta a kan shimfiɗa ya juyar da fuskarsa. Sai Abubakar ya shigo ya tsawace ni, ya ce: Muryar sheɗan a wurin Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam)?! Sai Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya fuskanto shi ya ce: Ƙyale su, (domin kowaɗanne mutane suna da adininsu. Wannan ranar idinmu ce). Lokacin da ya shiga wata maganar sai na harare su, suka fita. (Sahih Al-Bukhaariy: 949, Sahih Muslim: 2102)

Wannan ya nuna:

(i) Waƙa har daga yara ƙanana abin ƙyama ce, tun da dai muryar sheɗan ce, kamar yadda Abubakar As-Siddeeq ya faɗa kuma Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) bai musanta masa ba.

(ii) Wannan ƙyamar ta ƙara bayyana ta yadda Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya kwanta ya juyar da fuskarsa, sannan kuma a ƙarshe Aishah (Radiyal Laahu Anhu) ta kore su suka fita.

(iii) Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya hana Abubakar ya yi wa yaran tsawa a kan waƙar da suke yi ne saboda cewa a ranar idi ce suke yi.

Daga cikin misalin mawaƙan kirki irin naui na-biyu akwai: Ibn Rawaahah (Radiyal Laahu Anhu) wanda ya faɗa wurin yabo da bayar da kariya ga Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) cewa:

وَفِينَا رَسُولُ اللَّـهِ يَتْلُو كِتَابَـــهُ   * إِذَا انْشَقَّ مَعْرُوفٌ مِنَ الْفَجْرِ سَاطِعُ

أَرَانَا الْهُدَى بَعْدَ الْعَمَى فَقُلُوبُنَا  *  بِـهِ مُوقِنَــاتٌ أَنَّ مَـــا قَـــالَ وَاقِــــعُ

يَبِيتُ يُجَافِى جَنْبَهُ عَنْ فِرَاشِـهِ  *  إِذَا اسْتَثْقَلَتْ بِالْكَـافِرِينَ الْمَضَـاجِـــعُ

A cikinmu ga Manzon Allaah yana karanta Littafinsa, a lokacin da sanannen alfijir mai ɗagowa ya keto.

Ya nuna mana shiriya a bayan ɓata sai zukatanmu, suka amince da shi cewa abin da ya faɗa zai auku.

Yana kwana yana nisanta jikinsa daga shimfiɗarsa, a lokacin da shimfiɗu suka nauyaya da mushirikai.

Shiyasa Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya yabe shi da cewa:

« إِنَّ أَخًا لَكُمْ لاَ يَقُولُ الرَّفَثَ »

Haƙiƙa ɗan’uwanku ba ya faɗin mummunar magana. (Sahih Al-Bukhaariy: 6151)

Ta yaya za a haɗa irin wannan da waƙoƙin jahilai masu ƙasƙanta matsayin Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ko ɗaukaka shi sama da matsayin da Allaah Ta’aala ya ajiye shi a kai!

Daga cikin waɗannan mawaƙan na kirki akwai Hassaan Bn Thaabit (Radiyal Laahu Anhu) wanda ya riƙa bai wa Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) kariya daga sukan da mushirikai suka yi masa, har yake cewa:

هَجَوْتَ مُحَمَّدًا فَأَجَبْتُ عَنْهُ   * وَعِنْدَ اللَّهِ فِى ذَاكَ الْجَزَاءُ

هَجَوْتَ مُحَمَّدًا بَرًّا تَقِيًّــــــا   * رَسُولَ اللَّهِ شِيمَتُهُ الْوَفَــاءُ

فَإِنَّ أَبِى وَوَالِــدَهُ وَعِرْضِى  * لِعِرْضِ مُحَمَّدٍ مِنْكُمْ وِقَـاءُ

Ka yi wa Annabi zambo ni kuma na kare shi, kuma sakayya a kan haka a wurin Allaah ne.

Ka yi wa Annabi mai alheri mai taqawa zambo, Manzon Allaah da siffarsa: Cika alƙawari.

Tabbas! Babana da babansa da mutuncina, duk na kariyar mutuncin Annabi ne daga ku.

Har dai zuwa ƙarshe.

A kan haka ne Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya faɗa ma Hassan ɗin cewa:

« إِنَّ رُوحَ الْقُدُسِ لاَ يَزَالُ يُؤَيِّدُكَ مَا نَافَحْتَ عَنِ اللَّهِ وَرَسُولِهِ »

Haƙiƙa! Ruuhul Qudsi (Malaika Jibril) yana nan a tare da kai matuƙar kana bai Allaah da Manzonsa kariya. (Sahih Muslim: 6550).

Irin wannan kyawawan kalmomin na waƙa ne suka halatta har a cikin masallaci a yi su, daidai gwargwado.

Sa’eed Bn Al-Musayyib (Rahimahul Laahu) ya ce: Umar ne ya wuce Hassaan a cikin masallaci yana rera waƙa (sai ya harare shi) sai shi kuma ya ce:

كُنْتُ أُنْشِدُ فِيهِ ، وَفِيهِ مَنْ هُوَ خَيْرٌ مِنْكَ

Na kasance ina rerawa a cikinsa alhali akwai wanda ya fi ka alheri a cikinsa. (Sahih Al-Bukhaariy: 3212).

Daga nan sai ya juya wurin Abu-Hurairah ya ce: Ina gama ka da Allaah! Ka taɓa jin Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) yana cewa:

« يَا حَسَّانُ أَجِبْ عَنْ رَسُولِ اللَّهِ ، اللَّهُمَّ أَيِّدْهُ بِرُوحِ الْقُدُسِ »

Hassaan! Ka bai wa Manzon Allaah kariya! Ya Allaah! Ka ƙarfafe shi da Ruuhul Qudsi (Malaika Jibril)?

Sai Abu-Hurairah ya ce: Haka ne. (Sahih Al-Bukhaariy: 6152).

Ko kusa ba za a haɗa waƙoƙin irin waɗannan manyan sahabbai da waƙoƙin waɗansu mutanen da suka zo a bayansu kamar a wannan zamanin ba, masu da’awar suna yin waƙoƙin addinin musulunci, domin dalilai kamar haka:

(i) Galibi suna haɗa waƙoƙin da abubuwan da ba su dace ba, kamar haɗa muryar maza da mata, da amfani da kayan kiɗa kamar tafi ko ƙwarya ko garaya ko molo ko goge ko kalangu da sauransu.

(ii) Sannan kalmomin da ake amfani da su a galibi ba su dacewa da koyarwar shari’a, kamar ɗaukaka darajar waɗansu manya sama da matsayinsu, ko kuma ƙasƙantar da matsayin su.

(iii) Ana samun masu haɗa Allaah da wani ko waɗansu daga cikin bayinsa a cikin siffofinsa, ko kuma ma ɗaukaka su a sama da matsayin nasa.

To, ta yaya za a ce wajibi ne a riƙa jin irin waɗannan waƙoƙin?!

Don haka, wajibi ne malamai da ɗaliban ilimi su riƙa taka-tsantsan a kan maganganunsu, musamman a wannan zamanin na cigaban hanyoyin yaɗa bayanai. Su kiyaye faɗin kalmomi a dunƙule ba tare da cikakkun bayanai masu fayyace manufa ba.

Allaah ya ƙara mana fahimta a cikin addinimu.

WALLAHU A'ALAM

Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments