𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
As-Salaam Alaikum Wa Rahmatul Laah. Wani ‘course’
ne a ke yi a jami’a na waƙa da rawa (music & dance). Jarabawarsa kuma
ita ce ɗaliba
ta fito a gaban maza da mata ta yi rawa, kuma ba da hijabi ba! In kuma ba ta yi
ba, to tana da ‘carry over’ (ana bin ta bashi) ko da shekaru nawa ne kuwa ba za
a yarda ba, har sai ta yi. To, ya halatta ta yi?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah Wa
Barakaatuh.
Al-Imaam Al-Bukhaariy (52) da Al-Imaam Muslim
(4178) sun riwaito daga An-Nu’maan Bn Basheer (Radiyal Laahu Anhu) wanda da
kunnuwansa ne ya ji Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) yana
cewa:
« إِنَّ الْحَلاَلَ بَيِّنٌ وَإِنَّ الْحَرَامَ بَيِّنٌ ، وَبَيْنَهُمَا مُشْتَبِهَاتٌ لاَ يَعْلَمُهُنَّ كَثِيرٌ مِنَ النَّاسِ ، فَمَنِ اتَّقَى الشُّبُهَاتِ اسْتَبْرَأَ لِدِينِهِ وَعِرْضِهِ ، وَمَنْ وَقَعَ فِى الشُّبُهَاتِ وَقَعَ فِى الْحَرَامِ ، كَالرَّاعِى يَرْعَى حَوْلَ الْحِمَى ، يُوشِكُ أَنْ يَرْتَعَ فِيهِ »
Haƙiƙa! Halal a fili ya ke, haram ma a fili ya ke. A
tsakaninsu kuma akwai wasu abubuwa masu rikitarwa waɗanda yawancin mutane ba su san su ba. To,
duk wanda ya kiyayi abubuwan nan masu rikitarwa, to ya tsira da addininsa da
mutuncinsa. Kuma amma duk wanda ya afka wa abubuwan nan masu rikitarwa, to ya
afka a cikin haram: Kamar dai makiyayi mai yin kiwo a gefen iyaka, ya yi kusa
ya shiga yin kiwo a cikinta.
Daga wannan hadisin muna iya fahimtar cewa:
1. Kiɗa da
rawa - musamman kamar yadda su ke a yau - ba su daga cikin abubuwan da za a
saka su cikin halatattun al’amura a cikin addini, kuma ba za a saka su ma a
cikin al’amuran da suka zama masu rikitarwa ba. Babu abin da ya rage a bayan
haka, sai dai a kai su gidan haramtattun abubuwa. Domin ko ba komai dai, ba a
san shaharar hakan a cikin Sahabbai da sauran musulmin farko ba, baya ga abubuwan
da ke cikinsu na fasiƙanci da rashin mutunci.
2. Sannan ko da ma an samu aukuwan wani abu na
hakan a cikin zamunnan musulmin farko, wannan kam bai yi kama da yadda abin ya
ke a yau ba, kuma bai nuna cewa ya halatta a cigaba da koyar da shi ga matasan
wannan al’ummar ba, musamman kuma a irin wannan hali da yanayin da musulmi suke
cikin sa. Halin da a cikinsa suke fama da suka da zagi da wulaƙanci
da kyara da hare-hare da kisan ƙare-dangi ta ko’ina, kuma a ko’ina a cikin duniya.
Dangane da darussa a cikin jami’a kuwa, wajibi ne
duk matasanmu na musulmi su san cewa:
Jami’a matattara ce kamar kasuwa: Akwai mutanen
kirki daga cikin malamai da ɗalibai
da sauran ma’aikata, masu koyo da koyar da alheri da sha’awar yaɗuwarsa a cikin al’ummar ƙasa.
Sannan kuma akwai mugayen mutanen banza masharranta masu yawa daga cikin
malamai da ɗalibai
da ma’aikata, waɗanda
suke sha’awar yaɗuwar
sharri da ɓarna a
cikin al’ummar ƙasa.
Don haka, kafin ɗalibi ko ɗaliba ya shiga jami’a wajibi ne iyaye da
manyan masana da sauran ƙungiyoyin musulmi a ciki da wajen jami’o’inmu, su yi zama na musamman da su, su nuna musu kuma su fahimtar da su duk
irin waɗannan
abubuwan, kuma su cigaba da bibiyansu tare da yi musu jagora a cikin tsawon
rayuwarsu a cikin jami’o’in, don fatar su zama manyan da musulunci da musulmi za
su yi alfahari da su a gobe.
Ta yaya za mu ƙyale matasanmu maza da
mata suna koyon kiɗa da
waƙa da rawa a jami’a, a
daidai lokacin da sa’o’insu a ƙasashen Turai da Amirka
su ake koya musu harkokin ƙere-ƙere da yaƙe-yaƙe na zamani, kamar ta bin umurnin manyansu
wurin amfani da jirage marasa matuƙa (drones), suna kai munanan hare-hare na
hallakarwa ta ‘satelite’ a kan duk wanda suka so, a daidai lokacin
da suka so, kuma a duk inda suka so?!
Don Allaah! Akwai ɓacewar basira da lalacewar da ta fi
wannan?
Amma game da wannan fatawar, wajibin mai ita shi
ne ta sauya wani ‘course’ kawai ko dai a wannan jami’ar ko a wata, wanda zai
zama mai amfani gare ta da iyalinta da al’ummarta. Amma ba ya halatta mace ta
yi rawa a gaban mazan da ba muharramanta ba, ko da hijabi ne a jikinta,
ballantana kuma babu!
Abin tambaya ma a nan shi ne: Wai bayan ta gama
wannan course ɗin, me
mace za ta yi da shi? Za ta zama mai sana’ar rawa kenan, ko kuwa mai koyar da
rawa ana biyan ta?! Menene amfanin wannan gare ta da al’ummarta saboda
Allaah?!!
Kuma wajibi ne ga shugabanni a jami’o’in
yankunanmu su yi duk mai yiwuwa da gwargwadon ƙarfinsu da ikonsu wurin
ganin an yi watsi da irin waɗannan
darussa na shegantaka da rashin mutunci a cikin ’ya’yanmu.
Allaah ya sa mu faɗaka, mu gane.
WALLAHU A'ALAM
Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku
kasance Damu...
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.