Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Matar Da Ta Taɓa Yin Zina Sai Tayi Aure Ba Tare Da Ta Tuba Ba

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum. Mace ce ta taɓa yin zina shekaru goma da suka wuce, kuma bayan shekaru biyar daga haka ta yi aure, har kuma ta samu haihuwa. A bayan auren ne ta ji wa’azi a kan Surah An-Nuur aya ta 3 cewa: Duk wanda ya yi aure kafin tuba daga zina, to aurensa bai yi ba. Shi ne hankalinta ya tashi don ba ta iya tuna ko ta tuba ba a wancan lokacin! Don haka ta gaya wa mijinta, wanda ya fusata kuma ya bayyana mata cewa babu komai. Sai kuma ta sake shiga ruɗani a lokacin da ta karanta a wani wuri cewa: Duk wanda ya auri mazinaciya alhali yana sane to zaman zina suke yi, kuma duk ’ya’yan da suka haifa shegu ne! Yanzu wai menene matsayin gaya wa mijinta da ta yi, kuma yaya matsayin ’ya’yan da suka haifa?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah.

Akwai maganganu masu yawa a kan fassarar wannan ayar ta cikin Surah An-Nuur a wurin malamai, kamar yadda ya zo a cikin Al-Jaami’u Li Ahkaamil Qur’aan na Al-Imaam Al-Qurtubiy (12/173-177).

A taƙaice dai:

Gaya wa mijinta wannan maganar, kodayake bai kamata ba, amma dai bai shafi auransu da komai ba. Domin ayar tana magana a kan wanda ya san cewa wadda zai aura mashahuriyar mazinaciya ce kuma ba ta tuba ba, amma kuma ya cigaba ya aure ta. Saboda ƙissar Marthad Bn Abi-Marthad (Radiyal Laahu Anhu) da ya nemi auren karuwarsa Anaaq, sai Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya karanta masa wannan ayar sannan ya ce: Kar ka aure ta. (Abu-Daawud: 2051; At-Tirmiziy: 3177, Al-Albaaniy ya ce: Hasan Saheeh ne).

Aurensu zai iya samun matsala ce kawai idan mijin ya gano har a bayan aurenta ba ta daina yin zinar da wasu mazan ba, kuma amma ya ƙyale ta. Saboda hadisin da Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ambaci mutane ukun da Allaah ya haramta musu shiga Aljannah, kuma ya cike da: Ad-Duyuuth (mara kishi) wanda yake amincewa da ɓarna a cikin iyalinsa. (As-Saheehah, a ƙarshen hadisi mai lamba: 674)

Ya’yansu kuma ’ya’yan Sunnah ne, ba shegu ba ne. Laifin zinar da ta aikata ba zai shafi auren Sunnah da suka yi a bayan hakan ba. Hadisin Marthad Bn Abi-Marthad Al-Ghanawiy (Radiyal Laahu Anhu) da ya gabata ya nuna matsalar ta shafi wadda zinarta ta bayyana a fili a cikin jama’a ne, ba wacce abin ya auku gare ta a ɓoye ba tare da sanin kowa ba. Hadisin Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya nuna hakan a inda ya ce:

لاَ يَنْكِحُ الزَّانِى الْمَجْلُودُ إِلاَّ مِثْلَهُ

Mazinacin da aka yi masa bulala ba ya aure sai da irinsa. (Sahih Abi-Daawud: 1807).

Wanda aka yi masa bulala kuwa shi ne wanda laifin zinarsa ya bayyana.

Nasiha dai a gare ta da sauran matasa irinki ita ce:

1. Ku daina saurin yanke hukunci a kan al’amura muhimmai a cikin rayuwa ba tare da kusantar malamai masana ba.

2. Maganganun malamai a wurin wa’azi da waɗanda ake rubuta wa a cikin wasu littaffai galibi suna buƙatar ƙarin haske a kansu, musamman idan sun shafi wani muhimmin abu mai girma.

3. Bai halatta ta sanar da mijinta ko wani daban labarin wannan abin da ta aikata ba. Allaah ba ya son haka.

لَا يُحِبُّ اللَّهُ الْجَهْرَ بِال سُّوءِ مِنَ الْقَوْلِ إِلَّا مَنْ ظُلِمَ ۚ وَكَانَ اللَّهُ سَمِيعًا عَلِيمًا ٨٤١۝

Allah bã Ya son bayyanãwa da mũnãna daga magana fãce ga wanda aka zãlunta. Kuma Allah Yã kasance Mai ji, Masani (Surah An-Nisaa’i: 148).

Don haka, dai abin da ke a kan ta a yanzu sai ta yawaita tuba da istighfari da kyautata ayyukan alheri, na nafilar sallah da sadaka da azumi a bayan farilloli, domin fatan Allaah ya kankare mata zunuban laifukan da suka gabata. Kuma ta yawaita addu’o’i da azkaar domin neman samun kariya da ƙarin tabbata a kan tafarkin shiriya har zuwa ƙarshen rayuwa.

Allaah ya gafarta mana kura-kuranmu, ya ƙara mana fahimta a cikin addininmu.

WALLAHU A'ALAM

Sheikh Muhammad Abdullaah Asslafiy

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments