Amadu Na Funtua Ya Chika Shekaru 50 Chif A Sarautar Sa'in Katsina
A ranar 16th September a shekarar 1973 ne aka naɗa Alhaji Amadu Na Funtua a matsayin Sa'in Katsina, inda jiya 16th, ga watan Satumba 2023. ya cika shekaru 50 Cif a bisa wannan Sarauta ta Sa'in Katsina.
marigayi sarkin Katsina Alhaji Dr. Usman Nagogo, shi ne wanda ya naɗa Alhaji Amadu na Funtua a shekarar 1973 a matsayin Sa'in Katsina.
Sa'in Katsina Amadu na Funtua, a yanzu yana da shekaru 94 a duniya wanda yana daga chikin mutanen da suka yi tsawon rai cikin waɗanda aka baiwa sarauta a tun a wancen lokacin.
Muna Addu'ar Allah ya ƙara mashi lafiya da nisan ƙwana masu Albarka.
0 Comments
Post your comment or ask a question.