Namu Ba Irin Nasu Ba Ne - Ranar Hausa Ta Duniya

    1. Manta da zamani ɗau al'ada,
    In ta yi Kyau riƙe kama ibada,
    In Kai hakan ba ka zam wa wa ba.

    2. Farko da kaliƙina zan fara,
    Sunanshi na kira rabbu Tabara,
    Zan nai baituka ciki ba kushe ba.

    3. Na yo sallama wurin nawa Habibi,
    Na sa da Ali har ma da sahabi,
    Sun bi shi sam ba sui masa zamba ba.

    4. ‘Yan baituka na rero kan tsari,
    Don tsokaci gami har da kirari,
    Sai ku ji ni ban zo ni da wasa ba.

    5. Al'adunmu masu kyau sam ba muni,
    Duka za ku ji su sai duk ku biyo ni,
    In nai kuskure ku ce ba dai dai ba.
               HARSHE
    6. Harshenmu ya zamanto kan tsari,
    Wannan ne ya nakan rere kirari,
    Harshen Hausa yai fice ba kuri ba.

    7. Duk Harsunan ga in kai lissafi,
    Can ƙololuwa wajen ‘yan lissafi,
    Harshen Hausa ya wuce ko ba su so ba.

    8. Harshen Hausa ya zamonto mai kaifi,
    Duk tsarin zubinsa ya zam mai ƙarfi,
    Dukkan harsuna ba sa mana kushe ba.

    9. Ga a halinmu bamu gudun baƙunta ,
    In ka zo cikinmu ka bar baƙunta,
    Da kai da ɗan gida ba a bambanta ba.
                 TUFAFI
    10. In kun gan ni nan da kyau za ku fahimta,
    Don nai shiga da kyau ba ƙasaita,
    Haka nan duk shigar Bahaushe ba wai ba.

    11. Wandona nasa da Hulata Zanna,
    Wata ran Dara,Damanga a kayana,
    Kayanmu ne da ban ga ya mai shi ba.

    12. Alkyabba gare mu Riga ga Taggo,
    Ga Rawani mu sa mun zamto bango,
    Dukkanin shigar mu Banga kamar mu ba.

    13. Watta ran na sanya aikin nan kufta,
    Kowa ya gammu ya san da akwai tsafta,
    Na san na yi kyau bakwa kushe ba.

    14. Mata ke sanya Kallabi har Murjani,
    Wa za ya bar su yaɗɗau Zamani,
    Kayan ɗan gida ba ya zam ya na baƙo ba.

    15. Su sa Zani su Rataya sarƙa, 
    Buje su sa Ɗankunnen sarƙar,
    Kwalli Ido ya haska ba muni ba.

    16. Ga Warwaro ku sanya ‘yammata,
     Jiggida ku sa ta ko din ƙasaita,
    Na san sam ba za ku ce mini a a ba.
                  KAYAN AIKIN GIDA 
    17. In Har ka shigo gida ga wasu kaya,
    Zan ambace su duk sai ku ƙidaya,
    Dukkanin gida ba za a rasa sam ba.

    18. Akushi akwai shi har ma ɗan Turmi,
    Faifai,Rariya,Cibi a gidan Momi
    Mara,Wuƙa da Kumbo Ɗakin baaba.

    19. Ga Ludayi da Murhu har Tasa,
    Tulu gami da Randa duk nasa,
    Jallo kusa da salka ba wai ba.

    20. Fanteka,kwalla kai harma ƙwarya,
    Garwa Tukunya kai sa da Taɓarya,
    M Sanyo mafici don ban manta shi ba
    21. Ga muciya ire ga A ci balbal ma,
    Kasko,nasaa kusa har Tabarma.
    Dukkanin gida ba ka rasa wannan ba.

    22. Akwai  Ragaya ciki in kun Tambaya,
    Ga kasko,shantali, Kabet kun dai jiya
    Ga Tangaran da mai ros ban bar su ba.

    23. Ga gadon kara ce harda kwatarniya,
    Ga Tabarma ga fili huce gajjiya,
    Kun dai ji su yan uwa baku manta ba.
              WASANNI 
    24. Wasanninmu ga waɗansun su ku ji ni,
    Zan ambato su Ba wani ƙaulani,
    Duk sai ku ji su banzo wasa ba. 

    25. Mui kokowa da langa da Tashenmu,
    Ga ‘yar tsana wurin yammatanmu,
    Ko sui gaɗa, ɗan kurege ba su yo ba.

    26. Haka nan Tuwan ƙasa mu ba mu yo ba,
    Carman dudu shi ma ba mu yo ba,
    Sabis mun yi mun kuma ba wai ba.
           TSARIN MULKI
    27. Masarautun Hausa in har kun bi ni,
    Zan zayyano su ban da na zamani,
    Daura ga Kano Hadeja gari babba.


    28. Zazzau na ciki da Gobir kun sansu,
    'ya'yan Dikko Katsinawa gaishe su,
    Sannan sai Rano gari ba daji ba.

    29. Sarki shugaba wurinmu ya zam farko,
    Sai Hakimai waɗansun su na ɗan dakko,
    Sarkin fada na ciki ban fidda ba.

    30. Barde jarumi gwani a fagen yaƙi,
    Ga ma'aji ku ji ni har Sarkin Yaƙi,
    Wambai na ciki Galadima babba.

    31. Ajiya na ciki waziri kun ji su,
    Sannan garkuwa Turaki na faɗe su,
    Ku ji dai da kyau akwai wasu ba su ba,

    32. Ga Sardauna har ga mi da Uban doma,
    Sarkin shanu na faɗi kuma ga Jarma,
    Dallatu har da shi ban mance ba.

    33. Ga Ganuwa Maji ɗaɗi kun jiya,
    Ga matawalle Ɗan’amar duk dai na biya,
    Ga Santuraki,Madaki kun ji ba.

    34. Ga nan Dawaki harda Tafidanmu ma,
    Ga Ɗanadala Sannan ga Darma.
    Sa'i sai Turaki duk ban gajiya ba.

    35. Ga mai Unguwa da sauran fadawa,
    Ga Daggaci da su aka tsarawa,
    In nai kuskure ku ce ba haka ne ba.
           SANA’O’I 
    36. Sana'o’i na Hausa zan lissafa su,
    Ƙira na ciki da fawa kun ji su,
    Saƙa mun ƙware ba ai mana gori ba.


    37. Kana sassaƙa muna yi tun can da,
    Ga Maruna Rini suke yau har Shadda,
    Wanzamai akwai su sam ban shirme ba.

    38. Noma ne na duƙe tsohon cinikinmu,
    Ba mai gudun shi in dai ya san mu,
    Tushen Azrki ina wani ba shi ba.

    39. Kiwo ma munai kaɗan ba sosai ba,
    Dangin Yan Fulani su ke yin Babba,
    Don namu bai wuce na ƙananu ba.

    40. To kun dai ji yan ƙadan na lissafa su,
    Fata nake ga dangi ku kiyaye su,
    In mun bar su mun yi wauta ba wai ba.
                BUKUKUWA 
    41. Dukkanin bikinmu ba wani mai muni,
    Domin sun wuce bikin duk zamani,
    Ga su ku ji ni don ba zan manta ba.

    42. Aure bikinmu ba wani mai shakku,
    Sauƙi cikinsa ba wani mai shakku,
    Da za a yi shi kwa ce ban ƙarya ba.

    43. Ga nan biki na Sallah duk namu,
    Haka nan Haihuwa idan mun samu,
    Murna mun ka yi abin ba sabun ba.
           ABINCI
    44. zan kulle baitukan da abincinmu,
    Hoce,Ɓula da Dambu a gidanmu,
    Wainar Hatsi, Kunu bance Kwai ba.

    45. Rambo nasa nasa da koko,Tafasa ma,
    Ga zogale,miyar kuka ga Rama.
    ‘Yar tsala sam ba ka ce Waina ba.


    46. Ga nan ma gyaɗa da ma masara acca,
    Ga dawa hatsi da Ridi ba caca,
    Wake daddawar miya kai mun caɓa.

    47. Nan zan tsaya ina daɗa gauishe ku,
    Kuma can ga rai akwai tsananin Son ku,
    Wanda ya sam wuri ba za ya gushe ba.

    48. Waƙen na sani akwai ban-mamaki,
    Ko da cikinsa kuskure nai jan aiki,
    kui min hakkuri ba zan ƙara ba.

    49. Ni ne naku Ɗalibi mai ƙaunarku,
    Ni ne nan Aminu ɗanɗa a wurinku.
    Jikan Jauro ɗa ga Sani ba wai ba.

    50. Allajjiƙan su Allah ya Rahamshe su,
    Har ma da ni da ku kan mu bi bayansu,
    ƙarshenmu yai yi kyau ba ai kushe ba.
    Kafar Intanet Ɗin Da Za Ku Samu Dubbannin Rubuce-Rubuce Game Harshe Da Al'ada Da Adabin Hausawa

    ALHAMDULILLAH
    Daga Alƙalamin Aminu Sani Uba (Abu Isah Asshankiɗi)
    08162293321
    aminusaniuba229@gmail.com

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.