Ticker

6/recent/ticker-posts

Makada Abu Dan Kurma Maru: Wakar World Bankin Duniya

Allahu Akbar!!! Ya yi wannan Waƙar a cikin ƙarshe - ƙarshen shekarun 1970s  lokacin da ta hanyar Bankin Duniya (World Bank assisted Program) aka buɗe wani Shirin Inganta Ayyukan Gona da Raya Karkara da aka kira da (Gusau Agricultural Development Project, G. A. D. P) da Hedikwata a Gusau.
Cikin ayyukan wannan hukuma akwai samar da kayan aikin noma na Zamani da horad da Ma'aikatan gona na zamani da bayar da bashin kuɗi da kayan noma na zamani ga manoma da wayar da kan su akan dubarun noma na zamani da samar da hanyoyin karkara na ɓurji da inganta kiyon dabbobi da samar da tsabtataccen ruwan sha ga al'ummar karkara da sauran su. A lokacin dai ne wannan hukuma ta yi gidaje ko cibiyoyin bunƙasa ayyukan gona a garuruwa da Ƙauyuka daban daban musamman a yankin Sakkwato ta Gabas/Yankin Zamfara kenan. A waɗannan cibiyoyin ne hukumar ke kai takin zamani da iraruwan shuka ingantattu da Malaman Gona masu koyad da hanyoyin noma irin na zamani. Ta hanyar wannan hukumar ne akasarin garuruwa da Ƙauyukan da ta buɗa irin waɗan nan cibiyoyin suka samu hanyoyin motar da kafin bayyanar hukumar babu su, misali titin da ya tashi daga garin Ƙaura Namoda zuwa Birnin Magaji mai tsawon kilomita 36 da ya  tashi daga bayan babbar Tashar Motar Ƙaura Namoda babu shi, wannan hukumar ce ta ƙirƙire shi a lokacin. Shi ne mu ke kira Godaben/Titin Furojet(Project) daga sunan hukumar, (Gusau Agricultural Development Project, wanda Makaɗa Abu Ɗan Kurma ya kira da Woldu Bankin Duniya Furojet ita ag gaba a amshi wannan Waƙar). Kuma shi ne dai aka ci gaba da amfani da shi har ya zuwa cikin shekarun 2000s, lokacin mulkin Gwamna Alhaji Mahmuda Aliyu Shinkafi (Dallatun Zamfara) da Gwamnatin Alhaji Abdulaziz Yari Abubakar (Shattiman Zamfara) a Jihar Zamfara suka shimfida mashi kwalta.

Sannu a hankali wannan Shirin ya samu karɓuwa ga al'umma har ma daga baya da ya kai wa'adin karewar shi sai Gwamnatin Tsohuwar Jihar Sakkwato (Sokoto, Kebbi, Zamfara) ta mayar da shi a matsayin Shirin ta da canjin suna zuwa( Sokoto Agricultural  and Rural Development Project, S. A. D. P) ya kuma shafi kowane sashe na Jihar. An sake canza/canja ma shirin suna ya zuwa (Sokoto Agricultural and Rural Development Authority, S. A R. D. A) sunan da yake amfani da shi ya zuwa yau.

Makaɗa Abu Ɗan Kurma Maru asalin su daga gidan Kiɗa na su Makaɗa Ibrahim Gurso mai Kotso Talata Mafara ne. Wani Sarki  da aka naɗa a Maru(Banagan Maru) ne ya tafi da Mahaifin Abu Ɗan Kurma daga Talata Mafara, da amincewar wan shi /yayan shi, Makaɗa Ibrahim Gurso zuwa Maru domin ya zamo Makaɗin shi. Wannan ne dalilin haihuwa da zaman Abu Ɗan Kurma a garin Maru ya zuwa yau. Bayan rasuwar Mahaifin shi a nan garin Maru, Abu Ɗan Kurma ya zamo Halifan shi. Ya yi Kiɗan Sarauta da na Noma kuma shi ne babban Makaɗin Mutanen Kwatarkwashi dake tu'ammali da Tsuntsun nan da ake kira Maiki. Ya yi masu Kiɗan da ake kira "Baura" da abun Kiɗan shi da ake kira Kuwaru. Bayan rasuwar Abu Ɗan Kurma a halin yanzu Usman ne Halifan shi (duk da yake ban san takamaiman alaƙar su ba, ma'ana ko Ƙanen shi ne ko kuma ɗan shi ne). Allah ya kyauta makwanci, amin.
Daga Taskar

Malam Ibrahim Muhammad Birnin Magaji
Ɗanmadamin Birnin Magaji
Imel: birninbagaji4040@gmail.com
Lambar Waya: 08149388452, 08027484815 

Post a Comment

0 Comments