Yarinya: Girgije-girgije na zo gare ka,
Girgije: ‘Yar nan na ba ki me?
Yarinya: Na zo ka ba ni ruwa,
Girgije: Ruwan ki kai wa wa?
Yarinya: Ruwan na ba ciyawa,
Girgije: Ciyawar ta ba ki me?
Yarinya: Ciyawa ta ba ni ganye,
Girgije: Ganye ki kai wa wa?
Yarinya: Ganye na kai wa Nagge,
Girgije: Naggen ta ba ki me?
Yarinya: Nagge ta ba ni kashi,
Girgije: Kashin ki kai wa wa?
Yarinya: Kashi na kai wa Ɓaure,
Girgije: Ɓaure ya ba ki me?
Yarinya: Ɓaure ya ba ni ‘ya’ya,
Girgije: ‘Ya’yan ki kai wa wa?
Yarinya: ‘Ya’ya na kai wa Inna,
Girgije: Inna ta ba ki me?
Yarinya: Innar ta ba ni zanna,
Girgije: Zanna ki je ina?
Yarinya: Zanna na je ni wasa, tsara duka sun tafi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.