Ticker

6/recent/ticker-posts

Mahaifiyata

 Mahaifiyata

Uwata mai Juriya

Mai ba ni kulawa da soyayya

Wacce ta ba ni dukan ta sanda ban iya

Duk wani bashin bukatuna tana biya

Toh Mama, ga sako daga danki

Wanda kika yi wa komai har da wanki

Wanka, shanya, duk a cikin farin ciki

Don shi ma ya zama wani kamar sarki

 

Umma, Kiyi min komai a rayuwa

A kaina kin sha wahala mara masaltuwa

Tsangwama har da zagi daga 'yan uwa

Gaskia, a rayuwa babu wata kamar uwa

 

Ammi, ke daya ce

Wacce ta wuce duk kwatance

Ke haske ce a duhu amma fa a takaice

Ke ce kadai mai ban horo a sirrance

 

Toh yau yabonki zan yi

Da kalamai masu sanyi

Dadi irin su Sweet Mum na ya yi

Kuma fa'ida da ma'ana za su yi

 

Umma, 'you are my world' na ce da Turanci

I could have said things amma na yi sassauci

Don kin wuce duk wani suna har da ta Larabci

Mama, kin yi min, toh ga wata wake mai adalci

 

M.I Bagudu

Ink of Musteemah

23 July, 2023

Post a Comment

0 Comments