Hukuncin Jinkirta Sallah

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Malam barka da assuba

    Dafatan malam kana lafiya

    Malam tambayace, malam ni ne na Bakunci wani wuri sai kwana ya saman awurin malam, koda nitashi daga bacci sai naji suturata da sanyi koda naduba sai naga Ashe mafarki ne na yi malam kuma lokacin sallah ya yi, sai banyi sallarba Dan naga suturata tabace kuma banda wata da zansa malam, shi ya sa banyi taimama ba, na yi sallah, sai Na jikirta sallar sai da nakoma gida. menene cikakyan bayani a kan wannan mastalar, Malam nagode sosai da abin da kakemin.

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa alaikumus salam wa rahmatullah.

    Tabbas yadda kayi din akwai kuskure ciki. Ba laifi ba ne idan ka tsinci kanka a irin wannan yana yin ka nemi ruwan da zai ishe ka yin wankan janabah, kaje kayi wankan sannan ka wanke

    daidai wajen da maniyyin ya taɓa a jikin tufafinka sannan kaje kayi sallarka a kan lokaci.

    Koda babu damar yin wankan awajen saboda rashin ruwa ko faruwar wata larurar, to bai

    halatta ka bar sallah har lokacinta ya wuce ba.

    Kuma idan har kaga lokacin sallar zai fita, to ya halatta gareka kayi taimamah kayi sallah.

    Shaikh Abdurrahman Al Akhdhariy yace "Wanda

    ya jinkirta sallah har lokacinta ya suce, to lallai akwai laifi a kansa mai girma".

    WALLAHU A'ALAM.

    Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://chat.whatsapp.com/IerSx3AH0ZSJyHIuIYfƙds

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.