Na Mai Ango a Birnin Magaji ya fara Dambe ya na ɗan matashin shi a farko farkon 1980s. Ƙauyen su da ake kira Riyoji ya na yamma da garin Birnin Magaji duk da yake suna cikin Masarautar Zurmi ne.
Riyoji garin Madambata ne da ke da asirin Dambe sosai. Nan aka yi Aikau da Jijji da Issau da Olo da sauran su. Na Mai Ango wanda Ɗanbalade ke kira Ɗan Ango a cikin Waƙar da ya yi mashi ya taso a matsayin ɗan dambe marar fargaba da wayon dambe da kuma neman asiri sosai. Allah ya jiƙan shi.
Daga Taskar
Malam Ibrahim Muhammad Birnin Magaji
0 Comments
Post your comment or ask a question.