Ticker

6/recent/ticker-posts

Ɗan Dambe Alhaji Abubakar Yarkofoji (Shagon Bakura/Shagon Mafara)

Ɗan Dambe Alhaji Abubakar Yarkofoji (Shagon Bakura/Shagon Mafara)

"Wandara ko ga girbin gero,
Bara- bara ta na hana wake" 

Inji Makaɗa Muhammadu Bawa Ɗan Anace 'Yar Tsakkuwa, Gandi, Sakkwato a Waƙarsa ta Ɗan Dambe Alhaji Abubakar Yarkofoji da aka fi sani da Shagon Bakura /Shagon Mafara. Allah ya kyauta makwanci, amin.

Bara-Bara na nufin duk wani ciyayi/wata ciyawa ko haki irin su Yaryad'i /Yalyad'i dake zagaye da amfanin gona wanda idan aka girbe amfanin gonar zasu iya hana sauran amfanin gonar zalawa /girma.

Ya na baiwa Shago shawara ne cewa idan ya zo wajen dambe kada ya bar kowane irin ɗan dambe tsaye, ya naɗe hannu su yi domin barin waɗan su komi Ƙanƙantar su zai sa irin su su dinga hura hanci suna ganin kamar saboda ya na tsoron su ne.

Daga Taskar

Malam Ibrahim Muhammad Birnin Magaji
Ɗanmadamin Birnin Magaji
Imel: birninbagaji4040@gmail.com
Lambar Waya: 08149388452, 08027484815 

Post a Comment

0 Comments