Ticker

6/recent/ticker-posts

Amali Kande - Daga Littafin WAƘOƘIN HAUSA NA GARGAJIYA

Citation: Gobir, Y.A. & Sani, A-U. (2021). Waƙoƙin Hausa Na Gargajiya. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-0-01.

Amali Kande

Bayarwa: Wayyo inna wayyo inna!

Amshi: Amali Kande.

 

Bayarwa: Ban isa ba an ce a kai ni,

Amshi: Amali Kande.

 

Bayarwa: Kowa ya kai ni ya kai kunama,

Amshi: Amali Kande.

 

Bayarwa: Ban isa ba an ce a kai ni,

Amshi: Amali Kande.

 

Bayarwa: Kowa ya kai ni ya kai bala’i,

Amshi: Amali Kande.

 

Bayarwa: Ban isa ba an ce a kai ni,

Amshi: Amali Kande.

 

Bayarwa: Kowa ya kai ni ya kai jafa’i,

Amshi: Amali Kande.

 

Bayarwa: Ban isa ba an ce a kai ni,

Amshi: Amali Kande.

 

Bayarwa: To an kai ɗan maciji gidansa,

Amshi: Amali Kande.

 

Bayarwa: Wayyo inna wayyo inna!

Amshi: Amali Kande.

 

Bayarwa: Ban isa ba an ce a kai ni,

Amshi: Amali Kande.

WAƘOƘIN HAUSA NA GARGAJIYA

Post a Comment

0 Comments