Bayarwa: Ɗan tuɓulle, tuɓulle,
Amshi: To!
Bayarwa: Ga almajiri da ƙaho,
Amshi: To!
Bayarwa: Ga almajiri da ƙaho uku,
Amshi: To!
Bayarwa: Guda na shukar gero,
Amshi: To!
Bayarwa: Guda na shukar dawa,
Amshi: To!
Bayarwa: Guda na shukar marar tuwo a saka a baki da daɗi,
Amshi: To!
Bayarwa: Sai ni malam Audu
Amshi: To!
Bayarwa: Naj je barar alkali,
Amshi: To!
Bayarwa: Ciwon ciki ya riƙe ni,
Amshi: To!
Bayarwa: Daga mai jiƙa mini kanwa,
Amshi: To!
Bayarwa: Sai mai jiƙa min manda,
Amshi: To!
Bayarwa: Ba magani ke nan ba,
Amshi: To!
Bayarwa: A samu farare-farare,
Amshi: To!
Bayarwa: A samu fararen mata,
Amshi: To!
Bayarwa: Su ɗebo nonon shanu,
Amshi: To!
Bayarwa: Su likkiɗa mini damu,
Amshi: To!
Bayarwa: In karkace hulata,
Amshi: To!
Bayarwa: In rangaɗa ma cikina,
Amshi: To!
Bayarwa: Ciwon ciki ya yi sauƙi,
Amshi: To!
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.