Ticker

6/recent/ticker-posts

Godiyallare

6.82 Goɗiyallare

Wannan wasan mata ne da ke buƙatar yara da dama domin gudanar da shi. Kimanin yara goma sha biyar ne zuwa sama da haka ke gudanar da wannan wasa. Wasan yana tafiya da waƙa, amma ba ya buƙatar amfani da kayan aiki yayin gudanar da shi.

6.82.1 Wuri Da Lokacin Wasa

i. An fi gudanar da wannan wasa a dandali da kuma gidajen Bukukuwan aure.

ii. Akan yi wannan wasa da dare ko da yamma a tarukan aure.

6.82.2 Yadda Ake Wasa

Yara sukan yi da’ira. Daga nan sai mai wasa ta fito tsakiyarsu. Za ta fara waƙa tare da zazzagayawa. Sauran ‘yan wasa za su riƙa amshi tare da tafi. Ga yadda waƙar take:

Bayarwa: Goɗiyallare goɗi balan gutsire,

Amshi: Goɗiya.

 

Bayarwa: Wadda ta kai ana mata sannu-sannu,

Amshi: Goɗiya.

 

Bayarwa: Wadda ba ta kai ba ta ci kuɗin samari,

Amshi: Goɗiya.

 

Bayarwa: Uwar mijina,

Amshi: Goɗiya.

 

Bayarwa: Tana kira na,

Amshi: Goɗiya.

 

Bayarwa: Me za ta ba ni?

Amshi: Goɗiya.

 

Bayarwa: Fura da nono,

Amshi: Goɗiya.

 

Bayarwa: Ki bar abinci ɗanki yana siya min,

Amshi: Goɗiya.

 

Bayarwa/Amshi: Goɗiya, goɗiya, goɗiya, goɗiya …

A wannan gaɓa, dukkanin ‘yan wasa za su taka rawa. Da zarar an ƙare, ta tsakiya za ta fita. Wata daban kuma za ta dawo tsakiya.

6.82.3 Tsokaci

Wannan wasa hanya ce ta motsa jiki da samar da nishaɗi ga yara. Sannan waƙar wasan na ɗauke da baƙar magana zuwa ga uwar miji. Wannan hoto ne da ke nuni a kaikaice zuwa ga yadda uwar miji take a tunanin mata.

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments