Citation: Bunguɗu, U.H. (2021). Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar Hausa. Ahmadu Bello University Press Limited.
Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:
Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369
5.2 Rawa
Jagora: Ni daudun bara ɗan galadima bara.
Amshi: To.
Jagora: Na saba
bara bani kwana ban ciba.
Amshi: To.
Jagora: Kun ga
rawar tuwo kun ga tattakin miya.
Amshi: To.
(Daudun Bara)
A ɗa na uku na wannan waƙa an nuna ana dafsa rawa sosai yayin da Almajiri ke rea waƙar. A waƙoƙin sauran mabarata ma na baka ana haɗa su da rawa a lokacin rera su. Misali waƙar “Madogara Annabi”
Madogara Annabi.
Annabi dai Annabi.
Babu kamar Annabi.
Madogara Annabi.
Way yi kamar Annabi.
Ku ba ni don Annabi.
Annabi jikan Nuhu.
(Madogara Annabi)
Wannan waƙa mabarata manya ne suka fi amfani da ita, kamar guragu da kutare da makafi
waɗanda ba su
hardace wani abu daga rubutattun waƙoƙin wa’azi ko madahu ba. Ana rera wannan waƙa da ƙarfi sosai
kamar dai mai rera ta ɗin ba
ya cikin hankalinsa. Haka ma ana kaɗa kai da ƙarfi da wasu
sassan jiki kamar kafaɗa a
sadda ake rera ta. Waƙar mutum ɗaya ke rera ta, wato ba a cikin
taro ba.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.