Citation: Bunguɗu, U.H. (2021). Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar Hausa. Ahmadu Bello University Press Limited.
Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:
Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369
4.7.4 Mu Gode Allahu Mai Rahama: Ta Malam Zainu Zubairu Bunguɗu
1. Mu gode Allahu Mai Rahama,
Rahamarsa bai
manta kowa ba.
2. Tsira ta dawwama ga manzonsa,
Dikoshi ba’a keɓe kowa ba,
3. Zuwansa yazan zuwan rahama,
Garemu ba ko da
nisa ba.
4. Alaye Sahabbai Iyalansa,
Zuriyarsa ban zaɓe kowa ba.
Kowane rukuni na mabarata yana amfani da rubutattun waƙoƙi gwargwadon hali, sai dai makafi sun fi amfani da su. Kusan kowane makaho ya riƙe wani ɗan yanki na wata rubutattar waƙa ta wa’azi ko madahu ko wani fanni na addini. Wasu suna hardace dukan waƙa wasu kuma wani sashe cikinta suke hardacewa.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.