Ticker

6/recent/ticker-posts

4.7.2 Waƙar Infiraji

 

Citation: Bunguɗu, U.H. (2021). Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar HausaAhmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar Hausa

4.7.2 Waƙar Infiraji

 1. Ya ilahil Arshi ba ni,

 Hankali da yawan bayani,

 ‘Yan’uwa suka tambaye ni,

 In ma waƙa tamu sani,

 Gyara ba zai kamar kashi ba.

1.                  Gargaɗi mai bada tsaro,

 Nai nufi da hani da horo,

 Duk maso rahama ya taro,

 Hankali babba da yaro,

 Sai wanda ba za shi lahira ba.

 (Aliyu Namangi: Imfiraji ta biyu)

Wannan waƙa ta Imfiraji ita ma mashahuriya ce ƙwarai a bakunan mabarata musamman makahi. Ita ma ba domin bara Malam Namangi ya wallafa ta ba, ya wallafa ta ne domin wa’azi da bege, amma mabarata suka mayar da ita abin yin bara. Haka kuma suna da yawa tun daga ta Ɗaya har zuwa ta tara, kuma kowace ɗaya daga cikinsu mabarata na amfani da ita wajen bara.

Akwai kuma wasu waƙoƙin waɗanda mabaratan ke amfani da su wajen bara waɗanda wasu mutanen suka rubuta su domin wani dalilin kamar wa’azi ko madahu da sauran irinsu. misali:


Post a Comment

0 Comments