Citation: Bunguɗu, U.H. (2021). Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar Hausa. Ahmadu Bello University Press Limited.
Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:
Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369
4.6.1.3 Maula Ta Sidi
Jagora : Maula ta Sidi maula ta Balarabe.
Amshi : Maula.
Jagora : Babban gida da daɗin bara yake.
Amshi : Maula.
Jagora : Waccan ta ba ka waccan ta daɗa maka.
Amshi : Maula.
Jagora : Waccan ta ɗauki kere na shirin bugu.
Amshi : Maula.
Jagora : In ba ki ba ni shafa mani lahiya.
Amshi : Maula.
Jagora : In kin buge
ni wallahi kina biya.
Amshi : Maula.
(Maula)
Wannan waƙar Gardawa suka fi amfani da ita wajen bara. Wato mabarata masu neman ilmi
waɗanda suke sun
wuce almajirci. Masu wannan waƙa ba su shiga
cikin gidaje a lokacin da suke baran kamar yadda Almajirai ke yi, saboda su
manya ne. A garkar gida suke tsayawa suna baransu ana aiko yara suna kawo masu
sadaka. Ita ma a cikin taro ake rera ta, wani na bayarwa saura na amsawa. Mafi
yawa ba kulium Gardawa ke fita wajen bara ba, sukan keɓe daren Jum’a da safiyarta domin yin bara. Wato ke nan
tsarin baran nasu sati-sati ne.
0 Comments
Post your comment or ask a question.