Ticker

6/recent/ticker-posts

4.5.1.1.3 Laƙada Raliyallahu

Citation: Bunguɗu, U.H. (2021). Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar HausaAhmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar Hausa 

4.5.1.1.3 Laƙada Raliyallahu

Jagora : Laƙada raliyallahu anal muminina[1],

 Amshi: To

Jagora : Angal lahu angaruhin mu’asha[2],

Amshi: To

Jagora : An aiko mu inda malam mu gan shi,

Amshi: To

Jagora : Ga shi biki[3] gare shi mi zamu ba shi,

Amshi: To

 Jagora : Kai ka mukai mu samu lada cikakka.

Amshi : To

Waɗannan misalai ne kawai aka samo na ire-iren waɗannan waƙoƙin, amma dai akwai cikakkunsu a babi na takwas.



[1]  Wannan wata aya ta goma sha bakwai ce a farkon hijifi na tara a cikin wata sura da ake kira suratil fathi.

[2]  Wannan soki-burutsu ne ba karatu ba ne.

[3]  Don su nuna muhimmancin malaminsu.


Post a Comment

0 Comments