Ticker

6/recent/ticker-posts

Gamuwak ku da Shehu na Kaulaha... Ehiinn...

 
Gamuwak ku da Shehu na Kaulaha... Ehiinn...

"Gamuwak ku da Shehu na Kaulaha... Ehiinn..." Inji Makaɗa Salihu Alasan Jankiɗi Rawayya a cikin Waƙarshi mai amshi  'Abdullahi shiggaban sahu, Imamuddini Dabon Kano' wadda ya yi ma Marigayi Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Abdullahi Bayero. A wannan hoto ana iya ganin Marigayi Mai Martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi I ɗan Sarkin Kano Abdullahi Bayero ɗan Sarkin Kano Abbas ɗan Sarkin Kano Abdullahi Maje Karofi ɗan Sarkin Kano Malam Ibrahim Dabo na farko daga gefen dama tare da Sheikh Ibrahim Nyass a tsakiya da kuma Marigayi Mai girma Firimiyan Jihar Arewa, Alhaji Sir Ahmadu Bello GCON KBE, Sardaunan Sakkwato a wata haɗuwa a wani lokaci da ya gabata. Allah ya jiƙan magabatanmu, ya sa mu wanye lafiya mu cika da kyau da imani, amin.

Daga Taskar

Malam Ibrahim Muhammad Birnin Magaji
Ɗanmadamin Birnin Magaji
Imel: birninbagaji4040@gmail.com
Lambar Waya: 08149388452, 08027484815

Post a Comment

0 Comments