Ticker

6/recent/ticker-posts

Diya Maza Daukar Farko Baba

Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA). Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

Magaji PPRO,

Magaji Musa ɗan majiya baba baba PPRO,

Uban maza ɗiban Garko,

Kama a nan har ma Koko,

Ɗiya maza suke sakko,

Masu nunin fifiko,

Uban maza fa yana dako.

 

Baba tsarin taurari,

Na gano ka sahun nari,

Bakin wuta na kashe sharri,

Kasanta doka mai tsari,

Magaji ka zamto khairi,

Magaji ko kuma annuri,

Tsanin hawa kan alkhairi,

Allah ya sada mu khairi.

 

Ubangijina Jabbaru

Abin yabona Sattaru

Ina ta goden alkhairu,

Ka sa na zamto mashakuru,

Saboda dubban alkhairu,

Na yi tsani da mubarru,

Mubasshirun kana naziru,

Nurulhuda sirrul sirru.

 

Ina yabo gun Baballo,

Cikin zumuɗi da hakilo,

Yabon ya janyo 'yan kallo,

Kamar ana wasan ƙwallo,

Waɗansu don nuna hakilo,

Suna ta rauwa mai lilo,

Waɗansu don shauƙin kallo,

Suna dara ya na ɗan dalo.

 

Magaji ka biya allonka,

A yanzu ka iya allonka,

A yanzu hadda ke binka,

A gobe satu ke kanka,

A ɓangaren gogewarka,

Spacial duty naka,

Hagun zuwa ma damanka,

Magaji sai dai sambarka.

 

Abin da ke ban mamaki,

Idan kana sautin baki,

Kasantuwa taka kakaki,

Na rundinar masu kulaki,

Batunka na samin shauƙi,

A radio nika mamaki,

Da an ji an san ba sauƙi,

Su baba dodon shawaraki.

 

Abin da ke mani tasiri,

Da ka yi saƙon alkhairi,

Mutan gari ba sa ruri,

Majorati ba su burari,

Suna ta goden alkhairi,

Saboda ikon Jabbari,

Ya ba ka baiwa da sururi,

Allah ya kare duka sharri.

 

Idan Magaji yak kuta,

Ka ce wuya kashin ƙota,

Makangara za su wuyata,

Da masu halayyar wauta,

A nan sahu zai daidaita,

Na masu halayyar wauta,

Magaji ɗan barni in huta,

Kukan wuya kashin ƙota.

 

 

Kwamantaka ko alharga,

Magaji mai horon tsabga,

Ga ‘yan daba koko ayaga,

Waɗanda ke ɗaukar zuga,

Wuya tana filin daga,

Da masu wauta sun shirga,

Magaji mai siga-siga,

Da lalama ko kuma jibga.

 

A randa naj jeni ziyara baba a ofishin Fifi'ar'o,

Da ni da Rabi’u mai ƙara baba na kai shi gun fifi'ar'o,

Bayan da mun gama kai ƙara baba na kalli ofis fi'ar'o,

Ta ko’ina kambun girma nake gani na baba ne fifi'ar'o,

A nan na gano kakin nan baba ba duk mutum ke fi'ar'o.

 

Aminu ALA mai waƙa baba yake ta waƙar cancanta,

Na tashi in yaba halinka baba irin yabo don cancanta,

In kambama ka a sashenka baba da ka iya kuma ka huta,

Saboda ka biye allonka baba me za ya hanneka ka huta,

Aiki ka san bim umarni baba da an riƙe shi da an huta.

Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

Post a Comment

0 Comments