Wannan ɗaya ce daga cikin jerin waƙoƙin da aka yi wa Alhaji Aliyu Magatakarda Wamakko (ALU). A hasashen manazartan Amsoshi, ALU shi ne gwamnan ƙasar Hausa da ya fi kowane gwamna yawan waƙoƙi da aka yi masa.
JAGORA: Aliyu gwamnan SakkwatoRiƙa da ƙarfin Allah,
Yara: Aliyu gwamnan
Sakkwato
Riƙa da ƙarfin Allah,
Aliyu gwamnan Sakkwato.
Jagora: Ɗan Barade jikan Umaru
Yara: Aliyu gwamnan
Sakkwato
Riƙa da ƙarfin Allah.
Jagora: Ɗan Barade jikan
Umaru,
Yara: Aliyu gwamnan
Sakkwato
Riƙa da ƙarfin Allah.
Jagora:Aliyu ga ka sarkin
Yamma,
Yara: Ka zama gwamnan
Sakkato,
Jagora: Aliyu ga ka Sarkin
Yamma,
Yara: Ka zama gwamnan
Sakkwato,
Riƙa da ƙarfin Allah
Aliyu gwamnan
Sakkwato
Riƙa da ƙarfin Allah.
Jagora: Mun yi arziki
Sakkwato,
Ɗan Bamaguje ya faɗi,
Da shi da ƙattan banza.
Yara: A gai da ‘yan boyi
nai.
Jagora: Mun yi arziki
Sakkwato,
Ɗan Bamaguje ya faɗi,
Da shi da ƙattan banza.
Yara: A gai da ‘yan boyi
nai,
Riƙa da ƙarfin Allah,
Aliyu gwamnan Sakkwato,
Riƙa da ƙarfin Allah.
Jagora: Sai goddiya nake gun
Jarma,
Yara: Abin da yai min ya
biya ni,
Jagora: Kamar Sakkwato
Alhaji Ummaru,
Yara: Abin da yai min ya
biya,
Riƙa da ƙarfin Allah,
Aliyu gwamnan Sakkwato,
Riƙa da ƙarfin Allah.
Jagora: Sai godiya nake gun
Jarma,
Yara: Abin da yai min ya
biya ni.
Jagora: Kamar Sakkwato
Alhaji Ummaru.
Yara: Abin da yai min ya
biya,
Riƙa da ƙarfin Allah,
Aliyu gwamnan Sakkwato,
Riƙa da ƙarfin Allah.
Jagora: Katukan Sakkwato,
Mai gari Dingyaɗi na gode,
Yara: Abin da yai min ya
biya,
Riƙa da ƙarfin Allah.
Jagora: Katukan Sakkwato,
Maigari Dingyaɗi dattijo.
Abin da yai min ya biya,
Riƙa da ƙarfin Allah,
Aliyu gwamnan Sakkwato,
Riƙa da ƙarfin Allah.
Jagora: Na gode wa Bello Koc
ɗan gwamna.
Yara: Abin da yai min ya
biya,
Riƙa da ƙarfin Allah,
Aliyu gwamnan Sakkwato,
Riƙa da ƙarfin Allah.
Jagora: Tun can dori mun faɗi sun ka iya,
Kamar ka bat taɓa zaki,
Kare idan ba ka bari,
Yara: Yanzu ya gyara ma
zama,
Riƙa da ƙarfin Allah.
Aliyu gwamnan Sakkwato,
Riƙa da ƙarfin Allah.
Jagora: Gwamna ya yi ayyuka ƙauye da binni,
Binni da ƙauye duka mun gode.
Yara: Aliyu gwamnan
Sakkwato,
Riƙa da ƙarfin Allah.
Jagora: A kowace lokal
gommen an ɗauki matasa aiki.
Yara: A daina yawon
ta-zubar,
Riƙa da ƙarfin Allah.
Aliyu gwamnan Sakkwato,
Riƙa da ƙarfin Allah.
Jagora: Es (S.) Fulani
Sulaimana,
Abin da yai min ya biya,
Riƙa da ƙarfin Allah.
Jagora: Es (S.) Fulani
Sulaimana,
Abin da yai min ya biya,
Riƙa da ƙarfin Allah.
Aliyu gwamnan Sakkwato,
Riƙa da ƙarfin Allah.
Jagora: Godiya nake es-es-gi
(S.S.G.) Sahabi Isa na Gada,.
Yara: Abin da yai min ya
biya riƙa da ƙarfin Allah.
Jagora: Godiya nake es-es-gi
(S.S.G.) Sahabi yasa na Gada.
Yara: Abin da yai min ya
biya,
Riƙa da ƙarfin Allah,
Aliyu gwamnan Sakkwato,
Riƙa da ƙarfin Allah.
Jagora: Kantoman Gada lokal
gommen Abu Altine kyaɗawa
Yara: Aliyu gwamnan
Sakkwato,
Riƙa da ƙarfin Allah.
Aliyu gwamnan Sakkwato,
Jagora: Alhaji Bello Alti
gwarango,
Yara: Riƙa da ƙarfin Allah.
Jagora: Zubairu ya riga ɗan yari.
Yara: Aliyu gwamnan
Sakkwato,
Riƙa da ƙarfin Allah.
Jagora: Ɗan Barade jikan Ummaru
Yara: Aliyu gwamnan
Sakkwato.
0 Comments
Rubuta tsokaci.