Ticker

6/recent/ticker-posts

Zakkar Fid-Da Kai

Mene ne zakkar fid-da kai?

Sadaka ce da Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya farlanta ta yayin da aka gama azumi.

An kira ta zakkar fidda kai ne saboda tana wajaba ne idan an gama Azumin Ramadan gaba-daya.

HUKUNCIN ZAKKAR FIDDA-KAI:

Zakkar Fidda kai wajibi ce akan dukkan musulmi, wanda ya mallaki sa'i Daya na abinci (kamar kwano Daya kenan) wanda ya fi yawan abin da zai ciyar da iyalansa.

Mai ba da zakkar zai fitar wa da kansa, matarsa, da duk wanda ciyar da shi take kansa, har ma Dan jaririn da yake cikin ciki.

Dalilin wajabcinta shi ne abin da aka rawaito daga Dan Umar – Allah ya yarda da shi – ya ce, “Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya wajabta zakkar fidda kai, sa'i xaya na dabino, ko sa'i Dayan da sha'ir, an wajabta ta a kan bawa, da Ɗa, namiji da mace, babba da yaro daga cikin musulmi. Manzon Allah ya yi umarni a bayar da ita zakkar kafin mutane su fita sallar idi.

LOKACIN DA AKE FITAR DA ZAKKAR FIDDA-KAI:

An fi son a fitar da zakkar fidda kai ranar Idi, bayan alfijir ya Bullo kafin sallar Idi. Kuma ya halatta a gabatar da ita kafin ranar idi da kwana ɗaya ko biyu, saboda sahabbai sun yi haka.

Ba ya halatta a jinkirta ta har bayan idi, saboda hadisin dan Umar wanda ya gabata in da yake cewa : “Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya yi umarnin a ba da ita kafin fitar mutane zuwa sallar idi”.

Haka ma a cikin hadisin Abdullahi dan Abbas, Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya ce, “Wanda ya bayar da ita kafin sallar idi, to zakka ce karbabbiya, wanda kuwa ya bayar da ita bayan sallah, to sadaka ce daga cikin sadakoki”

GWARGWADON ABIN DA DA AKE FITAR WA A ZAKKAR FIDDA-KAI.

Kowane mutum sa'i  Daya na Alkama. KO Daya daga cikin abincin da  mutane suke ci, kamar shinkafa, dabino, alkama, saboda hadisin Abu Sa'id Al-khuduriy – Allah ya yarda da shi – ya ce, “Mun kasance muna fitar da zakkar fidda kai daga abinci a zamanin Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ranar qaramar sallah”

Abu Sa'id ya ce, “Abincinmu a wannan lokaci kuwa shi ne Sha'ir da zabibi,

WADANDA AKE BAWA ZAKKAR FIDDA-KAI:

Ana bawa WADANNAN mutanen guda takwas zakkar fidda kai, saboda sun shiga cikin faɗin Allah MADAUKAKIN Sarki “KaDai Sadaka a bawa faqirai …”.

إِنَّمَا ٱلصَّدَقَٰتُ لِلْفُقَرَآءِ وَٱلْمَسَٰكِينِ وَٱلْعَٰمِلِينَ عَلَيْهَا وَٱلْمُؤَلَّفَةِ قُلُوبُهُمْ وَفِى ٱلرِّقَابِ وَٱلْغَٰرِمِينَ وَفِى سَبِيلِ ٱللَّهِ وَٱبْنِ ٱلسَّبِيلِ ۖ فَرِيضَةً مِّنَ ٱللَّهِ ۗ وَٱللَّهُ عَلِيمٌ حَكِيمٌ.

HIKIMAR ZAKKAR FIDDA-KAI:

1- Tsarkake mai azumi daga maganganun wofi da na batsa, saboda abin da aka rawaito daga Abdullahi Dan Abbas – Allah ya yarda da shi – ya ce, “Zakkar fidda kai tsarki ce ga mai azumi daga maganganun banza da ayyukan batsa, kuma ciyarwa ce ga miskinai”

Saboda mafi yawanci mai azumi ba ya rabuwa da maganganun da basu da amfani da wasannin shirme, da maganar da ba ta da fa'ida, to wannan sadakar sai ta zamar masa tsarki daga irin wadanncan maganganun haramun da ya yi, wadanda suke rage ladan ayyuka, suna rage azumi

2- Yalwatawa miskinai da talakawa, da wadatar da su ranar idi daga roqon mutane, roqon da yake dauke da qasqanci da wulaqanci a ranar idi, wadda take rana ce ta farin ciki da murna, sai su yi tarayya da mutane cikin farin cikin ranar idi.

Allah Yakarbi Ibadun Mu Baki Daya.

Madogara: Al-Feqh

Post a Comment

0 Comments