1.
Dakata ke 'yar gajera,
Ambatona kar ki ƙara,
A cikin sallar Tarawih.
2.
Ba ni son halin bala'i,
Ga Arewa tana kata'i,
Za ki je sallah a kaina.
3.
Mai kike so ne gare ni?
Na gaya miki tun a rani,
Babu gurbin sonki zuci.
4.
Hankalinki yana ina ne?
Shin ta ya ya za ki gane!
Ɗanbala bai son ganinki.
5.
Ba ni son halin mugunta,
Kar ki zama silar jarabta,
Na raba ni da nawa buri.
6.
Ɗanbala boko na shirya,
Ba gudu sai naga ƙurya,
Don a yau shi ne rabauta.
7.
Lokaci naki ƙanƙani ne,
Ki cire ran za mu zaune,
A mafarki ko ko zahir.
8.
Allah baki miji na kirki,
Ya zamo ji har ganinki,
Tun da aure ne gabanki.
9.
Rabbi kai ka faɗa a roƙa,
Ga ni fuska duk da toƙa,
Kar ka amsa kiran gajera.
10
Nai Salatai gun shi Nura,
Na Amina mijin Humaira,
Da nake burin na gan shi.
Haƙƙin Mallaka
Mohammed Bala Garba
22/04/2022
Sabuntawa
1/04/2023
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.