𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Wanne ne ya fi falala;
mace ta yi sallan tarawihi da
tahajjud dinta a gida ko kuma a masallaci, musamman idan ana nasiha da faɗakarwa a masallacin??
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Abin da ya fi falala shi ne
mace ta yi sallah agidanta, saboda
faɗin Manzon Allah
Sallallahu alaihi Wasallama "Gidaddajinsu shi ya fi musu alkhairi"
Kuma saboda fitan
mata sau tari baya rabuwa da wasu fitintinu, dan haka ta zauna agidan ta shi ya fi mata alkhairi a kan ta fita
Masallaci, wa'azi da faɗakarwa da ake yi kuma a masallacin za ta iya samun su ta hanyar cassette (recordings).
Sannan ina jan hankali ga waɗanda suke fita
Masallaci (mata) kuma da su nisanci fita daga gida da mummunan shiga, sannan su
nisanci sanya turare".
📝 المصدر :
[ ٦٠ سؤالا في أحكام الحيض والنفاس/لفضيلة الشيخ محمد بن صالح العثيمين رحمه الله ص٢٥].
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/Fb6ƙgYPXfEeHb8CD1SWAkK
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.