Ticker

6/recent/ticker-posts

Waɗanda Allah Ba Ya Buƙatar Azumin Su

Daga Abu Huraira (R.A)  ya ce:

Manzon ALLAH {s.a.w}  ya ce:

Wanda bai bar maganar zur ba, da kuma aiki da ita ba, da kuma jahilci, to, ALLAH baya da buƙata da barin cin abincinsa, ko barin shan abin shansa.

[Bukhari da Abu Dawuda suka ruwaito shi].

SHARHI:

Wannan hadisi yana mana nuni da cewa duk wanda yake shaidar zur kuma idan an kawo masa ita ya yarda da ita, alhali yana Azumi ALLAH ba ya son Azuminsa.

Duk wanda yake yake ibadah abisa jahilci baya neman sanin hukuncinta ALLAH baya son ibadarsa.

ALLAH ka karɓi ibadarmu ka gafarta mana zunubanmu baki ɗayanmu Ameen.

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments