𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaykum. Malam ya ibada? Allah yasamu dace.
Malam don Allah ina son nasan nayi saduwa da miji neh kuma ina son nayi azumi
ko naceh natashi da niyar azumi amma sai na makara ban yi wakan tsarki da wuri ba bayan saduwa ta dashi sai 6:am na makara
shin zan iya ɗauki azumi na babu damuwa? Dan Allah ayi min bayani malam
Na gode
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa'alaikumus salam Warahmatallahi Wabarkatahu
Dukkan MAZHABOBIN nan huɗu sun yi ittifaki a kan sahihancin azumin mai janaba ko mai hailan da batayi wanka ba.
Sai dai an ruwaito daga URWATU BIN ZUBAIR da HASANUL BASAREE cewa idan ya
jinkirta wankan da gangan ba tare da uzuri ba, to azuminsa ya ɓaci.
Amma da a ce ba
da gangan bane misali da janabar ta kama shi sai ya yi barci bai farka ba sai bayan fitowar alfijir to anan
Azuminsa ya inganta. Irin wannan hukunci haka yake a ramuwar Azumin watan
Ramadan. Amma ga Azumi na nafila ko wadanda ba na watan Ramadan ba ko ramuwarsa
to su koda alfijir ya keto yana da janaba da gangan to Azuminsa ya inganta.
WALLAHU A'ALAM.
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/BSA30hdZD7V3WSJF8WVwUj
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.