Ticker

6/recent/ticker-posts

Dalilin Da Ya Sa Mata Suke Yin Jinin Al'ada

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum malam khamis, wai mene ne jinin Haila? ban san me Haila take nufi ba kuma Mene ne dalilin da ya sa mata suke yin jinin Haila amma maza basuyi?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salam warahmatullahi Wabarkatuh

Jinin haila wani jini ne wanda yake fita daga gaban (al’aurar) mace a kowane wata wanda Allah ya tsara ga dukkan 'ya'yan Adam mata. Jinin Haila ita ce babbar alama dake nuna mace bata da juna biyu, sannan ita ce babbar alama dake nuna jikin mace shirye yake da ya dauki juna biyu inhar da za ta sami Jima'i tsakaninta da namiji.

Yawancin mata suna fara yin haila ne daga shekara 12 zuwa 50 amma wani lokacin mace tana iya yin haila kafin shekara 12 ko kuma bayan shekara 50 wannan ya danganci yanayinta da kuma Wurin da take zaune.

Idan lafiya ƙalau ne, ana fara jinin alada ne daga shekaru 10 zuwa shekaru 16. Ɗaukewar jinin alada ya bambanta tsakanin mata. Wasu suna dainawa a shekaru 43 wasu kuma suna wuce shekaru 50.

Daga lokacin da mace ta fara al’ada, tsabtace kai na da matukar wahalar gaske. Musamman lokacin zafi, daga an yi gumi sai a fara wari mai tayar da zuciya, har mutane su rika kyamar wacce ke jinin al’ada.

Mafi yawan malamai sun ce mafi Karancin kwanakin jinin Haila shi ne Wuni ɗaya da dare ɗaya, Sannan mafi tsawon lokaci shi ne Kwanaki goma-sha-biyar.

Dalilin yin jinin Haila a kowane wata, mahaifa tana yin wasu shirye-shirye domin ɗaukar juna biyu. Wannan shirye-shiryen yana farawa ne da zarar mace ta kai shekarun fara jinin al’ada. Mahaifa tana daina wannan shirye-shiryen bayan mace ta kai shekarun daina jinin al’ada. A lokacin wannan shirye-shiryen (kowane wata), ƙwai yana fitowa tun yana ƙarami har ya kai girman da zai iya haɗuwa da ruwan maniyyin namiji, domin samar da ɗa.

Har ila yau, a kowane wata cikin mahaifa yana haɓaka, kuma yana yin kauri a lokacin wannan shirye-shirye. Duk wannan canje-canjen da yake faruwa a cikin mahaifar mace, yana faruwa ne domin tsammanin samun ciki. Idan mahaifa ta gama wannan shirye-shiryen kuma, ba a samu juna biyu ba, to sai cikin mahaifar ya kwakkwaɓo ya fara zubar da jini. Wannan jinin shi ake kira da jinin al’ada.

Da zarar jinin ya fara zuba, mahaifa za ta fara wani sabon shiri domin tsammanin ɗaukar ciki. Idan kuma aka yi sa’a, mace ta samu juna biyu, to mahaifa ba za ta sake yin irin wannan shirye-shiryen ba, har sai bayan haihuwa ko kuma cikin ya zube. Wannan dalilin ne ya sa duk macen da take da juna biyu ba ta yin jinin al’ada.

 

Abin Da Ya Haramta Ga Mai Haila sune: Sallah, azumi, Taɓa Alkur'ani, Yin Ɗawafi a ka'aba, zama a masallaci, saki, saduwa.

Shifa abin da ya shafi jinin al'ada al'amari da Allah madaukakin sarki ya yi bayaninsa a cikin Alkur'ani mai girma, Allah yana cewa:

''Kuma suna tambayarka dangane da al'ada, Kace: Shidinnan cutane, ku nisanci (saduwa da) mata a lokacin al'ada, kada ku kusance su har sai sun yi tsarki (Jinin ya dauke) idan suka tsarkaka (suka yi wanka) to ku je musu ta inda Allah ya umarceku, Lalle Allah yana son masu yawan tuba kuma yana son masu tsarkaka''. Bakara, ayata: 222.

Haka kuma ma'aikin Allah Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi- yace; (Wannan) Wani abune da Allah ya dorawa mata 'ya'yan Adam''. Ashe ba shaci-fadin da ake cewa bane ai sanadiyyar da ya sa mata suke al'ada shi ne wannan ganyan bishiyar da Nana Hawwa'u ta ci a gidan aljanna, amma Annabi Adam mala'ikane ya rike masa makoshi (makogaro) sai ya amayar da abin shi ya sa maza basa yi. Wannan labarin bashi da kanshin gaskiya domin ayoyin Alkur'ani sun tabbatar da Annabi Adam ya ci itaciyar.

WALLAHU A'ALAM

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/BSA30hdZD7V3WSJF8WVwUj

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments