Ticker

6/recent/ticker-posts

Yadda Ake Biyan Tsohon Bashi!

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Salam. Ina da tambaya

Na ranci kuɗi fam biyu kamar shekaru (62) da suka wuce, ban biya ba. In zan biya yanzu da haka fam biyun zan biya koko ya za a yi?

𝐀𝐌𝐒𝐀👇

Wa alaikum assalam

Wasu malaman sun tafi a kan cewa zai biya kima ne, na kuɗin da ya ranta, misali Fam biyu me za ta iya siya a wancan lokacin, sai a bada kimarta a yanzu, saboda in an biya da adadinsu akwai cutarwa ga wanda ya ba da bashin, kuma yana daga cikin ka'idojin Sharia tunkude cuta gwargwadon iko.

Malaminmu Sheikh Ibnu Jibrin (Bajimin malami, mai amsa fatawa a Saudiyya) ya tafi a kan cewa ana iya biyan kwatankwacinsu daga kuɗin da darajarsu ba ta faduwa kamar Dalar Amurka.

Allah Ne Mafi Sani

DR. JAMILU YUSUF ZAREWA

Ku Kasance Da mu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Faɗakarwa a Sunnah.

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/GEahmrOpR4pA5TmW0ZW0cU

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

************************************** 

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments