Ticker

6/recent/ticker-posts

Ya Za Ki Yi?

Ke ce mijinki ya shiga banɗaki zai yi burosh da safe can kawai sai kika ga ya fito da gudu da kofin ruwa a hannu yana ta dauraye bakinsa yana kuskurewa Alamar dai wani abun ne ya shiga masa baki mara kyau, ke ƙarshe dai har da amai ya yi. Kika taya shi ya wanke jikinsa ya koma ɗaki ya kwanta yana ta mai da numfashi. 

 Sai da kika bari ya huta sai kike tambayar shi habibi na me ya same ka ne a banɗakin da ka shiga dan na ga ko gama wanke bakin ma ba ka yi ba? 

Buɗar bakinsa cewa ya yi baby mantawa na yi na saka makilin a brosh ɗinki sai da na fara sanan na lura  Ashe ba nawa ba ne naki na ɗuka. 

 Wai idan ke ce matar me za ki cewa wanan dan rainin hankalin habibin naki?


Post a Comment

0 Comments