Ticker

6/recent/ticker-posts

Waɗansu Daga Cikin Dokokin Ƙwallon Yara

 

1_ Wanda ya fi kowa ƙiba shine zai kama gola. 

2_ Mamallakin ƙwallon shi ne zai zaɓi waɗanda za su buga kwallon. 

3_ Wanda mai ƙwallo bai yarda ya buga kwallon ba shi ne wanda zai tsaya a waje idan ta fita ya ruga ya dauko ko don a saka shi shi ma ya ɗana. 

4_ Idan aka ɓata wa mai kwallo Rai to lokacin tashi ya yi. 

5_ Idan ka daki Dutse da ɗanyatsanka kuma jini ya fara fita, cikin sauri zaka dibi Kasa ka tule raunin domin zuba Kasa cikin ciwon shine taimakon gaggawan da zaka fara yiwa kanka. 

6_ Ba za ka dinga yanke mai kwallo sau da yawa ba domin idan ka fusata shi zai ɗauke kwallonsa ne ya ce an tashi. 

7_ Babu Offside kuma babu Referee. 

8_ Babu Foul har sai idan ka tumu da Kasa kuma ƙura ta yi sama da yawa. 

9_ Ƴan wasa 2 da suka fi Kowa iya ƙwallo basa zama a gari ɗaya Kowannensu zai zaɓi ƴan wasansa ne domin nuna Bambamci a tsakani. 

10_ Idan ka zamo kai ne zaɓi na ƙarshe to hakan yana nufin babka iya ƙwallo sosai ba kuma a defence za a ajiye ka. 

11_  Ɗan wasan da yafi Kowa iya ƙwallo dole saidai su zauna gari daya da mai ƙwallon. 

12_ Domin bambamce bangarorin 2 dolene ɗaya bangaren su cire rigarsu. 

13_ Dole akwai wani Gida a gefe wanda da zarar ƙwallon ta faɗa to kowa yasan an tashi domin bazasu ba da ita ba. 

14_ Ba a tashi daga ƙwallon har sai gari ya fara duhu an daina ganin kwallon Sosai tukunna ake haƙura. 

15_ Daga ƙarshe za a tashi yayin da kowanne ɓangare yake tsokanar ɗaya ɓangaren a kan cin da sukayi musu kafin kuma aje Gida a tadda hukunci a gurin iyaye.

 Ka Yi Gaskiya

 

Post a Comment

0 Comments