HEGIYA. 😡😡😡
Wata yarinya ce a unguwarmu kullum in zan wuce 🚶 sai ta aiko min yaro 👲 da awara. Wai gashi inji yayarshi 👸. Ni Kuma in karba in lamushe .😋 Ana haka ana haka, Kai naga abunnan fa yayi yawa 🤔. Sai rannan na zo wucewa, 🚶 Kamar yadda aka Saba sai ga yaro da gudu 🏃. Wai gashi inji yayata. Na ce Kai, mu je wajan yayarnan taka 🤷 in ji dalilin da ya sa ta ke min kyauta. Muna zuwa Sai muka gaisa da ita 👋. Na ce baiwar Allah naga abun alkhairi nagode kullum sai an aiko yaro da kyauta 🙏. Budar bakinta ta ce ai karka damu. Ba kyauta bace. 🙅 Dama rannan kazo wucewa 🚶 kudinka dubu biyar suka fadi 💸. Sai na tsinta, shine nake baka awara a cikin kudin. Yanzu ma saura ta dari biyu kudinka su kare 🙅
😭😩😩 Wane mataki ya dace in dauka akan wannan muguwar yarinyar 😩???!
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.