Mai haila da nifasi da mara lafiya da mai shayarwa ko mai cikin da za su galabaita ko abin shayarwarsu ya galabaita, da matafiyi a tafiyar da ba ta saɓon ALLAH ba wadda ta zarce nisan kilo-mita (80), suna da rangwame, sai su ƙirga kwanakin da suka sha, bayan Ramadan sai su rama.

ALLAH shi ne mafi sani.

************************************** 

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam