Ticker

6/recent/ticker-posts

Bambanta Tsakanin Taransifa Da Kuɗi Hannu (Cash) YaYin Kasuwanci

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Tambayoyi sun yi yawa game da 'yan kasuwan da za a zo sayayya wajansu sai su ce in kuɗi hannu ne sun sayar (10,000), in kuma Taransifa ne (12,000) ko makamancin haka, shin hakan ya halatta a Musulunci ?

𝐀𝐌𝐒𝐀👇

A zahirin nassoshin Musulunci wannan cinikayyar ta halatta, saboda bamabanci ne ya yin siyan kaya, ba tsakanin kuɗi ne da kuɗi ba, hadisan da suka zo kuma sun hana yin fifiko ne a canji tsakanin kuɗaɗen da suke jinsinsu ɗaya, ba tsakanin kayan kasuwanci da kuɗi ba.

Malaman Fiƙhu suna kawo ka'idar (ضع وتعجل) wacce ta kunshi yin ragi a cikin bashin da za a amsa kafin lokacin da aka cimma daidaito ya yi, wannan sai ya nuna lokaci yana tasiri a harkokin mu'amala.

Transifa tana iya jinkirin zuwa, ta yadda ko da dan'kasuwa yana so ya yi amfani da kuɗin ba zai iya ba a cikin lokaci, sannan akwai kauyuka da wuraren kasuwanci a karkara wadanda ba sa amsar Transifa sai kuɗi hannu, sannan akwai abin da bankuna suke cira idan aka yi Taransifa zuwa asusun banki, wani lokacin ma Transifar ba za ta zo ba sai mutum ya je banki ya bi-biya, wannan ya sa Bambanta tsakanin Taransifa da kuɗi hannu ba zai ci karo da Sharia ba.

 

Wanda bai bambanta tsakanin Transfer da kuɗi hannu ba, ya saukakawa mutane, ya kyautata kuma zai shiga addu'ar Annabi SAW "Allah Ya jikan mutumin da yake saukakawa ya yin siye da kuma ya yin siyarwa.

Allah Ne Mafi Sani.

Dr. Jamilu Zarewa

Ku Kasance Da mu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Faɗakarwa a Sunnah.

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/GEahmrOpR4pA5TmW0ZW0cU

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

************************************** 

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments