Ticker

6/recent/ticker-posts

Sakkwatanci Zalla

Wani yat taɓa ba matatai ƙodatai guda. Ran nan ko da yad dawo gida sai ya isko ta tunzure da baki jaye da jikka giririri wai ta yi tashi. Biɗaw wuri ɗai yay yi walla yaz zamna yah aza ƙahwa tai bisa ƙahwa yay yi wani doro wada kas san bahillacen zabo. Yaɗ ɗora bugun tahin ƙahwag ga ta bisa. Yam mai da gaba yamma yac ce mata: "Ita ƙodata hwa, da ita za ki gidanku halan?"

Dakariyat dole tak koma ciki tana gunaguni.

Nic ce: "Lau, in ba a ɗatu da yaro, a ba shi daddawatai.

Sakkwatanci Zalla

Post a Comment

0 Comments