Wannan na ɗaya daga cikin jerin waƙoƙin Malam Khalid Imam da a kullum suke faɗakarwa da ilimantarwa da nishaɗantarwa. Yana taɓo fannoni daban-daban a cikin waƙoƙinsa, ciki har da abubuwan da suka shafi lamuran yau da kullum.
Tsaunin ƙayar tudunsa,
Na kumfa ne mu lura,
Bishiyar ƙarya jikinta,
Ƙayoyi ne mu gane,
Ƙarya ƙyawun jikinta,
Iri ɗaya ñe da kasa,
Kasa ko ta yi bacci,
Ɗan uwa janye jikinka,
Kumurci bai da sabo,
Sharri ne fal cikinsa.
Duk wanda ya ce da ƙarya,
Zai abota ko amana,
Babu shakka ya bi gaibu,
Halin jaki gare ta,
Ita ƙarya ɗan uwana,
Sai an nisa a hnaya,
Jikinka gaba ɗayansa,
Ka saki kafin ka farga,
Sai tai tutsu ka faɗo.
Ta bar ka a kwance wanwar.
Ka ji mai sharrin kilaki,
Ita karuwa ɗan uwa,
Nakiya ce hilatarta,
Ke sa wawa ya so ta,
Zuciyarsa tamau ta aure,
Gansheƙa ce kilaki,
Ko da liman ta aura,
Dace ke sa ta tuba,
Ta bar shegen halinta,
Gaskiya dai ta fi dahir.
Ƙarya na rusa komai
In har na gane ƙarya,
Ban ba ta riƙon amana,
Ko ana tafiya na gane,
Motar ƙarya na hau ni,
Zan sauka na canza mota,
In ba motar da zan hau,
Sayyadata sai na taka,
Wannan shi ne batuna,
Kuma shi ne gaskiyata.
Motar ƙarya hawanta,
Wallahi yana da sharri,
Sai kun nisa a hanya,
Za tai faci a daji,
Gaban garken su kura,
In kai gaba ga sayaki,
Can gefe ga su zaki,
Tarko ka yi wa kanka,
Halaka ka saiwa kanka,
Ka biye son zuciyarka.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.