𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu
alaikum malam. Mene ne hukuncin hadiye yawu, ga mai azumi?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Yawu baya cutar
da azumi, don haka in aka hadiye shi babu komai, kamar yadda idan aka tofar da
shi babu komai. Amma kaki da ke fitowa daga ƙirji
ko daga hanci, wanda larabawa ke kira (nukhamah), ko kuma (nukha'ah) wanda shi
kuma shi ne kaki mai kauri da ke fitowa daga ƙirji
ko kuma daga kai, irin Waɗannan
wajibi ne ga mutum namiji ko mace tofar da shi, da fitar da shi, da rashin
hadiye shi.
Yayin da shi
kuma yawu na al'ada babu matsala akansa, kuma baya cutar da mai azumi; namiji
ne ko mace.
MAJMU'U FATAWA
WA MAƘAALAAT
MUTANAWWI'AH, (15/ 313).
ALLAH NE MAFI
SANI.
Ku Kasance Damu
Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Fadakarwa a Sunnah.
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/J1hm5Tw12uYBƙfaiPwf28l
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ
ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ
ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ
ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ
ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ
ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ
ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
Post your comment or ask a question.