Ticker

6/recent/ticker-posts

Kamar Kumbo Kamar Kayanta

A.B Sanyinna da S.I Sanyinnawal

Kwalejin Ilimi Ta Shehu Shagari Sokoto

TSAKURE

Wannan takarda dai an rubuta ta ne da niyyar tunatar da Hausawa wani bangare na rayuwarsu ta asali da aka san su a kanta, da kuma wasu muhimman al'adunsu da suka yi wa rikon sakainar kashi, kamar rayuwa ta kunya, da tarbiya, da kuma riko ga al'ada, musamman a wajen sutura da zamantakewa.

A cikin takardar an fito da tsagaron rayuwar Hausawa a jiya, kuma an nuna yadda take a yau, haka kuma takardar ta yi bayanin yadda suturar Hausawa take ta asali, da kuma canje-canjen da aka samu a halin yanzu saboda shigowar bakin al'adu. A wajen zamantakewa ma haka aka dubi yadda abin yake asalatan, da kuma yadda abin ya tabarbare a wannan lokaci. Da niyyar shugabanni da dattibai daga cikin Hausawa da ma samari maza da mata, masu kishin Hausa da al'adunta, su mayar da hankali su gane Borno gabas take.

GABATARWA

Da sunan Allah madaukaki. Tsira da amincin Allah su tabbata ga fiyayyen halitta Muhammadu, da iyalansa da zuriyyarsa ga baki daya.

Hausawa na cewa, so duk so ne, amma son kai ya fi. Kuma mai madi ke talla, mai zuma ido yake sawa. Mun kara aminta da fadar masu hikima da ke cewa, ba a wane bakin banza. Ashe gaskiyar mafarauta da suke cewa, kowa ya ci zomo ya ci gudu. Hakika irin fice da daukakar da Hausawa da adabinsu ke da shi a idon duniya tun ba yau ba, ya cancanci a gutsura wa masu mamare domin su taki dahir, wadanda kuma demuwa ta kama, kan su ya waye. Babbar manufarmu a nan ita ce dan kyallarawa da hango Adabin Hausawa a duniyarmu ta karni na ashirin da daya (Kn 21) halin da yake ciki. Mun zabi adabin Hausa da Hausawa da yadda suke aiwatar da wasu al'adu na rayuwarsu, mun hade su wuri daya, da manufar gane wa ido irin yadda bakuwar rayuwa da al'adunta suka yi tasiri a kan rayuwar Hausawa. Don haka, da wannan muradi ne za mu ci gaba da luguden wannan takarda.

Babu shakka, da yawa za a sami Hausawa suna nunin adabinsu na gargajiya, da suka gada da hannun hagu. Irin wannan yana faruwa ne a dalilin aron rayuwar boko, da yake ita kuma bakuwa ce, saboda rashin fahimtar cewa, a yarda da kolo (ungulu), domin shamuwa gida za ta je, ko kuma sun kasa gane irin hikimar da ke tattare a cikin adabin nasu na gado, da kuma binciken sirrin da ke cikin sabon adabin da suka aro, wato na Turawa. Wannan shi ya sa wasu 'yan kallo daga cikin Hausawa ('yan boko) suke kallon mai karatun Hausa a matsayin raggo, ko dolo, ko maras aikin yi. Har ma sukan ce, wai me za a koya ga Hausa, bayan ita ce Harshenka da aka haife ka? Kuma mene ne ba ka sani a cikin ta ba? Sannan kuma me za ka yi da ita in ba karantarwa ba? Don haka karantun ta wauta ne.

A bangaren wasu kuwa, saboda tasirin addinin Musulunci, masu addini suna ganin ba abin da ke cikin adabin Hausa sai bori, tsafi, wake-wake da raye-raye da sauransu. Wasu kuma suna ganin cewa, tsayawa ga adabin Hausa, wani kauyanci ne, kuma kasawa ce ga rayuwa, don ta kasa karbar sabon salo na rayuwa, har suna cewa, “Duk rigar da zamani ya dinka sa ta shi ne magani,” Wai a ganinsu, me ke cikin adabin Hausa da ba a sani ba? Don haka tsayawa a gudanar da rayuwa a kansa gidadanci da rashin samun karbuwa ne.

A idon manazarta Hausa da adabinta masu waɗannan ra'ayoyi ba abin da yake damun su illa cutar rashin sani, wanda kuwa Hausawa suka ce, ya fi dare duhu. Domin dai sun kallaci adabin Hausa da ido daya, ita ma ijiyar ta hagu. Ita kuma dayar ta dama hakanya ta fada mata, don haka ganinsu ya zamo garaye-garaye, don haka ya sa ba su kai na hannu gida ba, na dawa kuma na batun tsere musu, wato sun yi kamun gafiyar Baidu, hasarar ta yi musu yawa; ba su ga hamma ba su ga hammada. Wasu kuma daga cikinsu ba su sani ba, kuma ba su da bukatar a waye musu demuwa. Wannan ya haifar, da yawa daga cikin al'ummar Hausawa a wannan zamani maza da mata, manya da samari, da 'yan mata, 'yan boko, da wadanda ba su ba, sun yi watsi da kashi saba'in daga ciki dari na rayuwar adabin Hausawa, sun dauki rayuwar adabin Turawa, da kuma na hauka. Su ba Musulmi ba, su ba arna ba, a rayuwance, sai suka kasance sun raina inda suke, inda kuma za suna an raina su.

Don haka dai manufarmu a nan da kuma sauran 'yan'uwa dalibai masu nazarin Adabin Hausa, daura damarar yin fito-na-fito da irin waɗannan matsaloli da ke damun al'ummar Hausawa, har sai mun ga an gano Borno gabas take.

Bayan wannan, takardar tamu za ta yi tsokaci ne a kan abubuwa kamar haka:

1. Hausawa Jiya da Yau

2. Suturar Hausawa A Jiya

3. Suturar Hausawa A Yau

4.Tsarin Zamantakewar Hausawa

5. Shawarwari

6. Nadewa

7. Manazarta

To kada dai mu cika ku da gafara sa ba ku ga kaho ba, ga kahon:

1. HAUSAWA A JIYA

A nan takardar tana magana ne a kan irin yanayi, da halayen da Hausawan jiya suka siffanta da su, kuma da su ne ake gane su a kowane yanki na kasar Hausa da ketare, duk inda aka gan su an san su ne babu tanbaba. Dangane da haka ne Muhammad Tahir Adamu (1997) yake cewa: “Hausa harshe ne na Hausawa. Su kuma Hausawa wasu al'umma ne da suke zaune a kasar Hausa cikin yankin Afrika ta yamma. Hausawa dai mutane ne bakake, wato bakar fata ba farar fata ba. Duk da yake akan sami 'yan farfare jefi-jefi musamman in aka sami auratayya da wata kabila.

Hausawa dai a da mutane ne masu tsananin rikon al'adunsu na gargajiya, musamman wajen tufafi (sutura), da abinci, da kuma al'amurran da suka shafi aure ko haihuwa ko mutuwa da sha'anin mu'amala tsakanin dangi da abokai, da shugabanni, da kuma al'amurran sana'a ko kasuwanci ko neman ilmi da sauransu.”

Shi kuma A.M. Bunza (1990) a nasa ra'ayi cewa ya yi Hausawa dai mutane ne da suke zaune a kasar Hausa tun farkonta, kuma suna da zuriya a cikinta har zuwa yau. Kazalika suna magana da harshen Hausa kuma ba su da wani harshe in ba Hausa ba, kuma suna da dabi'u da al'adu irin na Hausawa idan sun saba haka to barbarar yanyawa ne.”

Har ila yau wajen fayyace al'ummar Hausawa a jiya, malam Rabi'u Zarruk(1986) ya kara fitowa da su sarari da cewa “Hausawa dai su ne al'umma mai asali daya da yare daya, da kirar jiki kusan iri daya, da al'adu iri daya, da falsafa ko ra'ayin zaman duniya iri daya. Bayan haka cikin al'ummar kowa zai rika alfahari shi dan kabilar ne.”

Wannan kadan kenan daga cikin irin ra'ayoyin masana dangane da su waye Hausawa a jiya, to da yake manufa a nan gane al'ummar Hausawa a jiya, sannan kuma tare da haka a gano wasu abubuwa da suka canja su in akwai, haka ba za ta samu ba in ba an ambaci hanyar gudanar da rayuwarsu ba, don gano haka, sai mu leka rayuwar Hausawa a da mu ga yadda ake aiwatar da ita, kamar haka.

RAYUWAR HAUSAWA A DA

Kamar dai sauran al'ummomi na duniya, Hausawa sun dade suna tafiyar da harakokin rayuwarsu a lokaci mai tsawo, kuma tare da haka, canji yakan zo musu gwargwadon yadda abubuwa suke faruwa a ko'ina. To irin waɗannan abubuwa sun shafi rayuwar Hausawa a gargajiyance. Misali:

TSARIN SIYASA:

Tsarin siyasa shi ne tsarin gudanar da mulki, watau waɗansu hanyoyi da ake tafiyar da sha'anin mulki a cikin al'umma. Tsarin tafiyar da mulkin Hausawa na gargajiya ya samo asali ne tun wani zamani mai tsawo, watau tun kafin zuwan addinin Musulunci, da kuma zuwan Turawa.

A da mai gida shi ke tafiyar da duk harkokin gidansa ba tare da wani ka-ce-na-ce ba. Shi ne ke da ikon sa wa a yi ko a bari, watau tsakanin mata, 'ya'ya, kannai, kai da duk wani wanda yake karkashinsa, shi ke sasanta duk wani rikici ko sabanin da ke faruwa a tsakanin jama'a, wato ta hanyar kwato hakkin duk wani wanda aka zalunta, haka kuma abin kunya ne idan wata baraka ta faru a cikin gida, kuma mai gida bai yi kome ba. Wannan ya nuna cewa, a da mai gida shi ne wuka, kuma shi ne nama wajen tafiyar da harakokin gidansa. Haka abin yake kasancewa, ba za a taba saba umurnin mai gida ba.

A YAU

Bayan tafiya ta yi nisa, a sabili da shigowar baki, da kuma kara yawan yaduwar jama'a da tasirin Turawa, da ilimin boko, da kuma hanyoyin ci gaban mai ginar rijiya sai wannan abin ya dauki sabon salon zaman 'yan marina kowa da inda ya sa gabansa, da kuma salon kowa ya yi salla da karatun kansa, don haka ya kasance tsarin Hausawa na shugabanci, da al'adu, da adabi suka barkace. Aka wayi gari a yau a gida daya, za a taras kowa ya fadi kansa ne yake yi wa nishi. Wato abin nufi a nan, za a taras mai gida ya kasa hada kan iyalansa, hasali ma shi ne zai bi hanyar rarraba kansu ta hanyar bai wa kowa damar aikata abin da ya ga dama, sannan da yawa za a taras da yawa an mika akalar gudanar da harakokin gida ga hannun mata.

Haka kuma a zaman tare da Hausawa suke da shi a da, inda za a ga cewa mai gida baba, da da, da jikoki duk a wuri guda ake zaune, kuma tukunya guda ake azawa don abinci. Kuma shi ne kowa zai ci, yanzu aka wayi gari a zuriya daya gidan kowa da ban, abincin kowa da ban, sha'anin kowa da ban, iyalin kowa iyalinsa ne, kuma ana iya fada tsakanin 'yan'uwa saboda diya, ko mata da sauransu. Kula da waɗannan 'yan canje-canje zai nuna mana cewa wasu bakin al'adu musamman Bature ya yi tasiri a kan rayuwar Hausawa, kuma ya yi ƙoƙarin kawar da wannan kyakkyawan tsari da muke da shi, kuma mahankaltanmu suna kallo sun saki jiki har abin ya tabarbare. Ga shi kuma wani fitaccen mawallafin rubutattun wakokin Hausa mai suna Akilu Aliyu ya yi nuni kan irin hadarin da ke tattare da rashin kishin adabi da al'adun Hausawa ga Bahaushe. A cikin wakarsa ta Hausa Mai Ban Haushi, inda ya yi kira da cewa:

Abu namu ne mu rika shi kankam ya fi

In mun yi wasa dole zai mana nisa.

Irin waɗannan kiraye-kiraye akwai su da dama bakin masana masu yawa.

Wannan kadan kenan dangane da rayuwar Bahaushe ta asali, da kuma tasirin da wasu bakin al'adu suka yi a kan tsarin rayuwar, don haka manufarmu a nan a kula.

To da yake takardar tana magana ne a kan abubuwa kamar uku da suka danganci rayuwar Bahaushe, kuma ta yi din tsokaci a kan daya, yanzu kuma za ta juya akalarta ga abu na biyu wanda yake muhimmin abu ne, kuma shi ne kammalar kowace al'umma, wato sutura wanda yake saboda haka ne Bahaushe yake karin maganar (Sutura ita ce mutum). Don haka a nan za mu dubi yadda suturar Bahaushe take ta asali, da kuma wasu canje-canjen da aka samu a halin yanzu kamar haka:

SUTURA

Ma'ana: Kalamar sutura dai ararriyar kalma ce daga Larabci, wadda ake kira da Larabci (suturatu) da manufar tufafin da ke rufe wa mutum al'aurarsa, wato dai duk tufafin da ke isar mutum Muslmi ga yin salla. Amma a wajen Bahaushe kalmar tana da ma'anar tufafi isassu da za su kare mutuncika daga tsiraici dada kowadanne iri ne, sababbi ne, ko tsofaffi in dai sun kare tsiraici, ana kiransu sutura.

Sutura a wajen Bahaushe ta kasu kashi biyu, manya wato maza da mata, a wannan kashe-kashen kuma, sutura tana da rukunna da ban-da ban na mutane, kamar a rukunin maza akwai manyan dattibai, da matasa, da yara. Haka kuma a cikin manya akwai sarakuna, da malamai, da makada da maroka da dai suransu. Haka su ma a rukunin mata, akwai mata manya tsofaffi, da kuma yaryaje, da 'yan mata, da kuma yara kanana da sauransu. Waɗannan su ne kashe-kashe da rukunan Bahaushe, kuma kowane kashi da kowane rukuni yana da irin nasa tsarin tufafin da ya cancance shi; daidai matsayin da yake a kai. Amma kuma sannu a hankali yanzu abin ya cakude ya dauki wani sabon salo na kusan matsayin kowa na kowa ne, ko ma wannan ya saki nasa, ya dauki na wani, shi ma wanin ya saki nasa ya dauki na wancan. Inda za a taras babba ya sanya kayan da ba nasa ba ga matsayinsa, ko kuma yaro ya sanya tufafin da matasa ne ke sa su. Ko kuma a taras gaba-daya duk an aje kayan da aka gada kaka da kakani, kamar yadda yake faruwa a rayuwarmu ta yau, wannan kuwa a fili yake, domin idan mun dibi tufafin Bahaushe na asali, za mu ga kashi saba'in cikin dari, mun saba wa haka, mu dubi wannan tsarin na tufafin Hausawa da kyau mu gani su ne muke amfani da su?

TUFAFIN HAUSAWA MAZA NA GARGAJIYA

Ire-iren tufafin da Bahaushe yake sawa a gargajiyance domin kare mutuncinsa su ne:

1. Riga sace

2. Riga mai kwado

3. Riga binjima

4. Riga aska yakwas

5. Riga 'yar madaka

6. Riga kwakwata

7. Riga girken Gwandu

8. Bulla fara da baka

9. Riga mai barage

10. Riga gare da sauransu

Haka kuma Hausawa kan sanya:

Janfa, kaftani, wando buje, wando saisaye, wando tarangama, wando tsala da kuma wando zina.

A wajen huluna kuma, Bahaushe kan sanya:

Dankwara, da habalkada, da marfiyo, kube, da mangadara, da gurus, da bakwala, da Zanna Bukar, da kuma Audu Angale.

Yayin da a wajen Takalma Bahaushe yake da:

Huffi, da tsambatsai, da markube, da kwat, da fade, da sauransu.

Kayan da yake amfani da su kuwa domin a dinka masa waɗannan nau'o'in tufafi su ne: Zawaiti, da alawayyo, da sandar zane da turmin sanda da sauransu.

1. Dunhu Saki

2. Adire

3. Mukuru

4. Gwandai

5. Bakurde.

KAYAN KAWAR MATA NA GARGAJIYA

'Yan kunne, murjani, warwaro, tago, sarkar wuya, munduwa, Kwandaga, jeri na cunku, lalle, katambiri, hure da goro, da sauransu.

Ambatar waɗannan a matsayin sutura ga mata ya zama tilas, saboda suna daga cikin abubuwan da ke kare mutuncinsu ga idanun jama'a

Saboda kara tabbatar da bayanin wannan takarda da take yi a kan wannan batu, shahararren marubucin wakar Hausa, kuma masanin al'adun gargajiyar Hausawa wato malam Abubakar Ladan ya zayyana mana waɗannan baitoci a cikin wakarsa mai suna (Wakar Gargajiya) inda yake cewa:

Mu ma akwai suturarmu mun yi iri-iri

Gargajiya don nan kasar Najeriya

Rigarmu sace ko'ina yau a yaba

Mu ne muke dinka shi yau duka duniya

A yi adon kwado da linzame ka ga

Wa za shi kushe irin shigar Nijeriya

Ga binjima mai 'yar ciki wannan da ban

Rigarmu mai aska takwas sha tambaya

Rigarmu 'yar madaka a yanzun ta bace

Haka kwakwata girke da riga gariya

Girke na gwandu ku tabbata girken Nufe

Sai mai sukuni za ya su ya kewaya.

Ashe kenan Bahaushe yana da nau'o'in suturarsa da aka san shi da ita tun kafin haɗuwarsa da wasu bakin al'ummu. Kuma sutura nan ba abin yarwa ba ce. Ire-iren waɗannan tufafi da aka zayyana su ne wannan takarda take ƙoƙarin bayyanawa ga jama'a, musamman Hausawa.

Bayyana ire-iren waɗannan tufafin ga jama'a musamman wadanda abin ya shafa, wato Hausawa a wannan halin na yanzu zai taimaka ainun wajen gano cewa lalle akwai canje-canje na rayuwa da aka samu, wannan kuwa ya faru ne a dalilin shigowar bakin al'adu wadanda suka haifar da samuwar wasu nau'o'in tufafi da ba namu ba, kuma muka dauke su tamkar namu, saboda rashin kula har aka ba waɗannan bakin damar shimfida wundinsu wai da niyyar zama dindindin.

Irin wannan gobarar kuma sai ta zame mana tsumagiyar kan hanya, wato fyade yaro fyade babba, domin kusan kowa abin ya shafa. Sai dai kuma abin ya fi tsamari a wajen samari da mata, da 'yan matan Hausawa kuma abin ya kewaye ko'ina birni da kauye; lungu da sakon kasar Hausa. Domin a dalilin haɗuwar da Hausawan suka yi da waɗannan al'adun na baki ya haifar da samuwar waɗannan nau'o'in tufafi ga matanmu, da 'yan matanmu kamar haka:

Sitella, short play, play, follow me gaya, baba na isa aure, jahannama ga fasinja, sa hannunka masoyi, easy to rich, fish, tazarce, Kerewa, in ka isa duba, kai ka kula, da dai sauransu. Inda za ka ga mutum ka rasa inda za ka sa shi, shin Bature ne, ko Ba'indiye ne, ko Inyamuri ko dai wata kabila da ban. A nan dai ya zama ba ya cikin arna a zucci, kuma ba ya cikin Musulunci a siffance, ko suturance. Allah Ya kiyashe mu.

Yanzu kuma bayan takaita maganar sutura, sai kuma bayyana yadda zamantakewar Hausawa take, da kuma ire-iren canji da aka samu a cikinta halin yau.

ZAMANTAKEWA

Zamantakewa na nufin kamar yadda sunan ya nuna daga kalmar zama wato abin nufi a nan shi ne zama tare, ya'alla ko dai ta fuskar zumunta ko makwabtaka, ko kuma ta fuskar yanayin san'a, ko da yake ma'anar takan iya wuce wannan idan aka yi la'akari da ire-iren dangankar da ake samu tsakanin al'umma, misali zamantakewa tsakanin shugabanni da mabiyansu; da malamai da almajiransu; da mata damazajensu; da iyaye da 'yaransu.

Idan za a yi magana a kan abin da ya shafi zamantakewar Bahaushe, to ya zama tilas a fara da kallon irin yanayin zamansa na jiya, sannan da yadda yake a yau.

Bisa ga abin da ya wakana, Bahaushe mutum ne mai son zumunci da kuma biyayya ga na gaba gare shi, wannan ne ya sa yake da kare-karen magana masu nuna muhimmancin zumunta, da kuma biyayya ga na gaba. Ga abin da yake cewa game da zumunci “Zumunta a kafa take”, ko kuma “Gidan zumu ba kasuwa ba ne”.

Haka a bangaren biyayya, yakan ce “Bin na gaba bin Allah”. Dubi saboda tsananin kwadaitarwa ga biyayya da na gaba, yadda ya girmama yin biyayya ga na gaba, da bin wanda ya hallice shi.

ZAMANTAKEWAR HAUSAWA A JIYA

Idan aka yi la'akari da adabin Bahaushe wadanda ke a tsakaninmu a yau na zantukan hikima (Karin magana) za a ga cewa, Bahaushe wanda ke da tsarin zamantakewa na cude-ni-in-cude ka, da kuma biyayya ga na gaba (Shugaba), dubi abin da Bahaushe yake fada game da dan'uwa, “Dan'uwa rabin jiki”. Wannan maganar ta tabbatar da tsarin zaman gandu a cikin al'ummar Hausawa.

Zaman gandu wani tsarin ne na asali ga rayuwar Bahaushe, wannan na nufin samun magidanta 'yan asalin zuriya daya, a cikin gida daya a karkashin jagorancin Uban gandu, ko da yake kowane maigidanci na da rukunin nasa iyalin, amma kuma da hakan yana biyayya ne ga Uban gandu. Shi wannan Uban gandu zai kasance mafi shekaru daga cikin zuriyar wannan gida. Kuma bisa ga al'ada, Uban gandu shugaba ne; alkali ne kuma ba a girgiza masa, ko a yi masa bore. Hausawa za ka taras daga kakanni sai 'ya'ya da kuma jikoki. wato daga zabo sai zanensa.

Babban abin da irin wannan Zamantakewar ta kunsa shi ne, inganta dankon zumunci da taimakon 'yan'uwa da rufa wa junansu asiri.

Bayan da mutane suka fara yawa sai aka fara samun, ko kafa unguwanni. Akan sami unguwa ne ta hanyar haɗuwar gandu-gandu, waɗannan gandayen ne ke haɗuwa su samar da unguwa. A nan ma akan yi Mai unguwa, wato wanda zai shugabanci jamar da ke zaune a cikin wannan unguwar, ta haka ne za a ci gaba da kaunar jama'a da har a kai matsayin Sarki, wanda shi ne mai daukar nauyin jamar'arsa ta kowane bangare na rayuwarsu ta yau da kullum. Dubi abin da Ɗankwairo ke ce wa Sarkin Daura, dangane da talakawansa:

Rike talakawanka da kyawo

Kai musu hairi

Kasa su hanyoyin Musulunci

In sun takwanre ka lankwaso su

In ko sun kiya ka ba su kashi

….

(Musa Ɗankwairo, Wakar Sarkin Daura)

Da yake ba kudurin wannan takarda ba ne shiga tsundum cikin lamarin sarauta, illa dai kawai manufa ita ce ganin yadda zamantakewar Bahaushe ta faro daga gida cikin zuriyarsa.

Zamantakewar Hausawa a yau Hausawa na cewa, “In kida ya canza rawa ma canzawa take” Haka kuma yana cewa “Sarki goma zamani goma”. Idan muka dubi yadda yanayin tsarin zamantakewar Hausawa take a yau, da idon basira za mu ga akwai wasu muhimman abubuwa guda biyu da suka bakunci kasar Hausa, waɗannan ababen sun yi matukar tasiri ga kawo sauye-sauye ga rayuwar Bahaushe gaba-daya, ba ma wai a tsarin zamantakewa ba.

Waɗannan abubuwan su ne:

1. Addinin Musulunci

2. Turawan Mulkin Mallaka

Na farko dai shi addinin Musulunci da yake addini ne wanda ya kunshi dukan bangarorin rayuwa, dole ya kawar da duk wata al'ada ta Maguzanci wadda ba ta yi daidai da ta Musulunci ba, domin ta Musulunci ta samu sukunin zama.

Na biyu shi kuma zuwan Turawa da karatun book, sun zo da wasu bakin al'adunsu waɗannan al'adun na Turawa sun yi barazana kwakkwara a kan al'adun Hausawa, har ma wasu Hausawa marasa kishin al'adunsu sun sauya sheka daga al'adunsu, zuwa dabi'un Turawa, da wasu bakin al'adun wadanda karatun boko ya yi sanadiyar haɗuwa da su.

Da yake muna magana ne a kan zamantakewa ta fuskar zumunta da makwabtaka da sana'o'in Hausawa za mu dubi yadda zuwan Turawa ya kawo sauyin zamantakewa a cikin al'umar Hausawa. Zuwan Turawa shi ne ya kawo ilmin boko, shi kuwa ilmin ya sama wa mutane sababbin sana'o'in da hanyoyin rayuwa, kama daga ayukan kwadago ya zuwa gudanar da harkokin mulki da sauransu.

ZAMANTAKEWA TA FUSKAR MAKWABTAKA

Makwabci/Makwabtaka: Ma'ana wannan kalma Bahaushiyar kalma ce wadda a Hausa ana iya samun makwabci da makwabciya, da kuma makwabta. Na farko a matsayin namiji, mutum na biyu kuwa a matsayin ta mace daya, na uku a matsayin jam'i. Duk da manufar abokin zamanka makusanci amuhallance.

A wajen Musulunci kuwa, kalmar ta na nufin duk wanda kuke a tsakaninka da shi akwai gida arba'in, to kowane makwabcin wani ne. Amma a Larabe ba haka ake kiran kalmar ba. Da Larabci (ALJARU). Wannan ne Bahaushe ya fassara da makwabci.

To amma a gun Bahaushe yana iya kallon makwabci ta bangarori da dama kamar haka:

1. Makwabci ta hanyar sana'a

2. Makwabci ta hanyar zamantakewa a muhallance

3. Makwabci ta hanyar ma'aikata

Duk waɗannan abubuwa ne masu matukar muhimmanci ga rayuwar Hausawa.

Zumunta Ta Fuskar Sana'a

Ita ma wata dadaddiyar rayuwa ce da dangantaka da Hausawa suke a kanta tun fil-azal, kuma wannan rayuwa tana da kyakkyawan tsari da inganci ga adabin Hausa. Irin wannan inganci ne ya sa Bahaushe ya kalli zamantakewa ta fuskar sana'a ta hanyoyin da ban-da ban kamar:

a. Sana'a a muhalli daya

b. Yanayin sana'a

Waɗannan duk suna da zumunta ta zamantakewa a kan sana'o'in da suka hada zamansu wuri daya, ko yanayi daya, da yawa irin wannan zamantakewa kan haifar da auratayya da sauransu.

Zamantakewa Ta Fuskar Zumunta:

Ita ma wata alaka ce zumunta wato jini daya, ko dangi daya wadda ta hada na nesa da na kusa. Har ila yau Bahaushe yana da zumu na sana'a, wato dan'uwan sana'arsa, kuma yana da zumu na aiki. Wato dan'uwan aikinsa da suka hada wuri da irin aiki daya. Haka kuma yana da zumu na abota. Wato dan'uwansa a wasu harakoki da suka yi tarayya ga aikata wa ko yi.

To, ta la'alkari da irin wannan rayuwa da kashe-kashenta, za mu taras cewa a wajen Bahaushe ba karamin lamari ba ne, domin da yawa irin wannan zamantakewa kan haifar da abubuwa masu kyau, kuma na alheri, da kulla kyakkyawar dangantaka musamman ta auratayya ta zama dalili na yaduwar iyali a zama abu daya.

SHAWARA

Wannan takarda hannunka mai sanda ce, da kuma maganar Bahaushe da yake cewa: Wanda ya yi walle ba ya sani, sai an dage shi. Don haka shawara a nan ita ce, yana da kyau shugabanni da dattibai, da malamai masana a kan harshe da al'adun Hausawa su mike tsaye; su yi kira da babbar murya, kuma su nuna aikace, ga maganganunsu, da halayensu, da al'adunsu wajen nuna matsayinsu ga Hausa da al'adun Hausawa, wajen kare mutuncinta, haka kuma su nuna kyama ga saurin karbar bakin al'adu, musamman wadanda ke cin dugadugan namu. Idan an yi haka darajar adabi da al'adun Hausawa za su dawo kamar yadda suke a da.

NADEWA

Wannan takarda nuni ne cikin nishadi inda aka yi tsokaci a kan rayuwar Bahaushe ta asali musamman a kan yanayin suturarsa wadda aka san shi da ita tun fil-azal, kamar sauran kowace al'umma ta duniya, kamar Yarbawa, Larabawa, Turawa da sauransu, da kuma yanayin zamantakewarsa, yadda yake kallonta da kuma yadda ya karkasa ta; da irin muhimmancin da ke cikin kowane daga ciki.

Wannan takarda ta jawo hankalin shugabanni magabata a kan su jawo hankalin sauran mutane musamman samari wajen guje wa karbar bakin al'adu, su mayar nasu. Da fatan wannan za ta zama mai amfani ga harshe da adabin Hausawa.

MANAZARTA

1. N.N.P.C (1968) Labaru Na Da Da Na Yanzu.

2. Mu'azu, Y.Yahaya, Mu'azu, da A.Z. Sani (1992) Nazarin Rayuwar Dan Adam. University Press PLC Ibadan.

3. M.T. Adamu (1997) Asalin Hausawa Da Harshensu Salmayasin Publications Ltd Kano.

4. Dr. M.A. DAntumbishi (2004) Harshen Al'umma Da Kuma Zamananci: Takardar kara wa juna ilimi da aka gabatar a sahen Harsunan Nijeriya UDUS Sokoto.

5. M.A Bazar da A. Bukhari (2001) Dalilin Watsuwar Hausawa A Sassan Duniya Da Ban-Da Ban, Da Kuma Irin Tasirin Da Wannan Yanayin Ya Haifar Ta Fuskar Harshe Da Al'ada. Takardar Da Aka Gabatar A Ajin Karatun Na Manyan Dalibai (M.A. Hausa).

6. Nahuce I.M. (1994) Kananci Karin Harshe Ko Daidaitacciyar Hausa? Takardar Da Aka Gabatar A Bukin Makon Hausa UDUS.

7. M.A. Ladan Wakar Gargajiya Daga Baiti Na 16-43.

8. Usman Ibrahim da Habib Alhassan (1986) Zaman Hausawa



Source: Facebook: Tsangayar Daukaka Harshen Hausa Da Al'adu Da Kuma AdabiTsangayar Daukaka Harshen Hausa Da Al'adu Da Kuma Adabi

Post a Comment

0 Comments