Ticker

6/recent/ticker-posts

Idan Na Yi Mafarki To Abin Da Na Yi Mafarki A Kansa Sai Ya Tabbata

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum warah matullahi wa barakatu. Malam wallahi kullum addu'a mukeyi bisa lokacinka da kabawa al'umar shugaba sallallahu alaihi wa sallam, Allah ya baka kujera a fadar Shugaba salla lahu alaihi wasallam.

Malam na kasance daya Daga cikin mutanen da suke temakawa yara da karatu, a wata makarantar islamiyyya a layinmu, sai wata baiwar Allah take min tambaya cewa, ita ta kasance idan ta yi mafarki to abin da tai mafarki akansa sai ya tabbata. shi ne take cewa wai ko me ya sa hakan, to amma ban ce mata komai ba, sai na ce mata taban lokaci nima zan yi tambaya a kan hakan. kuma Malam babba ce me hankali, gata da son ibada, kuma karara take fitowa a kawayenta in dai ba mai bin addini bace to ba zata hada hulda da ita ba.

𝐀𝐌𝐒𝐀👇

Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.

Daga cikin bayin Allah akwai wadanda idan matsayinsu ya kai, Allah yakan yi musu ilhamar abubuwa afili ko amafarki kuma sai kaga abin ya tabbata.

Misali kamar Sahabban Annabi akwai da yawa daga cikinsu wadanda sukan ga abu a mafarki kuma ya tabbata. Hakanan a cikin Salihan bayin Allah da Waliyyai.

A gefe guda kuma daga cikin Aljanun dake shiga jikin Bil Adama, akwai wasu masu da'awar sanin gaibu. Idan suka shafi mutum sukan yi masa irin wannan sanarwar amafarki, kuma wani abun yakan tabbata afili. Musamman abin da ya shafi miyagun abubuwa. Ko kuma wata tsintuwa ko Jinya, etc.

Wani lokacin daga haka kuma za su fara nuna ma mutum cewar ya rika yi musu wata ibadah ta musamman. Kamar yanka ko sadaka, etc. Daga nan kuma shi ke nan mutum ya zama mushriki (Allah ya kiyayemu).

 

Shawarar da za ka ba ta a nan ita ce :- Duk lokacin da za ta kwanta barci ta rika yin alwala da kuma addu'o'in barci. Idan taga wani abu irin wannan a cikin mafarkinta, idan na alkhairi ne sai ta gode ma Allah. Idan kuma kishiyarsa ne to ta nemi tsari daga sharrin Shaiɗan da kuma sharrin abin da ta gani. Amma kar ta gaya ma kowa. Haka Manzon Allah ya gaya ma Abu Ƙatadah (ra) a cikin wani hadisi : "MAFARKI MAI KYAWU DAGA ALLAH YAKE. DON HAKA IDAN DAYANKU YAGA WANI ABIN DA YAKE SO (A MAFARKI) TO KAR YA BADA LABARINSA GA KOWA SAI WANDA YAKE SONSHI. IDAN KUMA YAGA ABIN DA YAKE ƘI, TO KAR YA GAYA MA KOWA. ya yi TOFI SAU UKU A GEFENSA NA HAGU, YA NEMI TSARIN ALLAH DAGA SHAIƊAN JEFAFFE, DA KUMA (TSARINSA) DAGA SHARRIN ABIN DA YA GANI. DOMIN ITA WANNAN MAFARKIN BA za ta CHUTAR da shi BA".

(Aduba Sahihul Bukhariy hadisi na 7044, Sahihu Muslim hadisi na 2261).

 

Allah ya datar damu baki daya.

 

WALLAHU A'ALAM.

 

Ku Kasance Damu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Faɗakarwa a Sunnah.

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/L8l4xHCd7wUG5xZEmvBbzB

 

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

Post a Comment

0 Comments